Sashe 166
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 7 TALIYAR HAUSA YAR MURJI Abinci na gargajiya, ano na musamman, jin da in iyali! Idan kina/kanason abinci mai ano na musamman wanda zai tunatar da kai da in gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al ada ce mai ha a iyali, auna da jin da i a teburin gida. Me yasa za ka za i Taliyar Hausa Yar Murji? An yi ta da tsafta da inganci Ta dace da kowanne irin miya: miya mai wai, miya taushe, ko miya mai Sau in dafawa cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa Lafiyayye, mai sau in narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman Muna a Kaduna amma anonmu ya zarce iyaka! Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). Idan kana son jin da in abinci na gida wanda ke ha a zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa Yar Murji yau! wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. Ka more anon gargajiya mai tsafta, mai da i, mai orewa! Jin alamar mutum a bayanta ya saka ta juyo, sai suka hada ido, yana sayen da wando bachi sai farar vest dake jikinsa. Ya daga mata gira like how far, ta aika masa murmushi. "Ina kwana" Ya daga kafadunsa. "Ni ma ban san inda yake ba" "Okay good morning" "it's morning but not Good Morning?" Ta kalleshi with confuse. "Why?" Ya jingina da kofar kitchen din yana bata amsa tare da saka hannayensa aljihu. "Cox i didn't get a kiss from my wife" Ta juya ta aje wukar hannunta tana murmushi, kana ta sake juyawa ta nufi inda yake ta yi dage zata sumbance shi ya yi dage shi ma yana kauce fuskatsa. "Bana so, sai da na yi magana rike abun ki bana so" Ta zagaye hannayenta a wuyansa. "I'm sorry haba autan maza, na tuba handsome na maka kiss ma kamin na fito kitchen fa" "Aa ni ban ji ba, kuma waya ce ki bar ni ki zo kitchen? Ke dai kin dange sai kin wahalar da kanki ko?" "Babu wahalarwa a cikin hidimar miji ko wace kala ce" Ta sake kai bakinta da sauri zata masa kiss ya kauce yana dariya. "Na ce bana so" "Toh ba ni wanda na baka dazun, da kana bachi dawo min da abuna" "Kiss din?" "Eh" Yayi dariya mai sauti. "A ina kika ba ni?" "A nan" Ta tura masa bakinta. "Ni na san ba ta nan aka ba ni ba, amman tun da wayo za'ayi min a yaudarini ba matsala" Yayi mata kiss din. Ta sake shi tana ja baya cikin zolaya da muryar yaudara ta ce. "Ba a nan na yi maka ba, a nan na yi maka" Ta nuna kumatunta. Ya fusgota ya dawo da ita jikinsa. "To dawo min da abuna, na baki na ki" Ta noke kasa tana dariya. Binta yayi kasa yana mata kyaculculi sannan ya sake ta ya nufi plantain din da take yankawa tana soyawa at the same, ya dauki wukar yana yankawa ta karaso ya kwashe sannan ta dauki daya ta hura ta nufin ba shi. "Ki daina hura abun da abun da zaki ci, Annabi ya hana, hura abinci" "Na karu da wannan, amman akwai zafi fa" Ya aje wukar ya dauki daya ya bude yana riritawa a hannunsa har ta sha iska. "Bude bakin" Ta bude ya saka mata. "Kai zan bawa fa" "Kuma kuka ci?" "Kai ka ba ni ai" Ya kai hannunsa ya rikota suka fara kokawa ala dole sai ya cire wanda ya saka mata a baki, ita kuma ta yi hanzarin taunewa ta hade har tana kwarewa sai dariya take. Sai da ya ji tana dari sannan ya sake ta. "Wai Qalbin miyasa baki jin magana?" Ya nufi gurin da ruwa suke ya dauko mata ta bude bottle din ya daga kanta ya saka mata a baki, ta sha kadan tarin ya kwanta. "Kai ka koya min ai" Ya kai ruwan bakinsa ya sha kadan. "Ni din?" "Ko da aka kawo ni gidan nan har kunyarka nake ji, amman ta bi ka bala ni" Tana maganar tana dariya. Sai ya kai bakinsa yana hura amsan kanta. "Haka ake yi ma yarinya idan su ta kware" "Yarinya matar...." Ya zaro ido. "Ni din? Ni za ki duba ki cewa yaro? Gaskiya ne da sauranki" Ya aje ruwan hannunsa kamin ya juyo ta gudu daga Kitchen din, be san lokacin da dariya ta subuce masa ba, sai ya nufi kofar kitchen din ya rufe ta ciki, be bude ba sai da ya karasa aikin da take ya hada komai a ya zuba a mazubinsa sannan ya bude kitchen din ya kawo musu komai a inda suka saba karyawa. Al'ada ce ta ya sabawar kansa tun a lokacin da ya auri Kameela, idan ya rigata tashi shi yake hada musu komai na karyawa, idan kuma ita ta riga sai ta hada, sai dai ya fita kokarin hadawa domin tana yawan bachin safe shi kuma ya kan fita aiki dan haka baya jiranta yake hadawa musamman lokacin da take da ciki, har na rana ma wani lokacin girka musu yake ko yayi musu takeaway. A yanzu kuma ya dora daga inda ya tsaya da Emily, banbancin Emily da Kameela shi ne, Emily tana son girkawa Aliyu abinci saboda tana son yi masa hidima tana son ta yi masa abu na faranta rai, abun da zai yaba mata. Tana gwada new recipe wani yayi dadi Wani kuma yayi ba lada ba la'ada, shi kuma da yake gwanin zama da mace ne, be taba kin yaba mata ba. Ko be yi dadi ba yabawa yake ya gode mata, sai dai ya fara mata inda za ta gyara ko su sake yi tare. Kusan inda ba shi da wani aiki a waje to yana gida kusa da matarsa. Ita vata yarda ta yi nisa da shi, shi ma kuma be koya mata ba. Idan ya fita har kewar dawowarsa take, takan tanadi labarai kala kala da take ba shi, kama daga na littafi zuwa na mutane da take ganina kafafin sada zumunta, wani lokacin har kudi yake sakawa idan labarinta yafi na shi armashi zai biya, idan kuma nata ya fi armashi zata biya, ita ta kan biya ta wata sigar ne, shi kuma ya biya da kudi. Zamantakewa suke kamar daman can ita ce matarsa ta farko, ita ma shi ne mijinta na farko, ko da yake masu iya magana sun ce macen da miji ke so kullum yar gata ce. Tun bikin su da sati biyu Ummi ta bar su a garin Kaduna ta koma Abuja gurin mijinta daman can take zama dawowarsa, abubuwan da suka faru ne suka saka ta dawo Kaduna da zama, a yanzu kuma tun da sun kamalla komai cikin aminci da farinciki sai ta koma gurin tata ibadar ta aure. Kamin ta tafi sai da ta yi musu huduba sosai, musamman Aliyu, saboda tana ganin Emily kamar bata da matsala. Ta gargadi Aliyu ta yi mata uzuri da kuma taka tsantsan akan zamantakewarsu, ya rufe ido kuma ya toshe kunnuwansa daga masu suka ko gulma, ita kuma ta yi biyayya ga mijinta ta gujewa bacin ransa, sannan ta toshe kunnu daga wasu kannan maganganu. Ummi ta roki Emily karta zafafa akan zaman Fatima a hannunta, domin abu ne da dukansu suka sani Turhan ba zai yarda Fatima ta zauna tare da su ba, ko da kuwa tana son haka. "Ki daurewa zuciyarki ko babu dadi ki masa uzuri, saboda ya so ki be samu ba yanzu kuma yana da yarki, to ki masa hakuri ya ji sanyi ko ta nan, kuma karki bude hanyar da zata kawo baraka da mijinki akan yarki, sannan karki yarda mijinki ya raina yarki ko ya kaskantar da ita, kuma ko da tana can ki rika kula da ita akai kai, dan Allah ku bawa marada kunya, kar a ji kanku, idan sulhu ya gafara da mijinki, akwai mahaifiyarki idan abun ya ci tura, ina nan kuma mahaifinsa na nan, ba fata muke ba, amman dai kar aji a waje" Nasihar Ummi ta saka Emily ta dauke kai daga damuwa da rashin Fatima a kusa da ita, domin washe garin ranar da aka daura musu aure Ammy ta aiko aka dauki Fatima, har yau Fatima bata san ya dakin Emily yake ba, saboda ta ki kawota ita kuma bata son ta matsa abun ya zame musu matsala. Dan haka ta saka musu ido, Fatima na garin nan bata nan bata da labarinta almost 3 months da bikin babu amo babu labari. KAMEELA POV. "Ko da mafarki ban dauka Aliyu zai iya juya min baya har haka ba, kusan duka kawayena na bata da kowa saboda da shi, gaba daya rayuwata ta ta'allaka ne akansa" Kanwarta Farida ta dafata. "Kameela ke kika dauki Aliyu wani shege fa, tun farko be dace da ke ba" Kameela ta dube ta. "Zaki iya fada min illar Aliyu daya?" "Zan fada miki da yawa ma, kin ga dai akwai masu sonki masu kudi amman kin nace sai shi, kuma an makiyinmu ne" Ta yi murmushi. "Ba zaki gane ba, wannan ba illa ba ce, kuma na gujewa duk sauran ne saboda suna da aure, Aliyu kuma saurayi ne, Aliyu ba shi da wata illa da za a dube shi da ita a hana shi aure, amman ya ci amanata" "Ko yanzu fa kin ki bawa sauran dama ne, mutane na nuna suna sonki" "Farida ba zan iya zama da mai mata ba" "Ko da Aliyun ne ya dawo?" Ta yi shiru domin bata da amsar tambayar a yanzu. "Dan Allah karki bari son Aliyu ko abun da yayi miki ya hanaki kula wasu mazan, ki duba fa da zai yi aure ma be zauna a gidan da kuka zauna ba sai ya zabi zama a wani gidan kuma ya kwaso kayanki ya aiko miki, da kin mana yadda muke so ai da yanzu kin riga shi aure" "Ba auren ba ai mazan ne, yanzu duk namijin da zaka ce ya saki matarsa ya aureka ba zai yarda ba, ni kawai sai idan na samu