Sashe 39
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ina maka godiya ba, iyayen ba yadda zamu yi da su sai hakuri, mu dai mun san muna son junanmu that's all, wacan a tsakaninsu ne, be kamata ya shafe mu ko ya shiga abun magana a tsakaninmu ba" Be sake ce mata komai ba ya kashe wayar, domin shi ba gwanin sa'in sa ba ne. Dawowa yayi cikin falon ya aje cup din hannunsa sannan ya kira Ummi ringing daya ta daga tana ta masifa. "Anya za a jure a auren nan na ku Aliyu? Har yaushe zaka je ka dauko mata a gidan kananan mutane da ba su san mutunci ba, a nemi wulakanta mu, kayan barkar da aka kai mata ne Hajiya Ramatu ta kira ni wai sun dawo da su, sun raina kenan ko? A gidan su waye za a kai kayan barka na mai jego kadai akwaiti goma ace an raina, alhalin ma a be zo da rai ba" Ya sauke ajiyar zuciya. "Ki yi hakuri Ummi yanzu na kirata take fada min, kin yi kokari sosai, ita da kanta ta yaba shiyasa dazun na kira na miki godiya da abun da kika yi" "Akan su aka fara faduwa zabe ne? Kujerar sanata tuwon gidansu ne da za ace dole ko wane zabe sai sun ci? Yanzu saboda sun fadi Allah yace mahaifinka ne zai ana sai abu ya zama dan zane? Har yana neman zama cin mutunci?" "Ayi hakuri Ummi In Shaa Allahu hakan ba zai sake faruwa ba" "A'uzubillahi wannan hassada ta yi yawa, idan son suke su kashe auren su aura mata Governor su sani dai yarsu ba daraja zata yi a idonsa yanzu ba, kuma wahala kawai zata je ta sha da wannan bakin kishin nata, kuma ya ma yi aurensa me zai yi da ita yanzu" "Ummi kin hau da yawa, Allah ya huci zuciyarki amman dai idan tunaninsu kenan sun yi kuskure domin babu saki tsakanina da Kameela, ko ba ita ba daman na kudurta a raina duk abun da zai faru ba zan taba iya sakin matata ba, kuma na mata magana In Shaa Allahu irin wannan ba zai sake faruwa ba" "It better, domin na fara gajiya sai kace kansu aka fara siyasa, shekara nawa Engr yana hakurin faduwa zabe sai bana dan Allah ya ba shi sai kuma su juyar da siyasa kiyayya" "Ummi ayi hakuri" Ta masa kwatankwacin abun da yayi ma Kameela, ita ta kashe wayar a cikin fushi. Ya sauke ajiyar zuciya. "Daddy ma lalabawa yake da Ummi, balle ni da nake a, iyayen Kameela suna neman kunno min wuta" Ya fada cikin yanayin damuwa. Sai bayan bayan sallah magariba Kameela ta kira shi tana bashi hakuri suka jima suna waya, yawanci abun da take bincikarsa na ina yake cin abinci ne sai kuma inda yake zuwa yanzu da bata gidan. "Ina zan je? Ina gida mana" "Yaushe zaka zo" Soon" "So soon" "Not so soon" "Okay, ka kula min da kanka, kuma dan Allah kar ganin bana nan ya saka ka rika kula mata ko kallonsu" Yayi murmushi kawai ya girgiza kai. "Toh ranki ya dade" Ta yi dariya, ya mata kiss a wayar sannan suka yi sallama. KAMEELA POV. Tana sauke wayar Farida ta shigo kiranta wai Abbansu yana son ganinsu gaba daya a bangarensa, haka suka dunguma gaba daya suka tafi bangarensa suka zauna har Mama Barakat da Kameela ke ta harara. Alhaji Tukur Nazifi Ataka ya fara kallon Hajiya Asma'u ya ce. "Waya ce a mai da kayan barkar da aka kawo?" "Alhaji ba fa wani kayan kirki bane, kamar gidan nan za a kawo kayan barka akwaiti 10, ko ya muke riko a gidan nan ai ta fi karfin haka balle kuma jininka, da gangan suka yi saboda su walakanta mu" A take Alhaji Tukur tsohon sanata ya rufe ta fada. "A wane dalili za a maida? Idan ma sun yi ne saboda abun da kike tunani miyasa za ki fiye masu? Wannan ai rashin dattako ne, kuma ba kowa ya janyo ba sai Kameela, su basa tunanin komai sai soyayya, gashi nan tun ba aje ko'ina ba sai abubuwa ake samu na rashin jindadi, toh daga yau sai yau kar a sake aiko wani abu daga gidan Bappa Mudallab a maida shi, ko ba can ko daga ina ne kar hakan ya sake faruwa" Ya kalli yaransa daga mazan har mata a fusace ya ce. "Ku kuma a cikinku kar wanda ya sake dauko ya ko dan makiyinmu yace sai zai aureshi last warning, shiyasa na tara ku a nan" Mama Barakat ta ce. "Alhaji ayi hakuri, kar a bari siyasa ta yi tasiri akan rayuwar yau da kullum, na san faduwar nan bata yi ma kowa dadi ba, amman kar a hana yara abun da suke so" Hajiya Asma'u taja tsaki. "To ke me kika sani a siyasa Barakat? Da har zaki fadi haka? Siyasa ai mu muka santa ciki da waje, domin Alhaji tun yana ba shi ba nake fadi tashi da shi akan siyasa har ya zama wani abu a yanzu" Alhaji Tukur ya kalli Hajiya Asma'u domin ya san da biyu ta fadi maganar. "Me ya kawo wannan maganar yanzu? Ku tashi na sallami kowa" Mama Barakat ta yi murmushi ta mike tsaye ta fice daga dakin, Hajiya Asma'u ta watsawa bayan Mama Barakat harara ta jin haushin yadda take karkada mazaunai kai kace da gayya take yi. (Mtssss kayan kashi) ta fada a ranta sannan ta mike tsaye suka fice ita da yaranta. ALIYU POV. A yau ya shigo aiki da wuri domin gidan yayi masa ba dadi, saboda hatsaniyar da aka samu tsakanin iyayensa da na Kameela gashi kuma Kameela bata gidan baya jin motsin kowa sai hakan ya saka shi jim gidan yayi masa girma. A nan yayi breastfeed yana gamawa ya kira Kameela suka gaisa ya ji tashinta, a nan ta saka masa kukan yaron da ta haifa ya koma, wai sai a yanzu take jin babu dadi abun yana damunta har mafarki take. Rarrashinta yayi ta yi sannan suka yi sallama, ya dauko qur'anensa dake office din yayi karatu daidai gwargwadon yadda zai iya sannan ya aje bayan yayi addu'a ya amsa kiran Turhan dake shigowa wayarsa ta WhatsApp video call. "Salam.." "Hey Aliyu ya gidan ya aiki?" "Lafiya kalau, ya Ammy?" Aliyu ya tambaya yana karantar ramar da abokinsa yayi. "Tana kaduna" Yanayin yadda ya amsa masa ne ya bashi tabbaci ya bar kasar. "Ka koma Sudan ne" "Eh jiya, abun da naje nema ban samu ba, still Ammy bata duba hakan ba, anyway na kira ne na maka barka matar ta haihu ashe?" "Eh amman yaron be zo da rai ba" "Eh Allah ya baku hakuri, kara kai ai kana haihuwar ba kamar ni ba, ban ma san ya ake ji ba idan aka rumgumi yaro" Tausayinsa kadan ya fada zuciyar Aliyu. "Kai ma wata rana zaka rumgumi yayanka In Shaa Allahu" "Ina fatan haka, agaishe da Madam" "Zata ji" Daga haka suka yi sallama, Aliyu yana jin kansa kamar wani mai laifi, meyasa Emily zata daure shi har haka? Ya kasa fadawa abokinsa a inda take tare da yarsa. Ya dago yana kallon kofar dakin da aka kwankwaso. "Yes" Nick ya shigo ya sanar masa Emily tana son ganinsa, Aliyu yayi shiruuuu yana kallon wani gurin kamin ya bash izinin shigowa da ita. Ya mike tsaye ya nufi windows din office din ya bude ya tsaya a gurin yana kallon kasan benen. Emily ta turo kofar office din ta shigo tana sanye da short gown black color gaba daya ta daure gashin kanta a baya tana rike da makulli mota da wayarta, sai kuma agogonsa a dayan hannunta. Ta dade tana kallon bayansa sannan ta matsa kusa da teburinsa ta dora agogon. "Zumudin zuwa ganin mutumen da ya taimake ni a yau, be bar ni na runtsa ba, da na zo ban san office din ba da tambaya na kawo kaina a nan. Kullum mafarki da buri na yadda zan maida alherin da aka yi min ne da alheri, na kasa manta yadda ka ceto rayuwata, a lokacin da ba ni da kowa babu mai taimako na, Vito yana yawan cewa na jefar da agogon nan ko na manta da shi, sai na fada masa indai har zan iya manta alheri to zan iya mantawa da agogon, manufar ba ta agogon ba ce kawai, ta mamallakinsa ce, ashe kuma na aje kwarya a gurbinta ne, ashe dai ka cancanci ko kasa ka taka na jimke na aje" Ta share hawayen idonta. "Ka taimake ni a lokacin da iyalinka da kai kanka kuke neman taimakon juna na karfafa guiwa, baka damu da addinina ko kazantar da take jikina ko ciwon yarona na ba ka taimake ni, hakika Aliyu kai mutumen kirki ne, kuma na yarda a ciki musulmai akwai na gari" Sai a lokacin ya juyo ya kalleta kallo daya ya dauke idonsa. "Duk abun da na yi na yi ne saboda Allah" "Fada min me zan yi na rama daya bisa ukun abun alheri da ka yi min?" Ya nuna mata kujera sannan shi ma ya zauna. "Wacece ke? Tun farkonki har zuwa yau, yadda kika hadu da Turhan har zuwa rayuwarki ta yanzu, shi kawai nake da bukata a gurinki yanzu" Ta nuna kanta tana hadiye bakin cikin daya tsaya mata. "Ni... i ni ce kawai, ni ce wata yarinya data tashi a gidan marayu bata san kowa ba sai kanta da mafarkinta..." Taja numfashi ta lumshe ido, Aliyu ya kalleta a karo na biyu kwarjin farar fata a cikin bakin tufafi ya cijeshi, ya dauke idonsa da hanzari ya maida akan agogon da ta aje masa. [4/28, 6:57 AM] ABOKIN RAYUWA