Sashe 58
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
sauri. "Idan kina son uba to ki rike Vito a matsayin Ubanki" "Bana son shi" Emily ta dago ta. "Baki da hujjar tsanarsa, kalli gidan da kike zaune, makaranta mai kyau ya saka ki, ya dauki mai girka muku abinci, tufafi sai wanda kika zaba kike sakawa, a ciki wadanda na aura akwai wanda ya bani rabin rayuwar da kike ciki yanzu?" Ta dauke da mari tana daka mata tsawa. "Karki sake min maganar abun da ya shafi ubanki" Fatima ta saka wani irin ihu ta dafe kunci, Emily ta tashi ta bar mata falon. Sai dai bata iya fushi ba dan haka ta dawo ta rarrashi yarta saboda tana jin babu mai rarrashinta sai ita ta rumgumeta, a tare suka kwana kamar yadda ta saba mata a yanzu tun bayan mutuwar London kullum a gado daya take kwana da Fatima. Washe garin ranar bayan Fatima ta tafi makaranta Chidimma tana ta aikin gyara gida Emily ta shirya ta fita saboda tana jin gidan ya mata babu dadi. Taxi ta shiga ta tafi gurin sabuwar kawarta Tasmia daman bayan can ai bata da wani gurin zuwa. Bata same a apartment din nata ba dan haka ta zauna a gurin har sai da Tasmia ta dawo. Da gangan ta yi kamar bata gane Emily ba. "Malama lafiya?" "Lafiya kalau" "Toh na ga kin zauna a nan ne" "Ina jiranki ne" "Kina jirana? Kin san ni ne? Wani abun zan miki ne?" "Haba Tasmia" "Malama ni fa ban san ki ba ban taba ganinki ba" Emily ta mike tsaye. "Karki fara wannan wasa" "Fine na gane ki, amman fa gaskiya ba zaki zo ki janyo min matsala ba" "Bana fatan janyowa kowa matsala, kin tsorata ne?" "Yanzu dai ba wannan ba me kika zo yi nan" Ta yi shiru na mintuna. "Bana da gurin zuwa ne kawai na zabi na zo nan, kuma na ji anje nemana gida na yi zaton ko kece ko Aliyu" "Ba ni ba ce, ni ba zan tafi gidanki ba yanzu kam, Aliyu ma ba shi ba ne domin be taba zuwa nemanki ba" "Okay zan tafi, duk lokacin da kika ji zuciyarki ta natsu da ni, kin san gidana kuma kina da number da wayata, sai anjima" Emily ta tafi ta barta tsaye a gurinta tana binta da kallo. A taxi ta dawo kamar yadda ta tafi a taxi ta shigo gidanta tana share hawaye. A falo ta samu Vito zaune Chidimma na zuba masa ruwa a cups. "Do you take my phone?" Ta tambayi abun da yafi zame mata wajibi a yanzu, domin jiya ta duba ko'ina bata ga wayarta ba. Vito ya k alli Chidimma yayi mata alama da kai sai ta tafi dakinta ta dauko wayar ta mikawa Vito da hannu biyu be karba ya aje cups din dake da sauran ruwa ya kalli Emily, sai ta juya da wayar bangaren Emily da hannu daya ta mika mata. "Akwai wata number data turo miki sako har sau hudu wai ki kirashi ya damu da ke" Emily ta karbi wayar da hannu daya sannan ta ware dayan hannunta ta wanke fuskar Chidimma da mari. "How dare you take my phone? Har ki karanta min sako?" "Ta saman screen na karanta sakon ni ban san password din ba ma, shi ma na kunna wayar ne kawai saboda na tabbatar tana yi saboda faduwar da ta yi a hannuna, bayan haka kuma na kashe ta kamar yadda take" Cewar Chidimma cikin kuka. "Waya aikeki daukar min waya? Tsawon kwanakin nan da na yi ban damu da wayata ba ashe tana gurinki?" "Ba ita ta dauki wayar ba, ni na bata ta aje, amman me zai saka wani ya turo miki sako? Miyasa zai damu da ke?" Vito ya bata amsa sannan ya dora mata da tambaya, Chidimma kuma ta fashe da kuka har da zubewa kasa. "Burinka kai ka raba ni da kowa, so kake ka ga ina rayuwa cikin kunci, matar da na samu mai kyakkyawar zuciya ta rike ni a matsayin kawa yau naje ta nuna bata san ni ba, saboda ka lalata tsakaninmu ka firgitata" Ta dauki ragowar ruwan da ya sha ta watsa masa a fuska. "Ni na saka ya damu, zo ka kashe ni ka huta" Ta wuce fuuuu ta haura sama, binta yayi da kallo sai kuma yayi murmushi ya kalli Chidimma dake ba shi hakurin ruwan da Emily ta watsa masa, ya rikota ya mikar da ita tsaye. "Karki damu" Ya fice ya bar falon. Emily ta shiga dakinta ta zauna tana ta haki kamar wanda ta yi ya i, ta kunna wayar ta cire Password ta shiga messages box dinta na sms sakon Aliyu ne kadai sakon da ya banbanta da sauran sakwanin dake wayarta na Mtn. Ta karanta duka sakwanin sannan ta gwada kiran numbersa. ALIYU POV. "Wato baki ma wani damu da ni ba kalli yadda kika yi kiba kika yi fari" Yana maganar yana kai mata abincin da ta shirya masa a karamin falon mahaifinsu. Ita kuma tana rike da wayarsa tana abun da ta saba yi masa a waya, wato bincike amman har ta yi ta gama bata ga wani abun da zata zarge shi da shi ba. "In ji wa? Wannan kibar fa ta haihuwa ce kowace mace tana yi da muke Video call baka gani ba" "Aa waya ai rage miki kyau take rabin raina" Ya sake kai mata wani spoon din. "Kina nan kina cinyewa Alhaji abinci ko?" Ta yi dariya tana kallon wayar da kira ke shigowa da number da babu suna a jiki, a take ta amsa kiran ta kara a kunne. "Hello... Aliyu..." Ta ji muryar mace tana ambaton sunan mijinta. "Wacece wannan?" "Emily ce" Mai kiran ta amsa mata kai tsaye. "Emily....?" Ta furta da mamaki, Aliyu ya aje Spoon din hannunsa ya mika mata hannu. "Ba ni wayar" Ta mika masa kamar ba ita ba. Aliyu ya dora wayar a kunnensa. "Emily kina lafiya?" "Ina lafiya" "Babu abun da ya same ki?" Kameela ta zaro ido tana sakin baki. "Aa na kira ne saboda na riski sakonka a wayata" "Okay, ina tare da Matata yanzu" Gudun kar zuciyar Kameela ta sosu ko ta yi zargin wani abu ya saka be ce mata zai kirata ba sai kawai ya kashe wayar. Tsabar mamaki Kameela bata san lokacin da ta mike tsaye tana kallon Aliyu ba. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [5/18, 7:55 PM] ABOKIN RAYUWA