Sashe 162
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
damar da za ki saurare ni ba Aisha?" "Wata kila zaka fada min magana marar dadi ne" "Aa dan Allah ki saurare ni" Ta juyo ta matsa kadan ta tsaya tana rumgume da hannayenta. Da ya kalleta sai ya ji kamar be san miye so ba sai a ranar. Cikin yanayi na sanyi jiki da damuwa ya soma magana. "Na san idan na ce ni ne, ba za a barki ki fito ba, saboda ke da mutanen gidan kuna kallona a matsayin makiyinku ne, shiyasa na yi amfani da sunan Mama Baraka" Ba ta dai ce masa komai ba har ya dora. "Aisha zan kara da kara baki hakuri na abubuwan da suka faru tsakaninmu, kasancewarki a rayuwata ya koya min darasi mai yawa, na san zafin so, na san zafin rashi, kuma na san zafin da kika ji lokacin da na juya miki baya, saboda a yanxu ina jin fiye da abun da kika ji, ke kin ji zafi ne kawai amman ba dan kina so na ba, ni kuma yanzu ina fama da tsabanin haka ne. Jiya da dare ban yi bachi ba, ina ganin abubuwan da suka faru kamar a mafarki, amman yau da safe sai na fahimci wani abu, idan kana son mutum ai zaka so farincikinsa ko? In har zaki yi samu farinciki da ni na kasa baki a gidan wani ne, me zai saka ba zan so haka a gareki ba? Idan na ce miki ban yi bakinciki ba na yi karya, ban kuma ce zan warke ba, amman sannu a hankali zan samu salama" Ya hade yawu. "Na gode Aisha, da kiyayyata ko tunanin abun da na miki, da wahala bata saka kin zubar da cikina ko jefar da yata ba, na gode da kika kula da Fatima, na gode da kika yi ma Ammy biyayya gurin aurena, a yayin da ni na kasa yi mata biyayya gurin rike amanarki, kuma ina fatar a duk lokacin da wani abu ya taso na Fatima idan na sanar miki za ki shiga ki tsaya mata kamar yadda kika saba, na kawo ne saboda anjima kadan jirgimu zai daga, zata zauna gurinki na dan lokaci, idan na dawo zan dauketa zan tafi Sudan da ita, na yi magana da Ammy ta amince kuma ina fatan ke ma ba za ki, ki yarda ba, ki yi hakuri amman ba zan iya barin yata ta zauna a gidan wani ba" Hankalin Emily ya tashi. "Fatima ta yi kankanta ka tafi da ita masarautarku, har yanzu bata san ta banbance daidai da rashin daidai ba, ta yi kankanta ta fuskanci kalubale" "Kina tunanin zan iya bari a wulakanta ke da kike mahaifiyarta, balle kuma ita? No babu abun da zai faru" Yana rufe baki Aliyu ya iso kusa da gate din gidan da motarsa. Ya bude motarsa ya fito ya tsaya inda suke, yana kallon Emily da karantar yanayinta sai dai be ce komai ba, ba shi da nufin zafafa domin Turhan uban yarta ne matukar ba yayi kokarin wuce gona da iri ba ne, dole zai bar wata karamar kofa a tsakani. Turhan yayi murmushi yana kallon Aliyu. "Ina taya murna, ka yi nasara, amman ka sani, ba a cin amana kuma a zauna cikin salama, kai ma nadama zata tambaye ka kamar yadda ta tambaye ni a yanzu" "Ba zaka fahimce ni ba, amman Wallahi ban tsare wani abu daga gareka ko daga Emily da nufin na raba tsakaninku ba, kuma ban boye komai da nufin na mallaketa ba, ni da kai da ita, muna zagaye ne da kaddara, a jiya da iyayenka suka zo, Wallahi ban tsammaci zan same ta ba, indai har zan iya cutar da kaina to zan iya cutar da kai Turhan" Turhan ya kalleshi sama da kasa kawai yayi murmushi, ya juya ya bude motarsa ya riko hannun Fatima ya fito da ita, yayi mata alama da ta tafi gurin Mamanta, ta kalli Emily da ke miko mata hannu tana mata murmushi. A gurin Fatima ta murje ido ta rike rigar Babanta da hannu biyu ta juyawa Emily baya. "Fatima sweetheart, za ki zauna gurin Momy yanzu kin ji?" Ta girgiza masa kai ya kara rike rigarsa. Ta kalli Aliyu ta shige da fuskarta a jikin mahaifinta. "Wani abun ka fada mata?" Emily ta tambaya tana jin babu dadi. Turhan ya girgiza kai. "Ban fada mata komai da zai saka ta tsane ki ko ta juya miki baya ba, kina kallona a matsayin makiyinki ne kawai, amman abun ba haka yake ba." Emily ta matsa ta kai hannu ta riko sai Fatima ta buga hannun Emily tana hawaye ta kara rike Babanta. "Tun da bata son zama, zan koma da ita idan ta bukaci ganinki direba zai kawota, ina miki fatan alheri ke da sabon ABOKIN RAYUWA" Emily ta kasa cewa komai idonta ya cika da hawaye bata yi zaton haka daga gurin yarta ba. Turhan ya bude mata mota ta koma ciki ta zauna, ya rufe sannan ya zagaya ta shiga yaja motar ya bar su a gurin tsaye, yana jin wani irin bakinciki da be taba ji ba, amman idan ya juya ya kalli yarsa sai ta ji sassauci. Emily ta bi motar da kallo tana hawaye har ta daina hangota. "Kowa na zauna da shi sai ya juya min baya, har da ya..." Aliyu ya rufe mata baki da sauri, ya juyo da ita ya sakata a kirjinsa ya rumgume, yana shafa bayanta a hankali, babu kalma ki yi hakuri rumgumar kadai sai ta ji hawayenta ya yanke, ta haka take iya gane Aliyu ne ABOKIN RAYUWARTA... Ta dago kai ta kalleshi sai ya sake ta ya saka hannayensa biyu ya share hawayenta. "Kuka be miki wahala ko? Zai na zane hawayen nan da suke bata fuskar matata" Ya bude mata gate yana rike da hannunta. "Shiga gida" Ya saki hannunta ta shiga ciki sannan ya koma motarsa ya yi horn aka bude masa ya shiga ciki. Da ya faka harabar gidan sai da ya tsaya ya jira Emily ta iso ta shiga falon sannan ya bi bayanta. A lokacin da ya shiga falon ya ga babu kowa sai ya jidadi yayi hanzarin kamo hannunta ta baya ya juyo da ita. "Hajiya ba ki gaishe ni ba fa" "Mun gaisa dazun" Ta amsa cikin rada kamar yadda yayi mata. Ya rufe baki ya kashe mata ido. "Aw haka na tuna" Ta cire hannunta da sauri ta nufi hanyar kitchen. Shi kuma ya nufi stairs yana murmushi. Dakin mahaifiyarsa ya shiga ya same tana daura dankwali. "Ummi ina kwana" "Lafiya kalau an shigo?" "Eh, Ummi sai na samu Ayusher a waje" "Eh Hajiya Baraka ce ta zo tana sallama da ita" "Waye yace Mama Baraka ce? Ba ita na samu a waje ba Turhan ne" Ummi ta kalleshi da sauri. "Turhan? Wanda aka aiko ce mana yayi Baraka ce" "Ummi baku bincika ba kuka barta ta fita, yanzu da wani ne da zai cutar da ita fa? Da yanzu ni za a bari a matsala" "Na yi zaton ko tana son magana da ita ne Private, ita ma da ta fita ta ga ba ita ba ce ai sai ta dawo" "To ina zata san wannan idan tana son magana da ita ai ga dakuna ko kuma ta aiko a dauketa, amman sai a bari ta fita a bincika ba kuma ba a bi bayanta" "Aisha ce ba zata san ta dawo ba?" "Eh mana, duka duka nawa Ayusher take? Wannan tunanin ba zai zo mata ba, yanzu ne fa kwakwalwata take girma" Ummi ta saki baki tana kallon Aliyu da a bakin gaskiyarsa yake maganar. "Toh za a kula next time, yanzu dai ka dawo da ita ko yaya?" "Ai ba zan bar yarinya karama a waje ba" Ummi ta yi murmushi kawai ta nufi kofa ya biyo bayanta. A falo suka rabu ta nufi bangaren Daddy shi kuma ya nufi dinning din da matarsa take zaune tare da Nafeesa. Nafeesa na gaishe shi ta mike tsaye ta fice dinning din domin ba su damar karyawa su kadai ba tare da takura ba. "Kika yi serving kanki? Baki bari na zuba miki ba?" Ta mike tsaye. "Bari na zuba maka" "No it's my duty to feed you, zauna zan zuba da kaina" Ta koma ta zauna tana murmushi. Ya zuba ma kansa tana cin abincin yana kallonta har ta aje spoon. "Kin koshi?" Ta daga mishi kai. "Ba ki ci da yawa ba, ko wani abun kike so dabam?" "Aa" Ta amsa, ganin Nafeesa ya saka ta jin kunya sai ta mike tsaye. "Bari na dauko wayata" Aliyu ya juya ya kalli Nafeesa. "Idan kika aje plate din ki dauko mata wayarta" Nafeesa ta amsa da tohm. Emily ta koma ta zauna tana dan jin kunya. Nafeesa ta dauko mata wayar ta kawo tana mata wani kallo na zolaya. Emily ta karba ta rike "Thank you" Nafeesa ta yi murmushi kawai ta koma ciki, sai a lokacin Aliyu ya sake kallonta ya ce. "Kamata yayi ta ce you're welcome Mrs Aliyu ko?" "Idan Ummi ta zo ta same ni a nan zata ce ba ni da kunya" "Haka fa, ke ce mai kunya ni ne marar kunya ko?" Ta yi dariyar da bata shirya ba ta sauke kanta kasa tana taba wayar. A nan ta yi arba da sakon da ya sauya murmushin fuskarta zuwa tashin hankali. Tuna Aliyu na gabanta ya saka ta yi kokarin boyewa da murmushin dole. "Miye?" "Ba komai" "Vito ne? Ko Kameela?" "Miyasa ka zarge su?" "Saboda Turhan be jima da barin gidan nan ba, ba zai yiyu ya miki wani sako na tashin hankali da zai bayyana a fuskarki ba, ko mutuwa yayi ba ke za a sanarwa ba, amman Kameela zata iya aiko miki da sako marar kyau, haka ma Vito, cikin biyu dole a samu daya" "Vito ne" Ta fada kamar zata yi kuka. Aliyu ya tashi daga inda yake zaune ya zagaya gefenta ya karbi wayar. "Congratulations kin yi aure ko? Kin yi min butulci Emily kuma dole ki dandana dacin hakan, ke da wannan Balaraben da ya aure ki, ke da fitinanniyar yarki" Aliyu ya ciro wayarsa ya kwafi number ya saka a wayarsa bayan ya gama karanta sakon,