← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 177

Sashe 153

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

shi fa ba saurayinta ba ne amman kalamansa sun ratsa ko wane ar go na jikinta, ko Khaleefa da ta san asalin soyayayya suka yi kamin aure be zuba mata baiwarsa kamar haka ba. Ta ko'ina Aliyu ya kai namiji, yana da kyau ga siffar irin ta mazan da suka amsa sunan maza ga addini da dabi'a mai kyau, ga tausayi da kulawa, yana taka tsantsan da ita da bacin ranta, yana kokarin ganin ba su wuce gona da iri ba, ba kamar Turhan da yake sonta a yanzu da ta zama mutum ba kuma ta haifa masa yarinya, ba kamar Vito dake kokarin taba jikinta ko dukanta ba kuma ya tsani yarta, ko da yake shi din ma bata gama sanin waye shi ba, kuma be zama lallai yana sonta ba, ta kan iya yiyuwa ita din ma ba tsarinsa ba ce. Kuma anya ta shirya a yanzu? Bata hankara cewar ta yi nisa ba sai da karar aje plate a dinning din ta dawo da ita duniyar hankalinta, ashe Aliyun ne tsaye a gabanta take kallo bata sani ba, zabura ta yi sai ta lumshe ido tana murmushi. "Kina nan kina lissafina a zuciyarki ko? Kaman ni na, dabi'una siffofina, da kuma tunanin ko haka nake ko zan canja a gaba?" Ta bude ido mamaki ya cika ta. "Ta ya ka sani?" Ya dauki plate ya rufe abincin da be ci ba. "Zuciyata bata karya akan duk wani abu da ya shafe ki, ita take ayyana min abubuwa akanki, shiyasa da kika gudu ta hararon inda kike boya, da kika bar min wasiyar rike Fatima ita ta fada min kina kokarin giving up ne, ta haka nake iya hango hasken dake zuciyarki a game da addinin Musulunci tun kamin na ji labarinki, ita ta taimaka min gurin gasgata gaskiyarki tun gabanin tafi da ni a duniyar tarihinki" Ta lankwafar da kai kamar zata yi kuka ido cike da shagwaba. "Wai kai wane irin mutum ne Aliyu?" Ya nuna kansa. "Wai ni? Mutum ne kawai" "Na musamman?" Ta fada a sigar tambaya. Sai ya dan sirinar da kai kadan ya cire facing cap din dake kansa. "Eh, ga ta musamman..." Ta dauke kai tana murmushin da be taba ziyarta ba, shi ma ya dauke kai yana maida hullarsa hakoransa a bude. Bayan sallah azahar tana Kitchen ita da Ummi suna hada lunch ma Aliyu da be iya cin tuwo miyar kubewa da mai aikin Ummi ta girka ba, sakamakon fitar da Ummi ta yi bata dawo da wuri ba sai ta kira waya cewar mai aikin ta girka. Shi kuma ya ji ba zai iya ci ba saboda be ci wani abin kirki ba da safe ba cikin ya zama empty be shirya sabunta shi da tuwo ba. Ummi na mata zancen komawarsu Abuja a satin da zai shigo, da kuma yadda take ganin kamar Ammy ba zata yarda a tafi da Fatima ba. Emily kuma tana wata duniyar bata ma san me Ummi take fada ba bata komai sai murmushi ta kallon wani gurin alamar hankalinta baya jikinta. Ummi ta taba ta. "Ke... Lafiya?" Emily ta zabura sai kuma ta fashe da siririyar dariya. "Ba komai Ummi" Gogan kamar ya san wainar da ake soyawa, sai ga shi ya shigo kitchen din dubawa idan abinci ya dahu cause he's starving, be ma san da Emily ake girkin ba, sai dai ganin bakin Ummi sake da mamaki jin Emily da fitar da sautin dariya. Ya saka shi tambayar mamakin da ke fuskar Ummi. "Lafiya?" "Aa dariya take yi?" Ya kalli Emily? "Are you okay?" Da Emily ta san Ummi ba ita take kallo ba sai ya turo baki gaba tana murmushi mai dauke da shagwaba ta girgiza masa, ya san kan garin ya fahimcin karatun tun ba a biya masa aya ba, yana son yayi murmushi ba dama saboda Ummi tana Kitchen sai kawai ya dauke kansa ya nufi fridge, a yayin da idon Ummi ya dawo kan Emily sai ta yi hanzarin sauke kanta kasa kamar ba komai. Aliyu ya dauki ruwan da ba su ya shigo sha ba ya fice gonar annashuwa ta ya u a kirjinsa. Sai da ya fice suka kammala shirya komai sannan Emily ta kalli Ummi ta ce "Ummi yanzu idan ina son, na sake zama musulma zan cigaba da ibada ne kawai? Kuma kina ganin Allah zai karbe ni? Zai yafe min barin addinin da na yi a baya?" Ummi ta aje cup din hannunta tana kallon Emily da mamakin abun da ba su yi zatonsa yanzu ba. "Kina son ki dawo musulunci ne?" Emily ta daga kai with so emotional. Numfashin Ummi ya fara rawa saboda farinciki. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" Ta juya ta fice Kitchen din da sauri jikinta har mazari yake. A falo ta samu Aliyu zaune yana durawa cikin ruwa. "Zan fada maka wata magana amman sai ka ba ni tukuici" Ya kalli Ummi gabansa ya dan fadi ba dan tsoro ba sai dan abun da be san miye ba. "Toh Ummi haka nan zan bada tukuici ban san girman albishir din ba? Idan aka min wayo fa?" "Wannan mai nauyi ne, Emily tana son ta musulunta" Ummi ta fada idonta fal da kwalla, Aliyu ya mike tsaye babu shiri ya leka Emily take tsaye bayan Ummi. "Seee.... Riiii.. Seriously?" Emily ta daga mishi kai, ya juya ya juyo ya daga hannunsa sama ya sauke kasa ya jimke. "Yes.... Yes... ALHAMDULILLAH YA ALLAH" Ya saka hannunsa aljihu ya ciro keys din ya bude hannu Ummi ya saka mata ya ciro Atm dinsa ya danka mata. "Ga tukuicinki nan Ummi" Ya rumgume Ummi cikin farinciki da emotional domim babu halin rumgume Emily dake tsaye hannayenta a baya tana lilo da su hawaye na sauko mata. Ya saki Ummi ya karasa gurin da Emily take tsaye. "Da gaske kin shiryawa wannan?" Ta daga kai. "Ba dan cilastawa ko tsana ba?" Ta daga kai. "Karki yi musulunci saboda farantawa kowa, ki yi musulunci da gaskiya da mana da kaunar Allah ta tsoron azabarsa da kwadayin rahamarsa, saboda mutane suna canjawa suna gushewa, Allah baya taba sauyawa yana tare da bawayinsa na gari a kowane irin hali" "Ina son Allah Aliyu, saboda shi zan yi na san shi ya saka min gamsuwar da nake ji, na shirya ko da zan sake shiga halin da na ninki wanda na shiga a baya, ba zan sake kuskuren barin addinin aminci da salama ba" "Ina son zan musuluntar da ke Emily ki min wannan alfarmar" Ta daga mishi kai. "Zan fadi wasu kalmomi ki maimaita da su ake shiga musulunci, saboda shi addini ne mai tsari da dokoki" Ta daga mishi kai tana hawaye. "Ash-hadu an l ha illall h, wa ash-hadu anna Muhammadan ras lull Yana fada tana maimaita da larabci da suka gama ya maimaita mata da hausa. "Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma na shaida cewa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne" Ta maimaita kowace kalmar cikin kuka da aminci da rahama da narkewar zuciya. Aliyu ya duka gabanta ya rike kansa, Ummi ta rumgume ta tana kuka kamar yadda Emily ma take kuka. [8/19, 7:16 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 153 · 0% Book details