← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 177

Sashe 112

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

biyayyarka da kuma son farinciki da gujewa bacin raina, gashi kuma ta zo mana da alheri haihuwar da kake ta nema sanadinta ka samu, ko bana raye na san zaka yi alfahari da hakan, kuma na san zaka rike yan'uwa ka rika ziyartarsu, aurenka da Emily zai kara kusancinka da ni, na san yanzu ba zata yarda ta bika ba, amman zata yarda ta zauna a nan, kuma na san a yanzu kam dole zaka bata hakkinta, inda kana son zama da ita kana son yarta dole zaka zo, toh kuma sai ka yi tunanin ba zan taya ka wannan yakin ba?" Kalman Ammy sun kwantar masa da hankali kuma sun saka ya ji sanyi kana sun karfafa nasa guiwa, sai dai hakan be kawar da abun da yake ji na kiyayyar ganin Emily ko magana da ita da Aliyu yake ba, domin baya kusa da ita yanzu. "Tashi ka tafi gurin yarka, ni zan shirya yanzu na tafi gurin Ummi zan yi magana da ita dole ai ayi ma tukar hanci" Turhan ya mike tsaye ya karasa inda Ammy take zaune ya kama hannayenta ya sumbanta sannan ya sumbanci goshinta. "Na gode Ammy" Ya nufi sama, sai ta bi bayansa da kallo tana murmushin jindadi, a yanzu ba a kadai take da shi ba har da jika gashi kuma Emily ta dawo komai zai daidaita ya zama daidai a rayuwarsu. Tashi ta yi ta shiga ciki ta shirya shirin fita kamin ta fito Nurse dake duba jininta ta shigo ta hauro har sama ta auna jinin. "Maa Shaa Allah, Hajiya jiki ya sauka sosai daman Dr yace idan na auna jinin na ga be hau ba, to na fada miki karki sake shan maganinki sai ya shigo anjima zai canja miki da su kuma ya fada miki yadda ya kamata a sha" "Alhamdulillah, hankali na ne ya fara kwanciya yanzu, ciwon sugar ma ina tunanin zai sauka In Shaa Allahu" "Eh shi ma naga jiya ya sauka sosai, Allah ya kara lafiya" "Ameen" Ammy ta janyo jakarta ta ciro kudi mai kauri ta mikawa Nurse din. "Aa Hajiya" "Haba ki karba mana, alheri ne ai ba a maida hannun kyauta baya" Nurse din ta karba tana mata godiya sannan ta fice. Waya Ammy ta janyo ta nemo number Ummi ta kirata sai da wayar ta fara ringing sannan Ammy ta karaa kunne. Ummi ta amsa tare da amsa sallamar da Ammy ta yi, bayan sun gaisa Ammy ta ce. "Ya Aliyu da karfin jikin?" "Alhamdulillah" "Ina son na shigo ne, kina gida ko kina asibiti?" "Ina gida" "Toh gani nan zuwa" Ta aje wayar sannan ta dauki mayafinta ta yafa a jiki ta dauki jakarta ta saka talkaminta ta fice, dakin da Fatima take ta fara turawa a hankali sai ta hangota zaune a kasa Turhan yana zaune gabanta. "Zan tafi" "Okay Allah ya kiyaye Ammy, Wallahi Aliyu yayi min Illa Ammy yarinyar yanzu sunansa kawai take kira sai na mahaifiyarta, tana da hujjar kiran sunan Aisha amman Aliyu fa? Miye hadinta dashi? Yanzu fa ko da na shigo ya kirata a waya magana suke yi" "Ka bi komai a sannu, ai mutum be taba cin amana ya ga nasara a rayuwa ba" "Ni mamana nake so, na tsane ku duka, sace ni kuka yi, Uncle Aliyu zai zo ya dauke ni" Fatima ta fada tana hararar Ammy daman karamin aikinta ne rashin kunya. Ammy ta saki kofar dakin ta shigo ciki ta karaso inda Fatima take zauna ta rikota sai Fatima ta fisge hannunta, Ammy ta sake rikota ta dagota ta nufi gaban madubi da ita ta dorata tsaye akan kujerar madubin, sai Turhan ya taso ya zo ya tsaya kusa da ita yana kallon madubin. Ta cikin madubin Ammy ta nuna mata Turhan tace "Kalli wannan mutunen" Fatima ta kalleshi tana kumbura baki. "Kalli wannan yarinyar" Fatima ta kalli kanta. "Fada min da wa take kama?" Fatima ta kara turo baki ta ki ta yi magana, ba dan kuma bata fahimci me Ammy take fada ba sai dan shakiyancin ba zai barta ta bada amsa ba. "Wannan yarinyar ta yi kama da wannan mutumen ko baki gani ba?" Fatima ta sake kallon Turhan ta cikin madubi ta kalli kanta. "Saboda wacan mutumen shi ne mahaifin wannan yarinyar" "Ba ni da mahaifina Momy ta fada min haka aka haifa ni ba ni da mahaifi, baki ji sunana ba Fatima Emily Aisha" "Aa kina da shi, kowa na duniyar nan yana da uba sai ke kadai ce za ace baki da uba? Kina uba Fatima ni kuma kakarki ce, ke yar dangi ce jinin sarauta daga da baya kuma yar larabawa, kina da uba Fatima kalli ki gani kin taba ganin wani wanda kuka yi kama kamar wannan" Fatima ta juya ta kalleshi. "Meyasa Momy tace bani da Baba? Kuma miyasa be taba zuwa ba?" "Yanzu su ya kamata ki tambaya, kowanensu sai ya baki amsa, amman tabbas wannan mahaifinki ne, daga sunanki ya tashi daga Fatima Emily Aisha, ya kuma Fatima Turhan Muhammed Abdo, idan ba mu da alaka da ke ai ba zai taba yayu mu rike ki mahaifiyarki ta kyale ba" Fatima ta kalleshi da cikin madubi ta ga kamaninsu sosai kuma tana ji ya kwanta mata a rai a matsayin uba tun a ranar daya rungume ta, sai dai kawai bata yarda da su ba ne, domin ba mahaifiyarta ce ta fada mata ba. Fatima ta fashe da kuka "Miyasa Momy tace ba ni da Baba? Idan shi Babana ne miyasa be zo ba shekara da yawa? Yan makarantarmu suna min dariyar sunana, suna cewa ba ni da Baba" "Tsawon lokacin nan, nemanki muke ke da Emily ba mu san inda za mu ganku ba, sai a yanzu da Aliyu ya zo da ke, wata kila shiyasa ya zo dake saboda ya nuna miki mahaifinki ne" "Ina son na yi magana da shi" Ta sauka daga kan kujerar ta nufi inda wayar Aliyu take ta dauka ta mikawa Turhan. "Kira shi" Turhan ya kar i wayar ya rike, har sai da Ammy ta ce. "Kira mata Aliyun" Kamar zai musa sai kuma ya taba number Aliyu ya saka hands-free, yana jin zuciyarsa kamar zata fashe tsabar bakinciki "Hello My Beautiful Angel" "Uncle Aliyuuuuu wani ne a nan yana cewa shi ne Babana da wata tsohuwa, a nan gidan da wannan matar ta kawo ni gaskiya ne? Tun ranar yake cewa shi ne mahaifina, kuma yana kama da ni" Aliyu yayi shiru na dakiku. "Eh mahaifinki ne" "Miyasa Momy tayi min karya tace ba ni da Baba?" "Saboda.... Ta yi tunanin ya rasu ne... Bata son ta fada miki ki shiga damuwa shiyasa take fada miki haka, amman yanzu mun gane yana da rai shiyasa aka kawo ki nan dan ki san shi kuma ki saba da shi, dan haka ki zama yarinyar kirki yi rika jin magana karki ce zaki yi tsiwa kinji ko?" "Ba zaka zo ka dauke ni ba?" "Zan zo amman sai kin kwana biyu kin saba da shi tukuna, sai na zo na dauke ki, ba na san kina son uba ba? Kina son canja sunanki ki hada da na mahaifi to daga yanzu zai canja" "Ba sunanka kace zaka saka min ba? Ni bana son sunan wannan ni bana son shi ni kai nake so, i don't want this old woman and her Son kai nake so da Momy" Ita kawai bata saba da su ba ne, tana son uba amman ta fi sha'awar ace akwai wani wanda ta wani a kusa. "Okay za mu zo ai, amman sai idan kin yi biyayya kin zama yarinyar kirki, bana son rashin magana da tsiwa, idan kina musu fushi ba zan zo ba, amman idan kika zama yarinyar kirki zan zo" "Okay i will be a good girl" "Yauwa, i love you can you say you love me back?" "I love you ka zo da sauri" "Okay bye" Turhan ya kar e wayar ya datse kiran ko da be iya mayarda duka yaren turanci ba ai yana jin abun da yake fada kuma ya fahimci komai, kamar zai buga wayar a kasa sai kuma ya daure ya saki murmushi ya mika mata wayar, sai ta kura masa ido tana ta kallonsa ya rage tsawonsq ya duka daidai ita sai ta matsa jikinsa ta kwanta ya rungume suka zauna a gurin Each and every second sai ta daga kai ta kalleshi ya kalleta tana kuka mai karfi ta ce "Zan fadawa yan makarantarmu ina da Baba, zan tafi kai zan nuna musu, i hate Momy i hate her" Hawaye ya cika idon Turhan Ammy daman tuni ta fara zubar da nata. "Ni ma zan fadawa family ina da ya, ina da kaso a jinjina, zan baki duk wani gata da kika rasa Fatima, ki yi hakuri na zo a makare" Ammy ta share hawayenta tana murmushin farinciki. "A yau zaka kara sanin muhimmanci na Turhan, zaka san abun da ake kira da iyaye, zaka san sha'anin yaya" Ta dauki jakarta ta fice daga dakin tana kara shaye hawayenta, sai da ta fito sannan ta sanar da direban ya fito ya same ta ya bude mata mota ta shiga, ta zauna kenan wayarta ta yi ringing sai ta ciro wayar daga jakarta ta duba sai ta ga bakuwar number. "Sallamu Alaikum" Mai kiran ta amsa mata ta dayan bangaren sannan ta gabatar mata da kanta. "Sunana Hajiya Barakat, amman yara suna kirana da Mama Baraka" "Maa Shaa Allahu, sai dai ban gane ki ba" "Eh to ba mu taba magana ba, ba lallai ki yi saurin gane ni ba, ni step mother din Kameela ce matar Aliyu abokin danki" "Okay Tohm Lafiya?" "Ba lafiya ba, ina son mu yi magana da ke ne akan Emily da kuma yarta Fatima da take gurinku" "Ina saurarenki" "Ba maganar waya ba ce ina son ganinki ne" "Zaki iya zuwa gidana zuwa anjima yanzu dai ina hanyar tafiya wani gurin ne, idan zaki taso sai ki sanar da ni na kwatanta miki" "Tohm shi kenan" Ammy ta sauke wayar tana mamakin kiran, zuciyarta na raya mata wata kila Kameela tana son ta karbe Fatima ne ta maidata gurin Emily saboda Aliyu, ko kuma dai wani abun ne tun
Chapter 112 · 0% Book details