Sashe 14
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
be barta ta rufe motar ba, ta bude back seat da sauri ta fara janyo danta sai ta ji karfinta ya kare ta gagara fitowa da shi, sai kawai ta fashe da kuka ta saka ihu, securities din da suke tsaye a emergency din suka nufota da sauri suka fito da London da har lokacin amai yake ta shekawa. Nurse suka fito da gado aka dora shi. Dan Allah ku taimaka min kar ya mutu, ku taimaka kar ya mutu Shi ne abun da take ta fada da halshe Ibo tana kuka ta bi bayansu, daya daga cikin security ne ya shiga motarsa ya faka a gurin da aka tana domin aje motoci, ya shiga mata da key din. Tana ta zarya ta kasa tsaye ta kasa zaune, kafarta babu talkami kanta a yamutsa fajamas din dake jikinta ma kadan wandon ya wuce mazaunanta be gama sauka a cinyarta ba, rigar kuma bata da kauri sosai. Kusan kowace fatar jikinta a bude take, ban da kirjinta zuwa kasan cibiyarta. Ga keys din motarki Ta kalli key din sannan ta karba ta rike ta cigaba da zirya kafarta babu talkami, kana kallonta kasan a firgice take, hankalinta kuma be kwanta ba sai da London ya samu saukin aman da yake yayi bachi a dakin da aka sauke shi, Likitan da ya karbe shi ya kalleta yana murmushi. Da sauki ma fa sosai kawai ke ce kika daga hankalinki Be saka yin amai irin wannan mai yawa ba, kuma zafin jikinsa ya wuce kima Ta fada hawaye na sauko mata. Eh amman da sauki sosai, kuma ina son na baki shawara ya kamata ace kuna da likitan dake zuwa yana duba shi akai akai, kin ga kamar irin yanzu, da ace akwai likitan dake duba shi ba sai kin yi wahalar zuwa ba, sai idan abun ya gagara, yana da ki samu likitan da zai duba shi koda yaushe, yadda kike daga hankalinki wata rana ba zaki iya kawoshi asibiti ba Ta daga masa kai, sai ya daga kafadarta alamar karfafa guiwa ya wuce, ita kanta zata so ace akwai likitan dake duba danta duk lokaci, sai dai tasan Vito ba zai yarda ba, domin baya yarda da kowa ya shiga gidanta balle kuma rayuwarta ko ta yaranta, ta yi ta kokarin yin haka yin haka ba sau daya ba amman be amince mata ba. Ta shiga dakin ta rufe kofar a hankali ta karasa kusa da shi tana kallon fuskarsa. Rayuwarta take tunawa a wani dare makamancin wannan da rashin lafiya ta kamata, ita kan ta fishi wahala kwananta uku tana ciwon ciki kamin akaita asibitin, sai kuma aka rasa mai jinyarta domin bata da kowa sai gamon tsintsiya da ragga wato mutanen da aka raine ta a tare da su a gidan marayu. Ta zauna a kujerar dake kusa da gadonta ta kama hannunsa ta rike, jininta ne wannan shi ne kadai zata iya shaidawa duniya cewar ita din daga gareta yake, kuma shi din nata ne, bayan wannan da kanwarsa bata da wani abun tunkaho, da ace ta rasa shi a yau da daren yau ya fi kowane dare muni a gareta. Hannu ta saka ta share hawayen idonta tana tunanin Fatima ta san zata ji tsoron zama ita kadai a gidan gashi bata fito da waya ba balle ta kira Chidimma tace ta shiga ta kwana tare da ita, haka kuma ba zata iya barin anta shi kadai a irin wannan lokacin da bata san karfe nawa ba ta tafi gida. Bachi rabi da rabi ta yi saboda tunanin Fatima, da kuma danta dake tsare da shi, sanyin asuba na fara saukowa ta mike tsaye daga kan kujerar yana mika, kamin ta sirina ta sumbanci danta dake bachi ta shafa kansa zuwa fuskarsa, tana matukar tausayin rayuwarsa saboda yadda tasa kaddarar ta zo, shi din ba kamar sauran yara ba ne, gashi kuma ciwon sickle be barshi yayi walwala ba. Ta dago ta nufi kofar ta bude a hankali ta fice ta rufe, haka ta taka har gurin motarta babu talkamin domin bata zo da su ba, sai da ta yi ta dubawa sannan ta gane gurin da aka aje mata motar. Ta tuka motar cikin natsuwa ta isa gida, sai dai ta yi horn ya kai goma kamin mai gadin ya taso ya bude mata, ta faka a gurin da ta dauki motar ta bude ta fito tana amsa tambayar jikin London da mai gadin yake domin ya ga yadda aka fita da shi. Ya ji sauki Ta amsa a gajiye sannan ta nufi cikin gidan ta bude ta shiga, sama ta haura da sauri ta shiga dakin Fatima, ba karamin dadi ta ji ba ganin Chidimma na rumgume da ita suna bachi, ta yi murmushi kadan sannan ta juya ta fice daga dakin ta shiga nata dakin, tufafin jikinta ta cire ta shiga bandaki ta yi wanka ta fito daure da bathrobe ta daure kanta da tawul. Kitchen ta nufa tana hamma ta kunna gas ta shirya abun karyawa, sannan ta fito a daidai lokacin da Chidimma ta sauko kasa. Good Morning Maa Morning Chi I'm sorry na kwana a nan ne saboda Fatima ta same ni tana ta kuka wai ba zata iya kwana ita kadai ba Kin kyauta na jidadin haka, ga abun karyawa nan na shirya ki shirya yanzu ki tafi asibiti gurin London, saboda zan tafi gurin aiki yanzu, ki fadawa direban Fatima idan ya daukota daga school ya kirani zan fada masa inda nake aiki sai ya kaita saboda kar dawainiyar ta miki yawa, idan na tashi zan biyo asibitin idan sun ba mu sallama sai mu dawo tare Okay Maa Emily ta ratsa gafenta ta haura sama, cikin kankanen lokaci ta shirya ta fito dakinta ta leka dakin Fatima sai ta same ta a bandaki tana wanke bakinta Good Morning My Love Fatima ta juyar da fuska, cikin rashin jindadin abun da ta yi Emily tace Idan kin tashi daga School ki fadawa direbanki ya kira ni, zai kawo ki gurin da nake aiki idan ban tashi ba a lokacin, saboda Chidimma zata tafi asibiti gurin London, ni kuma zan tafi aiki Tana fadar hakan ta ja mata kofar bandakin ta rufe ta fito daga dakin ta sauko kasa tana jin zuciyarta na mata babu dadi, ta karasa dinning wayarta na ringing a karo na uku, tea ta zuba ta daga cup din ta sha rabi sannan ta nufi kofar falon ta bude ta fice. A road din unguwarsu ta amsa kiran Vito dake ta shigowa wayarta, ta sani ba dan baya garin ba da yanzu ya karaso gidanta, domin a ka'ida idan yayi mata kira uku bata daga ba to ba zai yi na hudu ba, zata ganshi gidan ne. Hello Are you okay? Lafiya kike? Ta ji kamar ta ce masa aa ina cikin damuwa kuma ta fada masa London yana asibiti amman bata son daga masa hankali, haka kuma bata son yana shiga al'amurranta kokarin jenye shi take daga jikinta. Yeah I'm fine Dakikun da ta dauka bata ba shi amsa ba ya saka shi fahimtar tana cikin damuwa, daman kuma ya karanci muryarta. Don't lie to me, me ya faru bayan bana nan? Fatima ce kawai bata jin magana Yayi shiru ba tare da ya ce komai ba, sannan ya kashe wayar, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya ta tari okada ta hau ta, be sauketa ko'ina ba sai gurin aikinta. ALIYU POV. 8:36pm... Gaba daya yanayinsa ya canja zuciyarta ta sosu kuma ransa ya bace sosai saboda abun da yayi arba da shi a wayar matarsa. Sai dai a cikin sharudansa akwai kokarin kwantar da hankali da kuma yin uzuri a duk lokacin da wani abun bacin rai ko tashin hankali ya same shi, ya sani ya dara matarsa Aisha Ilmi da goge, kamar yadda ya fita shekaru haka ya fita hankali da zurfin tunani domin hankalin namiji ba daya yake da na mace ba. Ba da'asar bace bincikar wayar matarsa domin ya yarda da ita 100% ko da yake ita bata yi masa irin wannan yarda ba saboda kishi, a duk lokacin da ta samu dama sai ta bincike wayarsa, sai dai tana daga masa kafa domin bata taba daukar wayarsa ta bincika ta same shi yana chatting da mata ba, ko wani abu makamancin wannan, abu ne da ya daukarwa kanta nisanta wayarsa da duk wani abu da zai dauki hankalinsa daga matarsa a lokacin da tafi bukatarsa a kusa da ita. Ya haddace password din wayarta, ita ma ta haddace masa saboda yarda da suka yi da junansu. Ya aje wayar yana kokarin saita kansa, domin be kamata ya nuna mata bacin ransa a yanzu ba, ko ba komai tana dauke da juna biyu zata iya damuwa, haka kuma ba zama lallai abun da yayi arba da shi a wayarta ya zama wata illa ko laifi a idonta ba. Ta kalleshi bayan ta sallame sallar Isha'i tana murmushi. Ki yi min addu'a Ai kullum ina maka addu'a amman cewa nake Allah yasa daga ni babu kari Ya daga kafadunsa yana murmushi mai sauti. Daman ai daga ke babu kari, wai baki yarda da alkawarin da na yi miki ba? Na yarda mana, amman matan yanzu fa shaidanu ne, kai dai Allah dai ya tsare kawai kuma ya kawar da idonka Ameen Ya girgiza kai ya kai hannu ya dauki dabinon ajwa ya kai bakinsa, sai da ta kammala addu'ar sannan ta dawo kusa da shi ta zauna ta cire hijab din. Janta yayi a hankali ya kwantar jikinsa. My one and only ina bukatar tuna miki wani abu, kuma ina son ki dauke shi serious Ta dago kadan ta kalleshi. Minene? Sirrinmu sirrinmu ne, be kamata wani ya ji ba, musamman na auratayya, yadda muke mu'amala da duk wani abu da ya shafi gonarmu be kamata wani ya sani ba Gabanta ya fadi, domin ta fahimci kalamansa sai dai kunya irin na wanda aka tsinkawa zane a kasuwa ba zai barta ta nuna masa ta fahimci nufinsa ba. Ni bana gane yarenka ka fito fili ka fada min abun da kake nufi Ya tashi zaune da kyau ya fuskanceta. I'm sorry na shi whatsapp dinki na san be kamata na shiga ba