← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 177

Sashe 61

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Emily tace kin sake kiranta kin ci mutuncin kin ka e....!" Tun da ya fara fadan bata komai sai kuka, Mama Barakat data sauko tana kallonsu saboda daga muryar da Aliyu yake ta matsa ta rike Kameela. "Lafiya Aliyu?" "Karamin abu ne da ya faru da be ma kamata ka ji ba, amman yarinyar ta bi ta lalata komai" "Meyasa ba zaka fada mata saboda wata karuwa kake ci min mutunci ba, wata banza yau kake min abun da baka taba yi ba, saboda kana ganin ita fara ce mai kyau baturiya saboda kana ganin kamar ta fini kyaun? Abun kunya ma matar abokinka, yarinyar da ba a san su waye iyayenta ba, yarinyar da tsintarta akayi a Lagos, yarinyar da ba ma musulma bace, ai ko aure zaka yi ko soyayya zaka yi ka yi da mai ma'ana mana" Aliyu ya dube ya sake dubanta ya kuma ya dubeta sannan ya dauke kai ya fice daga falon. Da wani irin kufura da fushi ya isa motarsa, da ace halinsa ne saki ko dukan mata a yau ba zai ragawa Kameela da ko daya ba, domin kalamanta na yanzu sun fi abun da ta aikata zafi, yana barin gidan ya daga waya ya kira Umminsa tana dagawa be tsaya gaisuwa ba ya ce. "Ummi karki aika bikon Kameela a yanzu" "Me ya faru?" "Yar hatsaniya muka samu, kuma na san Hajiya Asma'u zata iya yin wani abun da zai bata miki rai ko ni, ni kuwa a yadda nake jin kaina a yanzu idan ta kuskura ta furta wata kalma marar dadi a gareki ko Daddy, na rantse da Allah sai na nuna mata ta fi kowa rashin sa'ar suruki a duk fadin garin Kaduna...!" "Toh Allah ya kyauta, shiyasa ake son idan mutum zai yi aure ya auro yar gidan mutumci, ba tarbiyar yarinyar kadai ba ta iyayenta ma ya kamata a duba, Hajiya Asma'u fa hankalinta ba zai kwanta ba sai taga Kameela bata gidanka, saboda ta dauke mu makiyansu. Ko da yake ma komai ya faru ai kai ka janyo, babu yadda ba mu yi ba ka nace sai ita, abun da duk iyaye suka ce a bari barin shi yafi alheri ko da babu dadi, idan riba ce yanzu ai ka fara ci" Tana fadar hakan ta kashe wayar. Aliyu ya cigaba da tukin motar sai huci yake har ya isa gidansa. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [5/20, 10:17 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 61 · 0% Book details