← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 177

Sashe 94

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 4 Sai da ta bar gurin sannan na fito na sallami mai achaba na koma ciki na rika ana dake ta ihu, gaba daya ya ki yarda da ni saboda be gane ni ba. Kansa na rike na saita shi ya fuskanci sai na koma kiransa da sunanyen da nake masa ina hadawa da Momy, a take ya tsagaita kukan da yake ya kalleni sai na yi masa dariyar dake tafe da hawaye na rungume shi ina jin kamar za a sake raba ni da shi ne. Kwana na uku a coci, a tsawon kwanakin nan bana sallah bana saka hijab duk wani abun da ya danganci musulunci bana yinsa, saboda na fada musu zan koma addinin Christianity, sai dai a can kasa zuciyata na ni na san ban shirya barin addinin musulunci ba, ba dan mutanen cikinsa sun yi min gata ba sai dan ina jin natsuwa da addinin a cikin zuciyata, domin addinin musulunci addinin mai tsari da tsabta da dokoki, ni kuma mace ce mai son zaman lafiya mai son natsuwa. Sun mutunta ni sosai a cocin domin gidan wani pastor aka kai ni, abinci sai na ture gurin kwanciya mai kyau, matarsa tana ta nanata min halayyen musulmai basa da kyau kuma daman su basa son kafirai, har take cewa na yi kuskure da na bar addinin da ace ban gane gaskiya na dawo ba da Yesu yayi fushi da ni kuma ya kona ni. Kusan duk wa'azinta jinsa kawai nake, amman a zuciya ina kyamar abun, ana gobe Lahadi wanda ta kama ranar coci a ranar za a min wanka da ruwa mai tsarki kuma a maida ni addinin kirista a ba ni bibles kamar yadda na sani yake a hukunce kuma matar ta jaddda min, sai na dauki London na goya ma sanya hijab dina cikin giyon na fito da sunan zagayawa harabar cocin, na nufi gate da yi ma mai gadin karya cewar zan fita naje na dawo kuma sun san da fita ta, domin an fada masa duk wanda ya zo nemana kar ya bar mutum ya shiga sai an sanar saboda ni da su muna tunanin Ammy zata dawo nemana. Salin salin na fice daga gidan, ba kuma dan na san inda zan je ba sai dan ban shirya komawa addinin ba, na hau achaba na tambaye shi dan Allah wace umguwa ce nesa sosai da cikin gari, unguwar da san yi tafiya sosai sannan a isa gurin, ya fada min sai na ce ya kai ni can, mun yi tafiya sosao kamin muka isa unguwar dake kama da sabuwar unguwa ma sauka na ba shi kudinsa na nisa cikin unguwar ina ta kallon yadda tsare tsarenta yake, har na hango wani gida dake da fanfo da kwararo a ciki, na dauki leda na tara ruwan na fara sha sannan na shayar da ana na yi alwala sallah na fara yi na rama duka wandada aka biyo ni har na ji na gaji, a lokacin kuma wata zuciyar take ta fadan min na koma dai domin wannan addinin be karbe ni ba, amman dayar data ci karfina ta hana ni komawa na zauna a gurin har dare, a nan yunwa ta fara tunkaro ni ga yarona be san babu ba. Kukansa ya saka mai gadin lekowa ya tambayi tafiya na fada masa yunwa yake ji sai ya shiga ya dauko ragowar abinci ya bani na bawa yaron da muka gama yace dan Allah mu kara gaba kar mai gidansa ya dawo ya same mu a nan zai masa fada. Na yi masa godiya na tashi na kara gaba, haka na yi ta rayuwa a unguwar daga wannan kwararo sai wannan wani gurin a hantare ni wani gurin a bani abinci ko sutura wani gurin kuma a ba ni hakuri, gaba daya na koma wata kazama saboda babu gurin da zan raba na yi wanka, bahaya ma sai na shiga daji, rayuwa ta yi tsanani gareni a lokacin, ga ciki ga yaron da ba lafiyayye ba, idan ciwonsa ya tashi sai dai na yi ta kuka domin ban san wani abu da zan yi ba bayan wannan, ni da shi muka rame muka lalace, nakan shiga gida gida neman aiki ko wanki, idan na samu mai son wanki na yi ta murna na wanke a biyani na ciyar da kaina da ana, na samu wani tsohon shagon kwano na laba ciki nake kwana ciki nake wuni idan ina cikin unguwar. Tun mutane ana jin tsorona a unguwar har aka fara sabo da ni wasu ma idan sun raga abinci da kansu suke kawo min saboda suna min kallon mahaukaciya, wani lokacin ba ni sadakar kudi ko abawa ana da haka nake ta fadi tashi har cikina ya tsufa, wani sa'in sai na yi tafiya mai nisa zuwa wata unguwa nake samun abun da zan ci, kuma ban sake bawa kowa labarina ba, idan naje gida sai dai na yi bara ko kuma na tambaya idan suna bukatar a musu wanki ko wani aiki. Wasu suka kam tambaye ni waye uban yarona ko kuma cikin da nake dauke da shi sai nace musu ban sani ba ni ma, hakan ya saka suka kara daukata mahaukaciya suna tunanin kamar fyade aka min na samu cikin ko kuma wani ya yaudare ni. Akwai masu fadar wai ko dai kishiya ta yi min asiri saboda ina kyau ta raba ni da mijina? Su tambaya daga ina nake sai na ce Lagos, idan aka ce Lagos a ina? Sai na ce ban sani ba, to gurin wa zan ce daman? Har lokacin ina jin da kamar akwai sauran kurciya a tare da ni, wata kila kuma shiga mawuyacin hali ne yasa ban taba kula da watan cikina nawa ba, ban taba kirgawa na gane ba, ciki dai yana ta girma kuma yana motsi, idan na ji motsin cikin sai na ji zuciyata ta yi fari tas kamar ba ni da damuwa, ni dai burina na haihu lafiya na samu karin wasu iyalin... Ana haka wata rana nakuda ta fara taso min tana kwantawa na kwashe kusan kwana biyu sai ta motsa min sai ta koma, idan ta laba min sai na cigaba da harkokina, wata rana na fita neman abun da zan ci ban karasa inda zan je ba aka sako ruwan sama na kuda ta taso min mai karfi kamar zan fita hayyacina gashi kuma na yi nisa da gida ba zan iya komawa ba, ana kuma ya firgice saboda tsoron ruwan da iska sai ihu yake min ni ma kuma ihun nake a gefen hanya babu wanda ya kula ni sai kai Aliyu, shi ne farkon haduwata da kai, na zan iya manta wannan alherin ba, na gode na gode Aliyu, a lokacin ne na rike hannunka har agogon ya cire ya dawo hannu sai na matse shi ina ihu na yi tunanin mutuwa zan yi ma gaba daya, ka taimake ni ka dauke ni ka kai ni Asibiti, duk wani taimako daya kamata likitocin nan sun ba ni na wahala sosai kamin na samu na haihu da kaina, ada har ina tunanin ko dai sai an fasa ni za a iya cire abun da ke cikina saboda na kasa nishi. Da na haihu sai suka bukac a kawo kayan jaririya ba ni da su, zanen da aka hadeta a ciki ma tsohon zanen wata mata ta bada a gurin aka lulkube Fatima, suka ce ina audugar da zan saka ina kaza ina kaza, na ce duk ba ni da, sai suka tambaya wanda ya kawo ni waye shi? Nace ban san shi ba taimakona yayi, a nan wata nurse ta fita ta shigo min da pad ta pant ta kuma ba ni zane na daura sannan suka canja min daki suka kawo ni wani dakin na dabam suna tambayar ina yan'uwana ya kamata na ci abinci na ce musu ba ni da kowa, daya daga cikin wadanda suka karbi haihuwa ta ta kawo min agogonka ta ce ga wannan kin saki a kasa dazun na karba na rike ga. Daker na iya awa hudu a asibitin na kamin na saci kafa na gudu da ana da kuma jaririya dana haifa, zanena mai jini da uwar da ke fadowa bayan haihuwa a asibitin na bar musu na gudu. Ban nisa sosai da unguwar da asibitin take ba jiri ya debe ni na fadi ban sake sanin inda kaina yake ba. Sai da na farko naga ana min fifita ga jaririya a kusa da ni ga kuma London yana ta kuka, mutane nata min sannu aka ba ni abinci na ci sannan aka dauke ni zuwa gidan wata mata dake kusa ana tambayar a ina nake daga ina na fito na fada musu a gidan na kwana sai washe gari bayan na karya matar ta siya min wani pad ta bani tsohon wandonta na saka bayan ta dora min ruwan zafi na yi wanka, ta bani wani tufafin na saka da hijab, makota kuma suka kawo min tsofin kayan jarirai na sakawa Fatima, ta kawo min abinci na ci na sha kunu sannan mai gidanta da wasu mutum biyu yan unguwar da kuma ita matar kanta, suka dora ni a napep muka tafi unguwar da nake rayuwa na nuna musu inda nake kwana sai suka fara tambayar wadanda suka san ni a unguwar, kowa sai yace da rana tsaka ya gan ni a gurin kuma ba ni da cikakiyar lafiya, cikin ma suna zargin yi min aka yi ta karfi, wasu kuma su nanata wai asiri aka min. Ni dai jinsu kawai nake idan aka tambaya daga ina nake sai na ce Lagos wane guri a Lagos nace ban sani ba, sai suka yanke shawarar za a kai ni police station ayi report, ina jin haka nace ba zan je ba da suka matsa na saka musu kuka a dole suka koma can gefe suka yi maganarsu sai aka dawo aka fada min wai zan bi matar zuwa gidanta na koma can da zama a nan ma na tirje domin na san akwai abun da suka shirya, ni kuma ina tsoron a yadani Cocin da na gudu su gani ko kuma Ammy. Na dake akan nan gurin zan
Chapter 94 · 0% Book details