Sashe 13
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 6 Sai da ta sauke numfashi sannan ta tura kofar office din ta shiga, ta manta da dokar Amal na neman izini kamin shiga. A gaban teburinta ta dora mata abun da ta siyo sannan taja ta tsaya tana jiran Amal ta gama wayar da ta shigo ta same tana yi. Sai da Amal ta gama wayar sannan ta kalleta a fusace. Wai ke kam baki da tunani ne ko kuma dai rainin wayo ne yayi miki yawa? Zuwanki na farko na miki gargadin shigo min office ba tare da neman izini ba amman baki ji ba ko? Ke ba yarinya ba balle ace za'ayi ta maimaita magana Emily ta kalleta da kyau tana jin babu dadi domin matar dake zaune a gabanta tana mata fada bata wuce sa'arta ba, amman take kokarin wulakantata saboda kawai tana aiki a karkashinta. I'm sorry na manta ne, zan kiyaye next time Better Cewar Amal tana daga bubble tea din da ya zube. Shayewa kika yi? No zubewa yayi by mistake To zan fada a cire min a cikin albashinki, yanzu kuma je ki siyo min wani Okay Emily ta amsa mata sannan ta juya ta fice jiki a sanyaye, cikin rashin jindadi da kasala ta sauka kasa ta sake komawa gurin dazun ta siyo mata wani bubble tea din ta dawo ta hauro sama ta yi knocking ta jira har sai da ta yi mata izini sannan ta tura ta shiga. Saman teburinta ta dora mata tare da atm dinta sannan ta juyo ba tare da tace mata komai ba zata fice sai Amal ta kirata. Emily ta juyo ba tare da tace komai ba, Amal ta nuna mata tulun takardun da suke zube kasa a gafen teburin. Ki dauki wannan ki je ki yi typing dinsu, a yadda kika gansu a papers idan kin gama ki turo min ta email dina Okay In short sannan ta nufi tulun takardun ta dauka ta fice daga office din zuwa nata Office din, Widows din office din ta bude tana kallon titi da kasan building din, hutun minti goma ta yi sannan ta juyo ta zauna a kujerarta ta bude system din ta fara typing tana murmushi kamar ba ita ce ta gama bacin rai a dazun ba. Sai dai abun da baka saba ba, yana da wuyar aiwatarwa musamman a karon farko, bata jima tana yi ba ta fara gajiya, haka dai ta daure ta cigaba da typing har azahar. Bata bar office dinta ba sai 4pm domin bata yarda ta fito ba sai da ta tabbatar ta gama komai, ko da ta fito kusan wasu sun dade ta tafiya gida, few mutane ne suka rage irinta sai kuma ma'aikatan dake gyara kamfanin. Bata samu Taxi ba dan haka ta hau okada ya kaita gida, bayan ta biya shi ta kwankwasa gate din mai gadin ya bude mata ta shiga ciki cike da gajiya, jakarta kawai ta jefar ta shiga kitchen, lunch da Chidimma ta aje mata ta dauka ta fito falo ta fara ci da sauri saboda yunwa. Anya zan iya aikin nan? Haka aikin yake ko kuma dai... Sai kuma ta yi shiru ba tare da ta karasa ba ta cigaba da cin abinci, a gurin da ta ci abincin a gurin ta kwanta ta fara bachin wahala da gajiya bata farka ba sai Magariba. Momy... Ta bude idonta daker domin bachin be isheta ba, ta kalli yarta. Fatima Momy yau kin kwanta da wuri Ta tashi zaune tana murmushi sai a lokacin ta tuna da yaran domin gajiya ta saka ta manta da su. Ina kuka tafi? Chimdimma ta tafi da mu park daga can muka je gidansu. Emily ta kalli Chidimma dake tsaye. Baki fada min ba Yes saboda Oga ya zo bayan kin fita yace na rika fita da su, saboda baki da lokacinsu yanzu kar ya zama suna kadaici a gida, musamman Londom da yake ba lafiyayyen ba Okay amman daga yanzu, karki sake fita da yarana ba tare da kin fada min ba I'm sorry Maa Emily ta mike tsaye ta nufi gurin da danta yake tsaye kusa da Chidimma ta risina tana shafa fuskarsa. My Baby how is your day Ya mata murmushi kawai ya cire hannunta a fuskarshi. Chidimma ta saki hannunsa Sai da safe ranki ya dade Emily ta fahimci Chidimma fushi ta yi dan haka ba ta dakatar da ita daga tafiya ba. Ba zaki karanta mana story book ba? Fadima ta tambaya. Sai mahaifiyarta ta amsa mata. Zan karanta muku, ina da labari mai dadi da zan baku, and zan girka muku dinner mai dadi Tana maganar tana rawa da kai tana murmushi, a take farinciki ya cika fuskarsu, yadda ta fada haka ta aiwatar, tana girka musu abinci tana fada musu yadda ta sha wahalar aiki yau. Ma'aikatar ana aiki da yawa ne Momy? Fatima ta tambaya tana cin abinc. Ina tunanin haka, amman akwai wahala wata zan saba zuwa gaba Ta busar da iskar bakinta, tana shafa kanta. Momy can i ask you something? Yes My Love Me yasa ake sunana ya kasance Fadima Aisha Emily, not Fadima Hamza like London A take Emily ta ji wani kunci da bacin rai ya tunkarota da kamar fada ta ce. Again? Ina tunanin mun gama wannan maganar tuntuni? Momy kowa yana using sunan babanshi, amman ni sai dai na yi using sunanki? Why? Even London ana kiransa London Hamza, why not London Aisha Emily? Emily ta aje spoon din dake hannunta ta mike tsaye. Time to bed I need to know Mom kullum yan makarantarmu sai sun min dariya, Yau ma da nafi gidansu Chidimma an tambaye ni sunana na ce Fadima Aisha Emily sun min dariya Ba na sha fada miki ba ki da Baba ba? London me yasa yake da Baba, Me yasa ake ce masa London Hamza? How many time do i have to told you Babansa ya mutu, ke kuma ban haife ki da ubana ba, haka nan na haife ki But- But, if you ask me one more Question zan doke ki da daren nan Ta fada mata a tsawace. But kin taba cewa Babana musulmi ne, amman ban taba jin sunansa ba Da sauri Emily ta bar dinning din domin ta san idan ta kara minti daya a gurin zata doki Fatima ne, gidan ya rikice mata domin tun a yanzu London ya fara rikicewa yana kuka. Dakinta ta shiga ta zauna bakin gado ta rike kanta tana shafa goshinta a hankali idonta a rufe sai numfashi take maidawa da karfi. Ta kwashe minti talatin a haka sannan ta mike tsaye ta cire rigar jikinta ta shiga bathroom ta yi wanka ta fito ta saka fajamas sannan ta sake dawowa falon ta nufi London da har lokacin kuka yake ta rumgume shi. Ya isa haka ya isa haka gani a nan Jikinsa yayi zafi sosai alamar fever, rage tsayi ta yi ta dago shi daga jikinta ta kalleshi. London saurareni, kukan ya isa haka kaga jikinka ya fara zafi, Fatima London yayi wasa da ruwa? Fatima ta juyar da kai ta rumgume hannayenta ta turo baki gaba tana cigaba da kallon tv ta ba tare da ta amsa mata ba, ita ala dole fushi take. Fatima I'm talking to you...! Emily ta daka mata tsawa har sai da London din ya zabura ya kara fashewa da kuka. Yayi wasa da ruwa Ta amsa mata a dikile sannan ta mike tsaye ta haura sama tana wani halba kafa kamar wata babba. Emily ta rumgume London tana jin kamar ta fashe da kuka, domin babu abun da yake firgitata a yanzu kamar rashin danta, He's not just an autisms yana fama da sickle tana yawan tashin masa lokaci zuwa lokaci, abu kadan yana iya saka ciwon nasa tashi, kusan ta fi wahalar da shi fiye da Autisms domin yana a cikin jikinsa ya zama rayuwarsa da hallintarsa ce a haka, wannan kuma a cikin jininsa take. Daukarsa ta yi ta koma saman cushion ta zauna tana rumgume da shi tana juyawa a hankali, kamin ta aje shi ta tashi ta haura sama ta shiga dakinsa, maganin ta dauko ta sauko ta bude ta bashi sannan ta tallaba shi daker ta haura sama, suna shiga dakinta ya fara kwara amai a jikin sai ta sauke shi da sauri ta rike shi. A nan fa hankalinta ya tashi da sauri ta sake shi ta nufi gurin da ta adana keys din motarta ta dauka da nufo shi ta dauke shi saman duk wani nauyinsa sai ta daina jinsa a lokacin. Kamar ba ita ba haka ta saukowa downstairs din da sauri ta nufi kofar falon ta bude ta shimfidashi a balcony ta nufi gurin da jerin motocin uku na gidan suke ta matsa remote din hannunta domin gane keys din wace motar ce ta dauko. Sai da ta fito da motar sannan ta nufo shi ta dauke shi har lokacin amai yake ta saka shi motar, gaba daya ta gama fita hayyacinta, ko kadan bata son wani abu ya sami yaranta sai take ganin zata ragu ne, domin a halin yanzu bata da wasu family bayan Fatima sa London, kuma ta tabbatar ba zata sami wasu ba, domin alkawarin da ta daukarwa kanta abu ne da take jin babu wani abu da ya isa ya saka zuciyarta kusantar kofar da zata karyashi. Yadda ta ja motar ta fice daga gidan kai kace koyon tuki take bata kware ba, domin jikinta rawa yake ta ko'ina irin rawar nan na wanda ke tsoron faruwar wani abu, each and every second sai ta juya ta kalli danta dake gidan baya tana kiran sunansa, kamin ta isa asibitin gaba daya ta fita hayyacinta, domin bata taba ganin danta yayi amai mai yawa haka kamar yau ba. Babbar asibitin kudi ce da aka saba kwantar da London a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, ba London kadai ba har Fatima da ita kanta Vito ya dauki nauyin a duba su asibitin ta kudi. Ta karbi kati shiga asibitin suka duba bayan motarta sannan ta tuka da karfi ta isa Emergency ta fito a firgice ta tare da ta kashe motar ba haka kuma tashin hankali