← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 177

Sashe 106

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai ta rasa me zata yi, bata gane gidan Ammy a yanzu balle ta je ya dauko yarta idan ma tana ganewa bata son abun da zai maida ita gidan har abada, wannan ya saka no matter how much she try dole ne ta dorawa Aliyu laifi domin shi ne silar faruwar komai. Mai Napep din ya sauke ta gurin wani katon Shagon pos ta fita ta shiga ciki ta yi musu transfer ta waya suka bata cashi ta sallami mai Napep din sannan ta cigaba da tafiya a kasa bata san inda zata je and bata san me zata yi ba babu abin da take bukata sai yarta, wata zuciyar na raya mata taje office station ta fada musu dauke mata yarinya aka aka kaita gidan sai dai kuma ko ta fada bata san yadda zata kwatanta gidan ba. Guri ta samu da babu haske sosai ta zauna, ta sake gwada layin Aliyu shiru be shiga ba, daga baya kuma ya shiga yayi ta ringing ba a daga ba. Duk abun da take Turhan na can gefe a mota yana kallonta bata sani ba, idan ta matsa gaba sai yaja motar ya biyota, ta yi tafiya sosai akafa tana take tana sake sake ta shafa kanta ta daga kai sama ta sauke ta sauke ajiyar zuciya amman ta rasa samu mafita ko daya. Daga karshe wata zuciyar ta raya ta koma gidan Aliyu wata kila zai dawo ko ya dawo, ko be dawo ba komai daren dadewa dole ya dawo ai, shi ya kamata ya dawo mata da yarta. Fitowa ta yi cikin haske ta isa gaban Titin da kyau ta tari Napep ta hau tana kwatanta masa inda zai kaita domin ba sanin sunan unguwar ta yi ba, mai napep yana tafe Turhan na bayansu har suka isa bakin gate din gidan Aliyu, yana ganin haka wani bakinciki ya sake rufe shi, ba mamaki sun shirya da Aliyu ne yace ta dawo gidan domin ya ga tana taba wayarta a dazun. Sai da shiga gidan sannan ya matsa yayi fakin gaban gate din ya fita yayi knocking mai gadin ya bude. "Aliyu ya dawo?" "Aa be dawo ba tun da ya fita, bakuwar da ya zo da ita ce kawai ta dawo" "Okay" Ya saka kafarsa ya shiga cikin gida sai kuma ya juyo ya tambayi mai gadin. "Dan Allah kwanan bakuwar nan nawa a gidan nan?" "Gaskiya yau ta zo" "Amman kamin yau ka taba ganinta a gidan nan?" "Aa Wallahi ban taba ganinta ba sai yau" "Okay" Ya nufi cikin gidan, sanin idan ya shigo da motarsa zai iya janyo hankalin Emily ta san ya dawo gidan, zata iya ficewa ta sake barin gidan ya saka shi barin motar a waje ya tsaya kofar falon cikin rashin natsuwar tsayuwar what if mai gadin karya yake masa Aliyu yana ciki? Ya duba harabat gidan be ga kamanin motar da Aliyu ya tafi da ita gidansu ba. Ya biyo sawunta ne kawai saboda kar ta bace masa domin tsawon lokacin da ya dauka yana nemanta yanzu kuma ya same shi ta ba zai bari ta masa nisa ba saboda Ammy. Yana jin kamar ya bude kofar falon ya shiga be da kuzarin haka, wayarsa ya ciro ya kira layin mahaifiyarsa ya sauka daga gurin ya nufi gate. "Hello Ammy kar fa Aliyu ya dawo ya lallaba ki ki ba shi yarinyar nan" "Ai ko hauka nake ba zan ba shi ita ba, kai dai ka yi kokari ka gyara laifinka, karka damu da wannan ka gyara kuskurenka" Ya kashe wayar, a gurin mai gadin ya karbi ruwa yayi alwala suka ba shi abun sallah yayi sallah Magariba da Isha'i, mai gadi da yaron gidan suna gefe suna ta shawarar me ya kamata su yi domin sun kira kira wayar Aliyu ta shiga tana ringing amman ba daga ba, gashi su ba su gane kan abun da yake faruwa ba. Turhan ya zauna a gurin har karfe goma sha daya na dare, baya son ya tafi ya barta kar tafita be san inda zata je ba, ko kuma kar ya tafi Aliyu ya dawo, ko da yake yarta na gurinsu ya san abu ne mai wahala ta iya yin nisa. Tunawa da Fatima ya jafashi a wata duniyar tunani, ya tashi ya fita wajen gate din inda motarsa take ya bude motar ya shiga ya zauna a ciki yayi mata key ya gyara farkin din ya gitta motar ta gaban gate din ta yadda babu wata mota da zata iya fita ko ta shiga sai ya sani, sannan ya kwantar da kujerar motarsa ya kwanta a ciki yana tuna abun da ya faru a dazun na taba jikin Fatima da yayi, gani yake kamar ba gaske ba ne, ace yana da ya, ba dan be yarda ba yarsa even though dna is the best way da zata tabbatar da haka, amman duk sign ya bayyana dake nuna Fatima jininsa ce, yana mamakin yadda yake ta kwadayi da kewar yara ashe akwai jininsa a doro masa be sani ba, lallai Aliyu ba karamin makiyinsa ba ne, yana daukarsa aboki ashe yana nan yana masa Zagon kasa be sani ba, daman duniya ta gaji haka mutanen da ka aminta da su su suke fara cin amanarka. Ya sake kiran Ammy domin idonsa sun soma kaikayin son sake ganin Fatima, and his mine yana jin kamar za'a iya Ammy wayo a karbi yarinyar ba tare da ya sani ba. "Ammy ina Fatima take?" "Gata nan a cinyata tana bachi, she told me everything Mamanta ta fada mata bata da uba! Haka aka haifeta, kuka take daker ta yi bachi ita ma tana son ganin mahaifiyarta" Ya kashe wayar jiki a amace. Sai kuma ya fita ya shiga cikin gidan ya bude gate din da kansa a hankali saboda kar yayi makin sound din da Emily zata san wani ya shigo gidan, mai gadi ya rika masa dayan gate din ya fita ya shigo da motarsa yayi farkin gurin da babu haske sosai nesa da entrance din gidan, ya kwanta jikim kujerar motar, tambayar farko da ya fara yi ma kansa why Emily zata ce mata bata da uba? Kamin ya tuna ranar da alaka ta kullu tsakaninsa da Emily by mistake, ashe be sani ba Allah yayi nufin ba shi ya ta hanyarta ne, ya busar da iskar bakinsa ya kwanta jikin motar yana kallon gate din gidan yana tuna zaman da suka yi a masarautarsu. Abubuwan da suka faru a baya yake ta tariyowa, yana tuna inda ya kamata ya nemeta kuma ya gwada hakan mutanen da suka karbe mahaifinsa ya tabbatar masa da cewar ta gudu, ba zai iya matsawa mahaifinsa lamba a domin yayi masa karya tun farko, amman zai iya tunawa ransa ya bace sosai ya ji babu dadi a lokacin da ya dawo ya samu mahaifinsa ya bada ita a matsayin kyauta, gurin matar abokinsa data nuna tana shaa'war abata ita, kuma ya nuna mahaifinsa rashin jindadin hakan ya nuna masa baiwar daga bangaren mahaifiyarsa take a gurin tana da daraja fiye da sauran bayin da suke nan. Misalin karfe biyu na dare ya fita motarsa ya bar kofar a bude ya taka har gurin Entrance din ya leka windows din baya iya hango komai dake ciki saboda a rufe suke, amman yana iya jiyo sautin kuka, a gurin ya tsaya kansa a kasa yana saurarenta har sai da ta ji shiru sannan yayi jihadi ya karasa gurin kofar falon ya murda a hankali without making a sound ya tura ya leka ciki, sai ya hangota zauna akan kujera tana bachi, janyo kofar yayi ya rufe ya dawo cikin motarsa ya zauna, a gurin ya kwana har asuba, idan bachi ya debe shi sai yayi maza ya bude idon. EMILY POV. Akan kujera ta kwana zaune bayan ta gama zirga zirgar safa da marwa a falon ta yi ta gwada layin Aliyu ba a daga ba, daga baya ma sai ta ji wayar a kashe, bata san inda zata je ba. No matter how much she try sai da ta kasa rike kanta misalin karfe 2 na dare ta fashe da kuka kuka sosai har sautinsa yana fita, sai da ta yi kukan ta gaji sannan bachi yayi gaba da ita. Bata farka sai 7am shi ma ta ji sanyi ya soma mata yawa ne, sai ta warware rigar Dr AB ta saka a jikinta ta rufe zip din ta saka hannayenta a aljihun jacket din sai tda nufin sararawa sai ta ji abu a ciki, ta lalaba ta ciro arba ta yi da card din Dr A-B mai dauke da email dinsa da number wayarsa da kuma sunansa Business Card mai kyau classic one. Tana rike da card din tana kallo da shafawa kira ya shigo wayarta da sauri ta dauki wayar sai dai ganin number Vito ya katse hanzarinta, bata gama tunanin abun da zata tsara masa ba ta samu kanta ta amsa kiran domin shi ne kadai mutumen da baya betraying dinta. "Hello" "Kina ina?" Ta hade yawu, ta yi shiru. "Kaduna ko?" Ta ji gabanta ya fadi. "Wani abun ne ya taso min da ban yi zato ba shiyasa na tafo" "I can't lie again Emily, wannan ogan na gurin aikin ku kika bi? Butulcin ne kika fara tun yanzu ko?" "No no nooo ba abun da kake tunani ba ne, na san ka yi min gargadi amman kuskure na aikata na bawa Aliyu Fatima ya zo da ita Kaduna va tare da sani na ba, kuma yanzu Turhan ya karbeta ina..." "Good, so me kika son na yi yanzu? Na yi fada da shi? Ko ke na sake yarda da ke? Ko kuma na yarda da duk wannan karyar da kika shirya? Na saka wasu kananan yan iska sun bawa boss dinki warning it's just a warning before i come" "What do you mean?" "Je ki tambaye shi idan rayu" Ya katse wayar. Kirjin Emily ya shiga bugawa da mugun karfi, ta sake gwada number Aliyu a nan ma ta shiga kuma sai ta yi sa'a aka daga kiran. "Hello" "Mai wayar yana asibiti" "Wace Asibiti?" Ta tambaya aka fada mata sai ta nufi kofar falon ta bude ta fitada sauri ta
Chapter 106 · 0% Book details