← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 177

Sashe 29

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 1 Masu tambaya daga farko zaku iya duba channel dina https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 Ko kuma wattpad @KhadeejaCandy Masu tambayar free ne ko na kudi, toh Free ne, yan bati sun hada kai da Iya sun min kiranye ya kamani tare da hadin kan Ummu Faisak yayar Wasim Asha karatu Lafiya ***. ***. *** VITO POV. Falon ya shiga ya zauna, can kasan zuciyarsa ya ji babu dadi na dukan da yayi ma Emily, ya saba samun kansa a irin wannan yanayin a duk lokacin da ya duke ta, sai dai kuma dukanta a gaban ko ma waye abu ne da ba zai iya hana kansa ba, ba zai iya rike hannunsa daga taba jikinta da sunan duka a duk lokacin da laifi ya fito ta tsagenta ba. Kamar yadda ba zai iya fin karfin zuciyarsa a duk lokacin da wani yayi mata kallon banza ko na soyayya ba, yana sonta ya sani, yana tsananin kishinta irin kishin da shi kansa yana tsoron kar yayi masa illa wata rana. Ban san ko kana bukatar ruwa ba Chidimma ta miko masa cup da gorar ruwa a tray cike da ladabi da kuma gudun bata masa rai. Ya kalleta kawai ya kalli gurin da zata aje ruwan, sai ta risina ta aje a kasa ta daga gorar ruwan ta bude ta zuba masa a cups sannan ta dora ruwan a kan side table. Ruwan ya fi da kallo yana mamakin yadda ya kasa yi ma Aliyu komai a dazun har ya tafi, me yasa ma ya daki Emily bayan kuma Aliyun ya kamata ace ta hukunta domin shi ya nemi addireshinta ya biyo sawunta har gida? Ya kawo karnukansa da nufin idan Aliyu ya shigo gidan ya rufe gate din ya sakar masa su, amman duk be samu nasarar yin hakan ba. A zahirin gaskiya Vito wani kalar mutum ne sa kallonsa kawai zaka yi ka firgita, saboda rashin annurin dake fuskarsa da kuma shigar da yake ta tufafi, amman sam be ga alamar hakan a tattare da Aliyu ba, toh miyasa ma ya biyo ta har gida? Me yake nema a gurinta? Ya kai hannu ya dauki ruwan da Chidimma ta zuba masa ya kai baki yana sha sai wani sanyi ya sauka a zuciyarsa wanda ya kara taimaka masa gurin hararo dalilin Aliyu na bibiyar macen da ba ma addininsu daya ba. 'Tana da kyaun da kowane kalar namiji zai iya cewa yana sonta ko son mu' alama da ita` Zuciyarsa ta bashi amsar da yake bukata, mikewa yayi tsaye ya nufi kitchen din da Chidimma take, tana ganinsa ta juyo da sauri. Kana bukatar wani abu ne ranka ya dade? Me kika shiryawa London na karyawa? Gashi nan Ta dauko big basket ta risina kasa ta aje masa, zai kai hannu ya dauka sai ta riga shi. Bari na kai maka mota ranka ya dade Be ce mata komai ba, ya juya ta bi bayansa har gurin motarsa sai da ta saka masa mota sannan ya yi mata key ya fice daga gidan. Sai a lokacin Chidimma ta nufo Emily dake kwance a gurin rumgume da Fatima ta tsaya kanta. Bana son na batawa daya daga cikinku rai ne, bana son daukar bangaren Sir Vito na bar naki, abu kadan zai iya sakawa ya koreni ko ya hukanta ni, shiyasa bana iya tarewa idan yana dukanki, ki yi hakuri Uffan Emily bata ce mata ba, ita ma kuma bata jira cewarta ba ta juya ta koma ciki ta cigaba da aikin da take. Yana faka motarsa harabar asibitin wayarsa ta yi ringing, ya amsa kiran har lokacin ransa babu dadi saboda dukan da yayi ma Emily, mahaifiyarsa ce take sanar masa jirginsu zai taso yanzu daga Murtala Muhammed International Airport (MMIA) dake Lagos zuwa Port Harcourt International Airport. Daman ta sanar masa da zuwanta tun kwanan baya. Safe journey" Ya fada as Answer sannan ya cire wayar daga kunnensa ya bude dayan side din ya dauko basket din da Chidimma ta saka masa ya nufi cikin Asibitin. Ko da ya shiga ya samu Nurse nata lallaba London ya fito daga kasan gadon majiyanta da ya boya amman yaki sai ihu yake mata. Heyyy my boy Vito ya fada cikin muryarsa ta manyan mazaje, London na jin muryarsa sai ya leko suna yi arba ya fito da sauri yaje gurinsa ya rumgume shi. Murmushi ko nuna farinciki ba al'adarsa bace balle kuma a yau da yake cikin damuwa, kan London kawai ya iya shafawa ya daga shi zuwa kan gadon Asibitin suka zauna. Tun dazun yake labe a gurin baya yarda da kowa, idan ka matsa kusa da shi sai yayi maka ihu Ta fada tana kallon London din da murmushi a fuskarta, Vito be ce mata komai ba, ya kai hannu ya dauko abinci ya bude ya fara ba shi da kansa, tana ganin haka sai ta fita ta bar musu dakin. Sai da London ya ci abinci ya koshi sannan Vito ya fara masa maganar Emily. Meyasa ka yi ma Momy Ihu jiya? Ina fushi da ita Na fada maka Momy tana sonka ba zata aikata abun da zai bata maka rai ba, duk laifinta akan kuskure ne, ka yafe mata ka ji? Ya daga kai, sai ya shafa kan yaron... Ina son mahaifiyarka, duk kuwa da kasancewar ta haife ku, na kula da ku na nuna mata soyayya da gata, amman ta kasa ganin hakan Yayi shiru yana kallon London. Wata kila kuma ta gani, kawai dai bata shirya karbata ba ne Ya ja numfashin da ya gagara saukewa. Uhmmm zan mata uzuri har zuwa lokacin da ta dibarwa kanta, sai dai ina da tabbacin abu daya, idan ban samu mahaifiyarku ba, wani ba zai same ta ba, idan ban mallake ta wani ba zai ci galaba a kaina ba London yayi murmushi domin be fahimci yaren ba. A hankali idonsa ya kai a kan card da Emily ta jefar a dakin. Mikewa yayi tsaye ya nufi card din ya dauka Dr A-B ne rubuce a jikin katin da kuma address din gurin aikinsa sai Email da number wayarsa. A take ya fara jin zuciyarsa ya tafasa, jimke katin yayi ya juyo ya kalli London. Chi chi zata zo ta kula da Kai bari na je na dawo ka ji? London ya daga masa kai alamar amsuwa, be bar dakin ba sai da ya kira Chidimma a waya ya fada mata ta bar duk abun da take ta zo yanzu asibitin gurin London, bayan ya shafa kansa ya sumbance ya fice. Kamin ya isa gida ya kira daya daga cikin yaransa ya fada masa ya tafi gidan ya dauke dog's da aka kai, yanayin yadda ya faka motar a harabar ya fito kadai ya isa ya sanar da bacin ransa balle kuma yadda ya turo kofar falon ya shigo, sai da Fatima dake zaune tana zane ta firgita. Yana kallonta ya dauke kai ya nufi upstairs. Dukanta zaka sake yi? Ya juyo ya kalli makiyiyarsa Fatima, domin ya fi tsanar ta fiye da kowa a gidan, sai dai duk da haka be taba unkurin kai hannu ya doketa ba, no matter what ta yi masa sai dai ya mata fada ko ya wani hukuncin na dabam amman ban da duka. Momi zata yi kudi, tana aiki zata samu kudi mai yawa zata gina gida zata maida mu can mu rayu a can ba tare da kai ba, ba zaka sake ganinmu ba balle ka dake ta, i hate you Ta fada cike da fitsara da tsageranci irin yadda ta saba yi masa, jimmm yayi yana kallonta kamar mai nazari ba tare da ya ce mata komai ba, kamin ya juya ya haura saura zuwa dakin da Emily take... EMILY POV. Meyasa kake son saka kanka a hatsari? Baka san wacece ni ba, kuma baka san da wa nake tare ba, kuma ya kamata kasan ni ba musulma bace, babu abun da Zai hada ni da kai, domin mutanen da na tsana irin musulmai, karka sake bibiyata karka sake shiga rayuwata, idan ba haka ba zaka jefa kanka a bala'i Ya mayar mata da amsa a take. I'm sorry for what happened earlier, bana nufin jefa ki a matsala, akwai wani tsauni ne da na hau ba kuma zan iya sauka ba har sai da gamsantsun amsasoshinki, shin zan iya sanin wani abu akanki? Wata kila hakan zai taimaka ya gina wata katangar da zata katange ni daga fadawa mai nemanki gaskiyar a inda kike Ni uwa ce da bata da aure mai zama a karkashin inuwar wani mai karfin kudi da iko, uwa ce da ta haifi yaranta ta raine su ba tare da taimakon kowa ba, ni din na tashi a gidan marayun ne ban san uwa ko ubana ba, balle ayi zancen yan'uwa, bana da kawaye bana da kowa sai Vito da yarana, ni din wata ce da wani musulmi ya yaudara, mummunar kaddara ta yi min dabaibai hada ni da mutanen da bana kirki ba, a yanzu kuma ni christen ce mai alfahari da jindadin addininta, mai kokarin gina kanta da rayuwar yaranta, bayan wannan sai me kake son ka sani? Ina son na san a lokacin da kika wanzu tsakanin rayuwa da mutuwa ne, ina son na san komai akanki, ta ina lamarin ya fara? Taya kika kawo har yanzu? Su waye suka munana rayuwarki, miye dalilin komawarki addinin Christianity? Su waye suka saka kika tsani musulmi da addinin musulunci? Miyasa baki son Fatima ta san tana da mahaifi? Wacece ke Emily? Na damu na na sani, kuma na damu da ke Taja numfashi tana karanta sakon hawaye na cika idonta, kai ta daga sama ta lumshe ido ta bude sannan ta maida idonta a kan wayar, tana kokarin rubuta masa amsa ta WhatsApp din Vito ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta yi saurin saka wayar a lock ta dora ta a kan madubi. Miye hadinki da likitan da zo duba London da har zai baki card dinsa? Idan wani abun da ya shafi rashin lafiyarsa ne ai da ni zai yi magana Ta juyo idonta a kumbura ta kalleshi hawaye na sauko mata. Waya kalleki? Waya miki magana? Gurin wa kika je? Da wa kika
Chapter 29 · 0% Book details