Sashe 43
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Oga Shakur da yaronsa da ya kasance bahaushe. Kwakwalwata tana da saurin fahimtar abu, kusan duk abun da na sakawa raina zan iya na kan iya cikin kankanen lokaci, haka ya saka tun ina primary har secondary school ni nake dauko ta daya aji. Sai da na yi wata biyu a gidan sannan na samu damar aron wayar mai aikin Momy kamar yadda muke kiranta na kira number Khaleepa da tuni na haddaceta, da na kira shi kamar zai yi karamar hauka saboda yadda nake ta jiran kirana a koda yaushe, ni kaina sai da na yi kuka, daman dauriya kawai nake amman duk tsawon kwananki da na yi a gidan da jindadin da nake samu bana jin farinciki saboda bana jin muryar Khaleefa. A ranar be iya bachi ba sai da na fita na tambayi mai gadin gidan ya fada min yadda zan masa kwatance ya zo ya same ni a gidan muka gaisa, a nan kam ban da fargaba duk kuwa da kasancewar ban gama sanin halin matar ba, amman dai da alama tana da fahimta kuma tana da kirki ina ganin kamar da alama zata bar ni na auri Khaleepa, ya kawo min waya a ranar keypad da sabon layi saboda ba zai iya jure rashin jina ba, ba tare da fargabar komai ba na karba na shiga da ita gida, ban boye mata ba na nuna mata wayar na fada manta wanda ya kawo min. "Saurayinki ne" Na daga mata kai ina murmushi ita ma ta yi murmushi. "Ashe na kai ga buduwar, bari na fara shirin aure" Na rufe ido ina dariya, ta tambaye ni sunansa da kuma inda muka hadu na fada mata komai, a take yanayinta ya sauya, sai ta karbi wayar hannuna tace zata aje sai idan mai gidanta ya dawo kasancewarsa matafiyi, idan sun tattauna abun da ya dace zata ba ni wayar, ban jidadi ba amman haka na daure na cigaba da waya da Khaleepa da wayar mai aikinta. Wata rana sai ta kira ni tare da mijinta suka zauna da ni suka fada min ilolin da suke cikin auren musulmi, ta yi ta fada min kalamai marasa dadi akan musulmai da kuma yan arewa, ita da mijinta burinta su cusa min kyamar musulmi kamar yadda ake yi sauran yara, ta fada min na yi kankanta da fara soyayya a yanzu, kuma Khaleepa ba ajina ba ne domin shi achaba yake yi, ni kuma a yanzu na kalli irin gidan da nake rayuwa. Soyayya bata da hankali bata ji bata gani, duk ban ji abun da suka fada min ba, a haka na nuna musu ni dai ina son Khaleepa ba zan rabu da shi ba, sai suka saka min dokar ba zai sake zuwa na fita ba, kuma ba zan sake waya da shi ba, haka kuma ba zan ma taba aurensa ba, idan ma ina wannan tunanin na aje. Suka saka min kulli mai tsanani bana zuwa koma'ina daga gida sai makaranta sai kuma idan mun fita siyaya, ko kuma ranar Sunday muna fita zuwa church. Sun min gata sun nuna min soyayya suna kashe min kudi amman duk bana gani saboda Khaleefa ne a rayuwata, kullum cikin kuka da damuwar rashinsa nake, ban sani ba a lokacin ashe hawaye ba su cancanci zuba saboda shi ba. Wata rana mun je Church, na sulale na ari wayar wata mata na kira shi na fada masa dokokin da Momy ta saka min ita da mijinta kuma sun ce ba zan aure shi ba, a wayar ya rika kuka yana fadin Innalillahi idan na rabu da shi zai halaka zai mutu, ni ma na rika kuka ina jin kamar ma na kashe kaina domin ban taba soyayya da kowa ba sai da shi. "Emily zaki iya aurena a kowane hali?" Na rasa taya zan amsa masa. "Amman ba addininmu daya ba Khaleepa" "Karki damu da wannan addinin musulunci ya yarda mu auri wanda ba addininmu daya ba, kuma na san idan kina so na zaki musulunta domin ki aure ni" "Zan iya ina kaunarka sosai Khaleepa" "Emily zaki iya bina mu gudu? Idan ba haka ba ban san wata mafita da nake da ita ba, daga wannan wayar ma ban san ta ina zan sake jin muryarki ba, kuma muna nan ba za su bari mu kasance da juna ba" "Idan mun guda ina zamu je" "zan gudu dake mu koma kaduna gurin iyayena, zaki zauna a can a daura mana aure mu zauna a can" "Ina tsoro ba zan iya ba Khaleepa" Duk wata kalma da zata raunata ni ta sanyaya min guiwa da zuciya sai da ya nemo ta ya fada, amman ban yarda be shi ba. Na koma gida ina ta tunanin mafita amman ban samu ba sai wanda ya kawo, gashi kaunarsa sai kara ruruwa take a zuciyata, da kaina na samu Momy a dakinta ina kuka na fada mata ina son Khaleepa ta bar ni na aureshi, madadin ta tausaya min sai tace idan na sake mata maganarsa sai ta min duka kuma ko zan mutu ba zata taba bari na auri musulmi ba. Ranar mutuwa ce kawai ban yi ba tsabar bakinciki da nadamar kin bin shawarar Khaleepa na bishi mu gudu. Da sati ya zagayo muka je church Momy ta saka pastor ya dafa kaina ya rufe ido yayi min addu'a, bayan an zauna zaman church ana tsaka da wakar church na saci kafa na fice daga cikin church din daman Momy tana zama a gaba ne mu muna zama baya. Na fito na ari wayar mai gadin church din na kira Khaleefa na fada masa yanzu na amince zan bishi mu gudu. Sai ya fada min inda zan je na jira shi, haka kuwa aka yi ba bawa mutumen wayarsa na fice daga church din na tari okada na fada masa inda zai kai ni, ko da na isa na samu Khaleepa a gurin tsabtsab da shi kamar kullum, yana jirana. Ya sallami mai okadan ya goya ni ya tafi da ni wani kangon gidan ya aje ni a nan, be dawo ba sai dare ya dawo da kudi mai yawa ya fada min ya siyar da babur dinsa kudin ne zamu hada da wanda ke gareshi mu tafi garinsu. A gurin ya bar na kauna ni kadai shi kuma ya kwana a inda ya saba washe gari da asuba dai gashi tare da kayansa, ba bishi muka isa tasha ni da shi muka kama hanyar Kaduna. Shi a tsorace ni, a tsoroce hankali be kwanta ba sai da muka isa cikin garin kaduna. Garin da ban taba zuwa ba kuma ban taba saka ran zuwa ba ko a mafarki sai ranar. A cikin tashar ya saka ni saka hijabi, kusan ko'ina muka bi kallona ake saboda farin fatana ba fari ba ne na sauran mutane, fari ne mai haske sosai da ya fi kama da na turawa ga kuma idanuwa blue. Tashar muka bari muka isa wata dabam muka hau motar garinsu Khaleepa, garin da basa son tubaben, basa marasa ba ni, bana tausayin kaddara da kuma kuskure da na aikata, garin da suka koya min hankali da sabon karatu, suka maida ni wulakantacciya. _________________________ A jiya na yi mistake a page 17, na yi page din ne kamin na canja akalar labarin, bayan na canja kuma sai ya zama na manta ban yi editing ba, wadanda suka karanta wanda na yi ba edited one ba, za su ga Nace Emily baka ce, ku manta wannan kuskuren ku shafe shi a Kwakwalwarku, ni yar adamce ina kuskure dole na. Emily fara ce kamar yadda aka fada tun a farkon labarin. Shin zaku iya fada min abu daya zuwa biyu da kuka fahimta a page din yau kawai? Kuna son a karo? Zo na gani a kasa, ance da kare ana biki a gidanku yace mu gani a kasa Ma'ana ku suburbudo comments na suburbudo muku pages Don't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Karku manta ku yi Sharing* [5/1, 8:59 PM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy ABOKIN RAYUWA