← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 177

Sashe 97

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na saba a kafada na rika hannun Ibrahim muka fita ta kofar dakin da sai a ranar ya bar min ita a bude. Dana fito sai na hango wata kofar a bude na nufi gurin haka na rika bin kofa kofa har na fito harabar gidan dake cike da ciyayi ga kuma wani bangare na gidan da ba a gama ginawa ba. "Zaki bimu ne?" Ya tambaya yana kallona da fuskarsa mai ban tsoro. Sai na daga mishi kai. "Kin yarda da sharadin?" "Nan ma na daga mishi kai" "Miye sunan wannan yaron" "Ibraheem" "Yarinyar fa?" "Fatima" "A cikin sunan mata ina jindadin Lisa, daga yau sunanta Lisa, shi kuma London shi ne sunan da na fi so, ke kuma zaki koma sunanki na asali Emily no more Aisha, that's my number one rule My name is Vito (King)" Ya kada min kai sai yaronsa ya bude min mota na nufi motar na shiga can baya domin mai gida uku ce, shi kuma ya zauna a tsakiya direbansa a gaba. Daga kaduna da direban yaja motar be tsaya ko'ina ba sai Abuja, muna isa ya wuce da mu Airport tun kamin mu bar garin Kaduna ya tambaye full name dina na fada masa ashe zai siya min ticket ne domin muna isa Airport din bamu wani sha wahala ba muka shiga jirgin ya daga zuwa garin da ban taba tunani ko mafarkin zuwa ba wato Part hartcour. A gidansa muka sauka akwai tsoro sosai a gidan domin a kowane lumgu da sako na gidan yaransa ne ga Camera ta ko'ina, a wani bangare na gidan ya aje shi, ya wadata ni da komai ya samo mai aikin da zata kula da yarana ya nemawa London asibiti mai kyau aka fara duba shi ya saya masa kayan wasa. A lokacin ne na ji na tsani musulmai har bana son jin labarinsu ko ganinsu. Ya kan ziyarce mu lokaci zuwa lokaci har na shekara daya a gidan ban san sana'arsa ba, amman ya wadata ni da komai na more rayuwa sai dai baya bari na tafi ko'ina kuma babu wanda yake shigo min. Da jindadin ya samu sai jikina ya dawo, wata rana ya shigo yana kallona yace yanzu me nake bukata, na fada masa da ace zan samu dama zan sha wani abun da zai rage min kiba ne domin ta fara damuna, kuma ina son wani abu da zai iya dauke min hankali domin ina yawan tunanin abubuwan da suka faru har mafarkinsu nake. Tambayar daya fara min ita ce zaki iya karatu? Nace zan iya, sai yace zai sama min duk abun da ake bukata zai fitar da ni waje na yi karatu kuma zai bincika abun da ya kamata akan rage kibata. Kamar wasa sai ga shi ya sama min takardun primary da secondary, ya zaba min London a matsayin kasar da zan tafi na yi diploma in business administration. Ya kuma fada min da yata zan tafi domin akwai gurin da ake bada ajiyar yara a can har sai idan mutum ya dawo daga aiki ko makaranta ya je ya karba. Da na yaye Fatima na bar kasar zuwa London na yi karatu acan na kan kai Fatima day care sai idan na dawo na je na karbota, gida ya kama min apartment daya, kudi kuma har ban sab me zan yi da su ba, sai da na shekara daya a can sannan ya bijiro min da zancen surgery, na ji tsoro amman likitan da zai min aikin ya kwantar min da hankali, ya fada min yadda dokikin abubuwan suke, kuma ya nuna min kudin da za a kashe a rubuce. Aiki aka min aka rage min nama jiki duk inda kitse yake a jikina suka cire min, na yi jinya na wahala ga dokoki da ka'idodin shan magani da abinci, a haka dai har aka yi nasara. Kamin na gama karatun na dawo kasar nan na zama wata kyakkyawa fari ya kara bayyana ni da turawan ba a banbance da wani, musamman idan na shiga cikin masu jan gashi irin nawa. A gida kuma mai aikin da Vito ya dauka Chidimma tana ta kula da London, shi ma kuma yana kula da shi ta wani bangaren, hakan ya saka suka shaku. Na dawo kasar a lokacin da Fatima ta yi wayo, sai ya zamana bata da wani makiyi irin Vito ba kuma dan ya mata komai ba, shi ma kuma baya wani jituwa da ita London ne na shi. A lokacin ne ya fara ba ni yancin fita yawo amman be yarda kowa ya zo gurina ba, sannu a hankali kishi ya fara shiga kamin ya sanar da ni yana so na, sai da ya fara sanar da ni asalinsa sana'arsa da komai. Ya fada min shi be taba son mace ba gaba daya aure ko soyayya basa gabansa sai da na zo rayuwarsa, kuma na yarda domin na lura da zaman dana yi a gidan ban taba ganin mace ko daya ba, kuma be taba nuna min son taba jikina ko yin wata mu'amala da banza da ni ba. Har sai da ya fara nuna min yana kaunata, ya cancanci na ba shi kauna amman zuciyata ta yi firrr ta ki karbarsa, na kan duba alherinsa da kyautatawa amman soyayyarsa ta ki zama a zuciyata wata kila saboda basa jituwa da Fatima ne, wata kila kuma saboda zuciyar tawa ta mutu ne bana jin son namiji a zuciyata. Da fatima ta shekara biyar sai kiyayyarta ga Vito, domin Fatima tana da wani irin hali na kafiya da rashin jin magana,karamar yarinya ce amman ta iya muguyen kalamai. Ko kadan Fatima bata dauko daga hali da kamanin na ba, a duk lokacin da kowa zai kalleta Turhan zai gani kamar an tsaga kara. Gashi da ta yi wayo sai ta tashi da son addinin musulunci ta hanyar CHANNEL din da muke kallo, daga ranar dana fada mata asalin sunanta Fatima ne bata sake amsa sunan Lisa ba, ni kuma bana iya hana ta abun da take so, shiyasa idan Vito ya fita sai na kama mata channel din tana koyon abubuwa na addinin musulunci har ta fara iyawa, domin Fatima tana da wayo sosai da basira ga bakinta a bude yake kamar na babba. Tun tana da shekara daya da wata hudu ta fara kiran Dady ba tare da kowa ya fada mata, sai na hana ta, a lokacin da ta yi wato sai ma fada mata ita bata da mahaifi, shiyasana hade mata suna uku Fatima Emily Aisha. Ko kadan jininta be hadu da na Vito ba har ta kai yayi tsanani har ya kan gwada dukanta ni kuma na nuna masa ba zan lamunta ba, ga shi kuma yana shan kayan maye ni kuma bana son yarana su taso suna sha, ko suna kallon abun, sai na fada masa ina bukatar gurin zama na wa ni kadai, be musa ba ya sama min gida na koma ya cigaba da kula da rayuwata da ta yarana, ni kuma sai na yi amfani da wannan damar na saka Fatima makarantar Islamiya dake garin ta kan je a duk lokacin da ta ji tana bukatar zuwa, a ranar da Vito ya gane dai da yayi min duka, daman ya saba idan na bata masa rai duka yake min tun ban saba ba har na fahimci haka halinsa yake. Vito yayi min komai Aliyu kuma ya cancanci komai daga gareni, a yanzu ma ya fada min ya gaji, kuma na san yayi kokari yana da gaskiya, yana tsananin kishina yana so na kuma ya kyautata min fiye da Turhan fiye da Khaleefa fiye da kowa, kokarinsa da hakurinsa kullum na jiran lokacin da zan amince da kaunarsa ne kuma na aure shi. Wannan ce Emily Aliyu wannan ne tarihin rayuwata, wannan dalilin ne ya saka na tsani musulmai kuma ya saka ba zan taba yarda Turhan ya ga Fatima ba, ba kuma zan taba sha'awar arba da Khaleefa ba, na san idan Turhan ya san da Fatima zai karbe ta ko dan ya kuntata min, ba dan yana sonta ba a yanzu kuma bani da kowa sai ita... Na wahala a lokacin da kowa yake bachi akan tasa rayuwar, na shiga taskun rayuwa a lokacin da babu ni da kowa, na kwankwasa kofofi da yawa ba su bude min ba, a duk inda na saka kafa sai na tarar rame ne na shiga ukuna Aliyu a yanzu ina kokarin gina kaina ne na zama kamar kowa, ni ma na samu yanci ni ma na jidadin da kowa yake ji. Har yanzu abubuwan da suka faru suna ruda kwakwalwata, abu kadan ya kan tuna min da baya, bana nufin cuta ma kowa miyasa ni ake cutar da ni? Shim ko dai ban cancanci farinciki ba? I'm so fighting for peace kwanciyar hankali nake bukata a yanzu, abu kadan zai iya buga kwakwalwata i have done enough i have done everything i can.. I deserve happiness too ko ba haka ba? ****. ****. *** "Kin cancanci, da ace zan iya dawo da lokaci baya Emily da na gyara miki komai, but it's not too late i Will make things right da yardar Allah Emily sai kin yarda musulmai akwai na gari kuma sai kin dauwama a cikin addinin da ke baki natsuwa har abada" Yayi furucin ne a daidai lokacin da jirgin ya sauka garin Kaduna, Fatima kuma take bachi. ______ Toh fa masu karatu kun ji tarihin Emily. [7/1, 9:53 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 97 · 0% Book details