← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 177

Sashe 93

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ba sai da muka bar fadar da muka isa filin jirgi na yi zaton za'ayi mana irin na farko ne, ashe shi saboda isa da jirginsa yake yawo, sai dai hakan be hana a tantance mutanen da suke tare da shi ba, ni kuma bi ta wata hanyar dabam da ni bata hanyar da kowa yake bi ba, sai da aka isa gurin jirgin aka fito da ni daga motar na shiga aka zaunar da ni can baya nesa da mutane. A lokacin ne abubuwa suka fara yi min gizo ina ganinsu kamar mafarki. Tun da muka tashi ba mu sauka ko'ina ba sai Abuja Nigeria. Da muka sauka jirgin ne matar tasa aka matso da ni kusa da ita ta gargade ni da halshen igbo. "Ina fatan ba karya kike min ba, domin idan ya zama tsabanin abun da kika fada min toh zaki hadu da mummunan hukunci kuma zan saka a nemoki a ko'ina kika a kasar nan" Na ce mata na amince, suka shiga motar alfarma mu kuma aka saka ni a wata motar, ina ta kallon gari da titunan Abuja da tunanin dan yancin da na samu har muka isa gidan mijin matar mai kama da wata babbar fadar Sarki, mutanen da suka tarbeta ita da mijinta ma abun kallo ne, a nan na kara gane kudi suna da muhimmanci sosai a rayuwar dan'adan. Da muka sauka gidan sai ta hannata ni a hannun wata mata yar Kaduna tace mata wai ina da zan je na dauko ana tana son kar a barni na tafi ni kadai na tafi tare da rakiyar wasu saboda tana son ta gano gaskiya ta, ni dai an kira ni kawai aka nuna min matar da za mu tafi tare, ta hanyar wayar da matar take da yaren yarbanci, na fahimci kudin wacan matar da ta ceto ni wanda ko sunanta ban sani ba. Komai aka bani kasa ci na yi ina ta zumudin ganin ana ga kuma tsoro ya cika zuciya gani nake kamar Turhan zai aiko a tafi da ni ne. Hankali be kwanta ba sai da muka bar garin Abuja tare da matar da mijinta da nake kyautata zaton dan siyasa ne. Guri daya na zauna da matar, da alama ticket din da aka saya min na kusa da ita ne. A nan ta gabatar min da kanta ta fada min sunananta Barakat amman yaranta suna kiranta da Mama Barakat ta fada min ita bayarabiya ce, sannan ta tambayi labarina, ita kan ban boye mata komai ba na fada mata labarina tun daga tashina zuwa auren Khaleepa da kuma Turhan, gaba daya sai ta sauya ta rika kallona har sai da na tsorota, har muka isa Kaduna hawaye ke cika mata ido tana sharewa. Mun sauka Airport din idanuwa a zare kamar wata marar hankali ga rama na yi gaba daya ba ni da natsuwa. Mota daya aka zo daukarmu na shiga gaba ita da mijinta suka shiga baya, duk maganar da mijin yake bata amsawa har ya tambaya lafiya? Tace babu komai. Mun sauka gidanta ba laifi gida ne mai kyau amman ko kadan be kamo gidan wacan matar ta Abuja ba, kuma ita wannan da alama tana da abokiyar zama domin gidan bangare biyu ne, sai da muka fara shiga bangaren na farko ta shiga ita da mijin sai ta fito ita kadai ta shiga motar aka karasa da mu bangarenta. Na sauko motar ina jin kamar na yi tsuntsuwa na gan ni gaban ana, haka dai na daure muka shiga ciki, ta nuna min dakin da zan zauna sannan ta haura sama har lokacin hawaye take hawan ma tana yi tana waigena har ta haura stairs din. Ina ganin ta shige na juya ya saci kafa na fice daga bangaren, da kaina na gate din gidan na fice, tafiya kadan na tari abun hawa na hau na fada masa ya kai ni cocin da take kusa a nan garin Kaduna, babu wata daguwar tafiya sai gamu gaban cocin, na gaishe da mai gadin na fada masa ina tafe da matsala ne amman ina son ya bani kudi na sallami mai achaba tukuna babu musu ya biya mai babur din, sannan ya shiga da ni ciki a tunani idan na je ma Ammy kai tsaye ba zata ba ni ana ba dan haka na zabi neman taimakon mutanen cocin bayan na fada musu ina ra'ayin komawa alnahin addinina na Christianity. Sai suka ba ni shawara na fara tafiya dauko yaron har sai idan ta hana tukuna za su shigo ciki, na ba su addireshin gidanta sannan na cire takardar na rubutawa Ammy martanin karyar da ta yi min cewar danta na kirki ne ya banbanta da sauran, domin na san ba lallai na samu tsayawa na fada mata baki da baki ba, amman idan na bata wasikar zata karanta. Su suka ba ni kudin abun hawa na hau achaba na isa unguwar a lokacin ne tsoro ya yaye min saboda ina son ganin ana ta kowane irin hadi, da Allah yayi nufin ba ni nasara ina buga gate din mai gadi ya bude sai da ya dade yana kallona sannan ya gane ni, ya bar ni na shiga ciki na samu falon babu kowa sai ana shi kadai yana kallon Cartoon, na karasa da zafin nama na dauke ana na aje mata takarda a gurin da na dauke shi na fito yana ihu domin shi ma be gane ni ba, mai gadin ya tsaya tambayar ina zan je da yaro na kai masa mugun halbi a gurin da ya fi komai muhimmanci a jikinsa, ba shiri yaja baya na bude gate din na fice da gudu kai kace sato yaron na yi. Ina tafe ina waije ko za'a biya ni amman ban ga sawun kowa ba sai da na samu Achaba na hau sannan Ammy ta biyo ni da motarta tana cewa na tsaya na cewa mai Achaba kar ya tsaya, be tsaya ba sai da muka isa cocin na sauka da guduna na tsaya layin mutanen da cocin ke rabawa tallafi. Ammy ta dade tana kallona har sai da mai gadin ya bude min na shige. TIRKASHI....!!! A tunaninku tsakanin Auren Khaleepa da Turhan a ina Emily ta fi shan wahala? Waya ya fi gallaza mata? Team Turhan kuna da katon aiki a gabanku indai kuna son Emily da Turhan sai kun tanadi makaman sallama _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [6/26, 9:29 PM] : https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL ABOKIN RAYUWA
Chapter 93 · 0% Book details