Sashe 41
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ina kallon sama, yadda taurarin suka jera abun ya burgeni sosai, sun yi ma sama ado sai sheki suke, kirgasu na fara yi da yatsana duk kuwa da kasancewar na san ba zan taba iya kirgesu su duka ba, wata maganar taurari ce dake cikin Bible ta fada min a rai. "Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya one su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel" Murmushi nai ina mamakin yadda wani zai iya kona taurarin nan na samaniya har ya kwashe tokarsu. Wani lokacin bana son zufafa bincike akan addini na amman ina ganin kamar akwai gyara a litattafin bible domin kuwa wasu kalaman ko nace surorin da suke ciki sai kaji kamar abun ba zai yiyu ba wani abun ma nakanji kamar labari ne irin na shaci fadi. "Kina nan kina aikin kallon taurari ko?" Maganar marry ce tasa na dawo da dubana izuwa gareta, kokarin zama take kusa da ni. "Wata rana za ki zauna tare da mijinki ku kirga taurari" Na kalleta "Marry kina da ban dariya" "Miyasa na ke baki dariya idan nai maganar miji? Baki taba daukar hakan da gaske ba" Shiru nai kamin na ce mata. "Ina ganin wani abun kamar ba zai faru ba, akwai wadanda suka girmemu a nan gidan kuma suna nan basu yi aure ba balle kuma ni da ke, balle ma ba zamu auri mutumen da zai ga girman mu saboda ba mu da iyaye" "Wata kila ke din kina da iyaye Emily, ina ji a raina kamar muna da iyaye yawancin mu da muke gidan marayu muna rayuwa kawai a matsayin marayu, amman wasu iyayensu sun yi cikinsu ne sun jefar da su" "Indai har haka iyayena suka min bana kaunar ganinsu, domin sune silar shigata wannan hali" "Idan kuma iyayenki suna tsoron ki wahala ne suka kawo ki nan fa? Ko kuma wani ne ya sace ki ya kawo ki nan?" "Zan iya yafe musu idan wani ne ya kawo ni nan, zan yafe musu amman talauci ba hujja bace komai talaucinsu kara su yi hakuri da ni a haka mu zauna a haka, tun da suka kasa hakurin zama da ni ba zan yafe musu ba" Na fada idanuwa na cika da kwalla, sai ta saka hannunta ta lakamoni. "Zaki yafe mata Emily, lokacin da mijinki zai risina a gabanki ya roka mata yafiyarki ba kisan lokacin da za ki yafe ba" "Ba zan iya yafewa ba marry, i just can't" Dariya tai jin yadda nai maganar ina son yin kuka. Mun dade zaune a gurin sannan muka tashi muka shiga block din mu ta nufi dakinta ni ma na nufi namu. Babu wuta a dakin amman an kunna hitila kamar yadda aka saba idan ba wutar, ban kula kowa ba dukuwa da irin wasan da abokina na dakin ke jana da ita, ganin bana cikin yanayin wasan yasa suka kyaleni na hau gado na kwanta wata kofar tunanin ta bude min. 'Suwaye iyayena? Yarbawa ne, igbo ne ko ibra ko hausawa? Ban sani ba, wane addini suke? Miyasa suka jefar da ni? Basa sona ko wani dalilin ne na dabam?' Da wannan tunanin nai bachi kuma har gari ya waye ban samu amsar tambayoyina ba. Ban farka da wuri ba kasancewar ban yi bachi da wuri ba, shiga nai bandakin mu dake can kusa da kofar shigowa dakin nai fitsari ba tare da tsarki ba na wanke bakina kuma nai wanka sannan na fito. Mai kawai na shafa, ni ma ina da kyau kamar mutumen jiya duk kuwa da kasancewarsa namiji. Karamin wandon jean na saka wanda iyakar tsayinsa guiwa na saka wata t-shirt black na dauko kofina na jika gari na sha domin an san by this time an gama raba abincin safe kuma wanda be je ya karbo ba ba za a aje masa ba indai ba wani ne ya karbo masa ba. Bayan na gama sha na rufe waduruf din na saka wukata a aljihu tare da makullin lokar na dauki jacket dita na daura a kwankwaso na sannan na fito zuwa gurin gyaran mota wato gurin aikina. Nayi ta sauri a hanya ganin na yi latti ba kasafai nake son oga na rigana zuwa gurin ba, naje latti sai dai duk da haka oga Abdulshakur be fito ba wata kila wani abun ya tsayar da shi a gida ko wani gurin, rigar aikin na dauka na dora saman tufafina na soma gyara gurin sannan fito da kayan aikin a waje, na kusan awa biyu a gurin sannan ya iso. Cikin girmamawa na gaishe shi ya amsa min da far'a kamar kullum, sannan ya shiga aikin gyara motocin da ke gurin a lokacin ne mutane suka fara zuwa ciki kuwa har da yaran da muke aikin tare da su yan gareji. Ni nake tsaye kusa da shi ina aikin miko masa abubuwan bukata kamin ya bani list din abubuwan da zan je na siyo a kasuwar da ake siyar da jarafuna a unguwar Orile Iganmu a nan lagos. Zuwa nai dakin dake garejen na cire rigar aikin na dawo ya bani kudi na saka a aljihu sannan na kama hanya. Ba mu da nisa sosai da unguwar dan tafiyar bata wuce ta awa daya da rabi ba, so i decided naje a kafa na rike kudin babur din ko wani abu zan iya siya da su. Na tafiyar minti arba'in kamin na kama hanyar da ke kusa da kasuwar, hanyar kamar unguwarmu take babu mutane sosai duk kuwa da kasancewar da rana ne. Gungun wasu mutane na hango za su kai mutum hudu zuwa biyar a tsaye gefen titin, ban ji tsoron ganin mutanen masu kama da yan ta'adda ba domin na saba ganin irinsu da ma wadanda suk fisu a lagos. Ban lura da abunda suke da niyar aikatawa ba har sai da na isa kusa da su, mutumem jiya ne suke kokarin karbewa mashin suna masa barazana da katuwar wukar da ke hannunsa. "Bamu makulli" Dayan ya fada da yaren turanci ni kuma na katsa masa tsawa da yaren yarbancin ganin zagen fuskarsa da yana nuna cewar shi bayarabe ne. "Ba zai bayar ba, ku kananen yan iskane da kuke yawo da wuka, kuma duk wanda ya kuskura ya taba shi ai cikinku sai nasa an kasheshi ba kune yan apapa ba?" Duk tsayawa sukai cirkocirko suna kallona yadda nai musu barazanar yasa sun dan tsorota, ban san su ban san yan ina ba ne amman yawacin yan iskan lagos apapa suke, sun dauka a yadda nai musu kamar na sansu ne ko kuma ina da wani mai tsaya min ne. "Wacece ke?" Dayan ya tambaya da yaren yarbancin kamar yadda nai masa magana dazu. "Idan kun taba ni zaku san ko wacece ni" Na fada ina zaro wukar dake cikin aljihuna na nuna musu ina yatsine fuska kamar yar ta'addar gaske. "Ku wuce daga nan" Kamar umarnina suke jira suka kama hanya suka kyaleshi suna ta waigena. Sai da suka wuce sannan ya kalleshi na ce "Kai sakarene zaka tsaya haka a kwace maka babur?" "Kamar ke ce yarinyar da kika taimake ni jiya" Ya fada cike da mamaki yana nuna ni. "Yes kuma yau ma na taimakeka ba, dan ka zama dolo" Murmushi yai. "No ina tsorone amman kin san su ne?" "Ai a lagos ba dole sai ka san kowa ba, as long as kasan sana'ar mutun barazana kawai zaka masa, idan har kace kyalewa zaka yi kowa zai cuce ka ne, shiyasa na ke yawo da wukata" Na fada ina maida wukar aljihuna sannan na kama hanya tafiya kasuwa ta ba tare da na jira abunda zai ce min ba. "Na gode Emily" Ya fada sai na juyo na kalleshi ina murmushi. "Baka manta sunana ba?" "Taya zan manta sunan Jaruma" Ya fada da dariya nima dariyar nai na cigaba da tafiyata. _________________________ Want more? *Comment* *Share* *Follow* my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 [4/29, 6:17 PM] ABOKIN RAYUWA