← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 177

Sashe 103

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

magana, ya rasa ta ina sauti zai fito daga bakinsa. "If you hurt my baby Kameela, sai na kashe ki Wallahi sai na halaka ki" Daker ya iya hada kalmomin bakinsa cikin wata iri siga ta kwantar da hankali da rarrashi da be taba sanin yana da ita ba ya furta. "Your Baby is in safe hands....Aisha.... Emily...." Daga nan be sake jin komai ba, aje wayar yayi ya kara rumgume Fatima a kirjinsa yana motsawa a hankali kamar wanda ke rike da sabon kwai. "Momy ta fada min ba ni da mahaifi waye kai?" Fatima ta tambaya tana ta sauke ajiyar zuciya na kukan da ta yi da karfi, Turhan ya girgiza kai ya rufe ido ya kasa cewa komai. KAMEELA POV. Ta kama hanyar komawa gida wata zuciyar na raya mata ta koma ta dauko yar mutane abun da ta aikata zai batawa Aliyu rai, wata zuciyar kuma na raya mata abun da ta aikata daidai ne domin idan ba haka ba Aliyu ba zai fita sabgar Emily ba, gashi abun har ya fara wuce gona da iri, ta san yadda Emily take da kyaun nan komai zai iya faruwa, idan ba haka ba bata ga dalilin Aliyu na boyewa Turhan lamarin ba. Ta isa ta faka motar waje ta fita ta shiga dakinta amman ta kasa natsuwa gabanta sai faduwa yake tana ta jin tsoro da tunanin abun da Aliyu zai fada mata, iyakar abun dai yayi fada yayi fushi, ko kuma yace ba zata koma yanzu ba, idan kuma ya wake ni fa? Ta raya ma kanta. No ba zai ma taba farawa ba da na saka masa guba ma be sani ba balle dan wannan. Kiran wayar Aliyu na shigowa wayarta sai da ta zabura tana kallon wayar har ta gama ringing bata daga ba, ya sake kira baya daga ba har yayi mata kira uku, tasowa ta yi ta fito daga dakinta ta zauna falo tana ta sake sake ta san ko ta koma Turhan ba zai bata yarinyar nan ba, ko da ya bata ai aikin gama ya gama ta fada musu komai, ta saka wannan ta kwance ita kadai ita dai babban hujjarta ita ce Emily tana kokarin anshe mata miji alhalin ga mai nemanta har da ya a tsakaninsu. Tana jin tsayawar mota ta leka Window ta hango motar Aliyu sai ta nufi kofar falon da sauri ta bude kamin ta saka kafarta waje har ya iso bakin kofar falon cikin wani irin yanayi da bata taba ganinsa a ciki ba, kuma bata taba tsorota da bacin ransa kamar na yau ba. Baya baya ta yi hakan ya ba shi damar shigowa falon fuska kamar bakin hadari. "Ina yarinyar da kika dauka take?" "Tana gurin da ya kamata ta kasance, gurin mahaifinta" Aliyu ya dauke ta mari da bayan hannunsa, sautin mari yayi mata chauuuuuuu har cikin kunen, ta dafe kuncinta ta zaro ido kamar za su fado. "Saboda wata banza zaka mare ni a cikin gidan Ubana Aliyu?" Ta daga hannu zata rama ya rike hannu ya jefar ya sake sauketa da mari sai da ta fadi. Mai aikinsu ta fito da sauri, kanwarta Farida ma ta fara saukowa da gudu. Aliyu ya nunata cikin tsananin fushi. "Abun da kika aikata ba kishi ba ne, hauka ne da rashin tunani, kin dauki yarinya kin dankata a gurin mutumen da bata taba sanin waye shi a duniya ba, kin rusa abota da aminci da ke tsakanina da Turhan na shekaru da yawa, kin yi sanadin karya alkawarin da na daukarwa Emily, kin zubar da kimar da Ammy take kallona da ita, wace irin mace ce ke? Alkawarin da na miki be wadatar ba? Bibiyar wayata be gamsar da ke ba? Kokarin kashe ni be saka kin natsu ba? Toh babu abun da zai sauya halinki Kameela, na gaji ko diamond ce ke haihuwar gold na hakura dake Kameela, na dauki abun da zan iya dauka yanzu kam anyi na karshe... NA SAKE KI... Enough is enough" Ya fada kai tsaye sannan ya juya ya fice daga falon ya koma motarsa, yaja ya fice daga gidan rai a bace, gidansa ya sake komawa domin a can ya baro Emily. Ya shiga cikin gidan ya faka ya fita motar ya shiga falon gidan, tsakiyar falon ya samu Emily duke dafe da kanta wayarta kuma a kasa. "Emily..." Be fadi abun da yayi nufi ba ta katse shi. "I want my baby" "Ta... Ta... Tana.... Gurin... Turhan..." "I know ka kawo min yata, ba zan je can ba saboda bana son ganinsa bana son jinsa" "Okay but i want you to know ba ni na shirya wannan ba?" Ta mike tsaye ta daka masa tsawa. "To waya shirya?" "Calm down Emily ki kwantar da hankalinki" Ta zaburo masa ta yi cikinsa da masifa idonta na cika da hawaye. "How dare you told me that? Kana son kwanciyar hankalina ka taho min da a? If you didn't plan all this taya ka san Turhan ya zo? Meya ka zo garin nan just for two days? Ka taho da Fatima ba tare da na sani ba ba, that's means ka san da wani abu Aliyu! Zuwa ba tare da ka sani ba ya rusa yadda ka tsara abubuwa shiyasa ka saka matarka ta dauke ta kamin mu zo ta kaita gurin Turhan right? Saboda ka san ina son yata dole na kai kaina a gurinsa ko? Ka min alkawari Turhan ba zai taba sanina ta hanyar ka sai idan ni na bukata, ina alkawarin yake? Ka ci amanata ba zan sake yarda da kai ba Aliyu, kallon da nake ashe ba haka kake ba, ka dawo min da yata Aliyu" Wani irin ihu take kamar zata tashi gidan sai da Aliyu ya ji wani tsammmmm yayi baya ya runtse ido ya bude saboda tsawar dake saka masa, ya juya da sauri ya fita a rikice. Motarsa ya koma ya koma ya shiga ya dauki hanyar gidansu Ammy. Zuciya a karye jiki a sanyaye kunyar yadda zai yi ido hudu da abokinsa ya rufe shi amman a haka ya daure ya shiga gidan saboda Emily ya san idan be dawo mata da Fatima ba ba zata taba yarda da shi ba, kuma ya san gaskiya idan ba shi ya dawo da Fatima ba Turhan ba zai bata yarinyar nan ba. Be raina kansa ya kara girmama laifin da Kameela ta yi ba sai da ya isa bakin kofar falon Ammy for the first time ya ji kunya da nauyi tura kofar dakin ya shiga, yayi unkurin fasawa ya fi a kirga kamin ya samu kuzarin tura kofar ya shiga da sallama. A tsaye ya riski Turhan yana maida hannayensa duka biyu a baya ya daure fuska yana kallon kofar falon da alama yana jiran shigowar Aliyu ne. Aliyu be taba gani abokinsa a cikin irin wannan yanayin ba sai yau. Aliyu ya gagara furta komai sai kallon Turhan yake babu kowa a falon sai shi kadai. "Fatima ka zo nema ko ka zo ka shirya wata karya ne? Ka ba ni mamaki Aliyu, daman ance acikin abokai da yan'uwa akwai makiyan mutum a yau na yarda, me na maka? Miye manufarka na boye Emily? Matar da ka san nemanta nake ido rufa? Matar da saboda ita mahaifiya ta gagara fahimtata har take ciwo? Abun bakin ciki kuma da kai nake shawarar nemanta? Har a airport na hadu da kai amman ka gagara cewa yata ce? A tsawon lokacin nan a tsawon wahalar nan ka san inda Emily take ka boye min? Da kai muka zo nan kana jin kalaman Ammy akaina amman ka gagara furta cewar ka san inda Emily take? Miye manufar ka? Wallahi kallon mutunen kirki nake maka aboki da ya juye ya zama kamar dan'uwa amman a yau wannan duk ya kau... Ka zama koren maciji a cikin korayen ciyayi, mutum mai fuska biyu! But thanks to your wife daman haka abun yake ka ci amanar wani kai ma aci taka, ta bayyana komai a lokacin da ya dace" Har lokacin Aliyu ya rasa abun cewa tambayar ina Fatima take ma ya gagara yi, Ammy ce ta fito dakin dake kasa a falon, Aliyu ya kalleta cike da kunya da nauyi, ya ambaci sunanta wai ko ita zata fahimce shi. " Ammy..." "Aa Aliyu ban da yau, da ka dauke ni uwa da baka aikata haka ba, na tabbatar da Ummi ce ba zaka aikata mata abun da ka aikata ba, ka ba ni mamaki shiyasa hausawa suka ce halin mutum dabam kalamansa dabam, bana son wani abun bacin rai dan Allah ka tafi" Ya juya ya fice daga falon tsabar kunya da bakinciki yana jin kamar kasa ta bude ya shige ciki ta rufe da shi, yana tafiya yana jin kamar ba kafafuwansa ba, haka dai ya shiga mota ya sak juyawa ya fice gidan sai kuma ya rasa ina zai tafi, ya san be isa ya koma gidansa ba tare da Fatima ba to yace ma Emily me? Haka kuma be isa ya dawo ya ce Turhan ya ba shi Fatima, gaba daya sai ya rasa ina zai saka kansa, gefe hanya ya faka ya bude motarsa ya fito yana sauraren kiran sallah da ake ko zai samu sallama. Shi ma dai yau ya zama marar mafaka be da wani gurin fakewa sai gurin mahaifiyarsa, wayarsa ya ciro ya kira Ummi tana dagawa ya ce. "Ummi ki min addu'a dan Allah" "Lafiya Aliyu" "Ba lafiya ba, kawai ki min addu'a ko zan samu mafita" "Ka daga min hankali wace irin addu'a zan maka? Me yake faruwa?" A takaice ya labarta mata abun da zai iya na haduwarsu da Emily zuwa abun da ya faru yau. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un, abu be yi dadi ba Aliyu ka yi sakaci na shiga tsakanin mutane biyu, gashi Allah ya baka mata da bata dace da kai ba ta jefaka a kunya, sannu a hankali idan baka rabu da yarinyar nan ba, nan gaba kadan ma sai ta yi kokarin kashe ka" "Already ta gwada Ummi ta saka min guba a abinci saboda Emily, amman ban ci ba sanadin haka na maida ita gida Mama Barakat ta ba ni shawarar maida ta na dawo ne wannan abun
Chapter 103 · 0% Book details