← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 177

Sashe 141

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki. Ni da ita muka yi ta gudu muka barki kina kuka, ni ma ina kuka. Tun daga ranar mafarkinki be bar ni ba, ban kuma sake zuwa aikin ba, an aiko har inda nake nemana na sanar musu ba ni da lafiya, da kansa ya zo dubani amman ban fada masa ba, matarsa ma ta zo duba ni ita ma bata sani ba. Tsoron yadda duniya zata kalle ya saka ban waiwayeki ba, wata kila sun ga kin yi kama da turawa ne suka saka miki Emily, ko kuma basa bukatar musulmai ne, domin bayan na aje ki na sake bi da gurin sai na ga gidan marayun na Christian ne karkashin kulawar wata coci. Daga lokacin kuma zaman garin be sake min dadi ba, sai na tattara na koma garinmu da zama, dan abun da na tara na cigaba da kasuwancina da shi, ban yi wata uku na miji aure ya fito min daga dangin mahaifiyata na aure shi, ba mu dade ba ya rasu kuma ban haihuwa da shi ba, bayan rasuwarsa rayuwa ta cigaba na kama sana'a duk inda na ji ana neman aiki na kan kusa na nema ni ma, amman ban yi nasara ba sai a wani banki da ke kusa da mu. Sanadin wannan aikin na hadu da mijin da nake aure yanzu, kasancewar dan kasuwa a wacan lokaci ya kan siya abubuwa daga arewa ya shigo da su gurinmu, na gurinmu kuma ya dauka ya shiga da su, wata rana ya samu matsala ya zo bank a nan muka hadu. Har ta kai ya san gidanmu ya fada min labarinsa kuma ya nuna yana son ya aureni, da farko iyayena ba su amince ba, saboda suna ganin bahaushen mutum baya rike aure tun a wacan lokaci sai dai kudin da yake da su sun taka rawa gurin amincewar iyayena, ni kuma ina hangen yadda bahaushe yake wadata matarsa da komai ba sai taje nema ba, a wacan zamanin mazan hausawa suna daukar nauyin dawainiyar iyalansu ne. Da haka aka amince muka yi aure ya dawo da ni gidansa a garinsu, a nan kuma wani tashin hankali ya same ni, domin matarsa fitinanniya ce yayansa kuma fitsararru ne, sai dai yarda da yake da ni da kuma yadda yake kaunata ya taimaka min wajen jure zama da su, sannu a hankali likkafa ta yi gaba arziki ya kara bunkasa har siyasa ta shigo ciki, zuri'a kuma ta samu, ta karkashin kasuwancin ya zama bashi da uban gida sai Alhaji Bello Bulama wani mutumen Maiduguri ne wanda ya shahara ciki da wajen kasar nan ta bangaren kasuwanci. Ba zan yi karya ba, mijin da nake aure a yanzu yana sona sosai domin ba ni da hayani duk kuwa da kasancewa ta bayarabiya wasu sukan ce yarbawa suna da fada, amman ni na sha banban, kuma na rike matarsa da yayansa da amana, sannan ni ce yar boko kusan duk inda zai shiga da ni yake zuwa, idan wani abu ya taso ma kasuwanci na kan ba shi shawara kuma idan ya bi sai ayi nasara, wannan ya saka har maigidansa ya san da ni, da muka tafi gidan muka samu tarba daga matarsa wacce ta kasance mai son mutane kuma ita ma yar kasuwa, muna gaisawa ni da ita muka gane juna, ita ce matar da na yi aiki da mijinta kuma mijinta ya amintar da ita da ni. A nan ta fada min sun rabu da mijinta saboda baya son haihuwa kuma yana da wata mata a can bata sani ba sai da lokacin da zai koma garinsu yayi ya koma da ita, daga baya ta gano yana da wasu iyalan kuma ita baya son ta haihu da shi, ashe a can idan ka saki mace sai ka bata rabin dukiyarka musamman idan akwai yara, ta shigar da kara kotu ta rabu da shi aka danka mata dukiya mai yawa sai ta siyar da komai ta bar kasa ta dawo garinta na Lagos ta fara kasuwanci ta fada min bayan dawowarta yarta ta rasu ya rage yaro ne kadai take da shi. Ta sake wani aure sai ta auri musulmi wanda ya kasance Alhaji Bello Bulama, mai gidan maigidana a bangaren kasuwanci, da haka ni ma na shiga cikin mukarrabanta, ta ja ni a kusa tana saka ni cikin huldodinta. Idan mijinta yayi tafiya ya dawo ko'ina mai gidana yake zai aje abun da yake yaje ya yarboshi, ba shi kadai ba kusan duk yaran da suke karkashinsa haka suke, idan zai tafi daga Kaduna tare muke zuwa saboda yana ganin mun san juna ni da ita kuma muna da kyakkyawar fahimta. A lokacin da suka dawo daga Sudan muka tarbe su har ta hado ni da ke, ina ganinki jikina ya ba ni, ba na gane ki ba, na sanin ni ma ina da a mai kama da turawa a wani gurin da ban sani ba ko tana raye ko a mace, amman daga lokacin da muka shigo jirgi kika ba ni labarinki sai na kasa rike kaina a kamaninki suka bayyanar min fuskar mutumen da na bi son zuciya na biye masa na lalata rayuwata. Na tsorata kuma na yi bakinciki da halin da na ganki kuma kika fada min domin ni ce silar komai na san dole ina da kaso mai tsoka na zunubin abun da na aikata da kuma yadda kika tsinci kanki a matsayin kirista, mun shigo gidana kamin na haura sama na sauko kin gudu, a lokacin na ji babu dadi, amman ban neme ki ba saboda ban san yadda zan fuskance ki ba, kuma ban san kalar amsar tambayoyin da zaki min ba, kuma ban san da wane ido zan kalli yayana da mijina ba, ga ni da kishiya mai zafin kishi da yayanta marasa tarbiya. Amman a yanzu na gane kuskurena na fadawa mijina komai kowa ya san ke yata ce, a daren da na mari Kameela mahaifinta ya same ni da zance tare da neman dalili na fada masa komai ban boye ba, sai ya zabi ya sake ni amman baya son na bar gidan saboda yaransa da kuma gudun makiya kar su masa dariya, yace na yi zaman yayana. Ni kuma na amince na zauna ne kawai saboda baki zo ba, na fadawa yayana daga lokacin da muka gano inda kike kika dawo gareni, zan koma gidana da na siya ne mu zauna ba a gidan da zaki ji wata magana marar dadi ko ayi miki kallon banza ba, idan sun yarda sun ni falillahil Hamdu, idan kuma suka zabi zama gidan ubansu, ni dai ke ce damuwa Aisha... Tun da Mama Baraka take bata labarin Emily ta rufe fuska tana ta sharbar kuka. Mama Baraka ta sauka kwanta a kasa irin na mai neman gafara ta hade hannayenta ta kama kafar Emily tana kuka sosai mai cike da nadama. "Ki yafe min, ki yi hakuri ban kyau ta ba na sani, ban sauke nauyin da Allah ya dora min ba na ki, kuma na zalince ki, hakkina yana nan akaina, ku ma yaya kuna da na ku hakki akan iyaye, ki yafe min Emily ki karbe ni, " n mi. Mo ti d aiy mi ru, . Mo ti e, mo ti w gan-an" Emily ta kama hannyen mahaifiyata ta rike ta mikar da ita zaune tana kuka. "Idan ban yafe miki ba me zan yi? Zan hukunta ki ne? Zan doke ki ne? Mai faruwa ta faru, komai ya afku rashin yafiyar ba zai dawo da rayuwar baya ba, ba kuma zai cire ni daga kangin da na shiga a baya ba, amman na dauki darasi mai girma kuma na jidadi da ban tafi na bar nawa yaran ba, ina alfahari da haka" Ta sake hannayenta ta mike tsaye ta fice daga dakin ta nufo downstairs. Aliyu Ummi da Fatima Nafeesa suna dinning suna karyawa Emily ta sauko da kuka ta nufi gurin da Fatima take ta dauketa, ta rumgume. "Momy are you okay?" Fatima ta tambaya ganin tana kuka kuma ya rumgume ta sosai. "Karki sake zabar kowa ki bar ni, na wahala na rana da dare na ratsa wuta, amman ban taba sha'awar tafiya na barku ba" Aliyu da tun da Emily ta sauko ya mike tsaye ya kalli Mama Baraka data sauko ita ma tana kuka ta yi zaton ko Emily zata gudu ne, Fatima ta labe jikin uwarta kamar ba ita ba, Emily ta juya ta haura sama tana dauke da yarta sai hawaye take. "Mama lafiya?" Aliyu ya tambaya. "Lafiya kalau ka fada mata komai da take son sani ne" "Okay, amman ki dan bata lokaci yanzu, ki tafi gida na miki alkawari da kaina zan kawo miki Emily idan ta huce" Mama Baraka ta amsa masa da kai sannan ta hade hannayenta zata musu godiya tana bude baki sai ta fashe da kuka ta zube a gurin. Ummi ta taso ta zo tana bata hakuri. TURHAN POV. Da gadon yaki masa dadi gashi bachi yaki ya dauke shi sai fito dakin ya sauko kasa ya zauna falo a nan ma ya ji ba shi da natsuwa saboda Fatima bata gidan yau, haka kuma be samu saka Emily a ido ba, ga bakinciki kallon matarsa da zama gida daya da ita da abokinsa yake babban makiyinsa a yanzu, ba zuciyarsa ba jikinsa ma ya gagara yin dadi komai ya yamutse masa. Ya bude kofar falon ya fita ya zauna a balcony abun da be taba ba, sam be san damuwa na hana bachi ba sai a yanzu da yake kokarin ganin ya gyara tsakaninsa da Emily. Ta ina zai fara.? Gaba daya Aliyu ya bi ya tare masa kofa babu ta inda zai leka balle ta hangeshi, duk wani yunkuri da zai yi da zarar ya tuna cewar Emily tana gidansu Aliyu karkashin kulawarsu sai yaji ya karaya, abu da ya sani idan yayi sanyi Aliyu zai kwace masa mata ne shi kuma ba zai jure hakan ba. Ya mike tsaye ya sauka balcony yana safa da marwa a gidan kar kace ba karfe 3 dare ba ne, ya dade a haka yana ta sake sake sannan ya juya ya koma ciki ya rufe kofar, dakinsa ya shiga yayi alwala ya fito daga bandakin ya nufi
Chapter 141 · 0% Book details