Sashe 54
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... FOLLOW ME ON FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2 "Har yanzu zuciyarki tana sha'awar musulunci ko Emily? Har yanzu baki dauki darasi daga azabar da muslmai suka koya miki ba? Da biyu kike zaune a cikin addinin kiristiyaniti ko?" Ta dago ta kalleta inda take kyautata zaton fuskarsa take domin bata iya gani da kyau. "A yanzu kake son mu yi wannan maganar?" "idan har babu wata manufa a zuciyarki a wane dalili zaki ce a kai shi makabartar musulmai? Ina ruwanki da kasancewarsa a baya musulmi? Ai kin canja masa addini ko? Ubansa da yake a cikin addinin be damu ba sai ke da kika haura kika leka ciki?" Ta rasa abun cewa, domin ta san ya fita gaskiya, Ubansa be damu ya san halin da take ciki ba balle abun da ta haifa gashi har London ya bar duniya be taba ganin ubansa ba. "Ba ni da alaka da musulmi ta kusa ko ta nesa, ba zan iya tafiya makabarta na tambayi wani yadda za a binne London ba, ina son kin Emily ina son yaranki, amman hakan ba zai saka na kusanci addinin da ba ni da makiyi irinsa ba" Ya mike tsaye ya dauki wayarta ya saka aljibu, ba tare da ta gani ba domin idonta a rufe suke. "Ka bar min dana bana son ka masa biki" Be juyo ba kuma be ce mata komai ba ya fice daga dakin, ko da ya sauko ya samu Chidimma zaune a falon har lokacin tana kuka sosai ita ma idonta ya kumbura domin mutuwar London ta zo mata a bazata. Wayar Emily ya ciro ya mika mata. "Ki aje wannan a gurinki karki bata har sai idan na bukata" "Okay Sir" Ta fada cikin kuka sannan ta karbi wayar ta tashi ta fice daga falon zuwa bangaren da dakinta yake ta boye wayar sannan ta dawo ta shiga dakin da Fatima take. Cikin karfin hali Emily ta tashi tana lalabe har ta isa bandaki ta kunna fanfo ta jika kanta da jikinta ta dauki karamin tawul ta zuba ruwan zafi ta gasa idonta, sannan tana iya daga su ta kalli abu but still tana jin ciwo. Ta fito bandakin ta nufi wardrobe dinta ta sauko short gown ta saka ta nufi gurin da makullin motar yake ta ga baya gurin, sai ta tuna yana cikin aljihun gown din data cire motar kuma tana can asibiti, gashi dare ne yanzu idan ta fita ba lallai ta samu abun hawa in time ba, haka kuma ba lallai ne ta tafi inda take nufin tafiya ta samu mutane a gurin ba. A nan ta fara neman wayarta ita ta rasa ina ta aje wayar, ta dafe kanta ta busar da numfashi sannan ta bude gurin da Vito yake aje mata kudi ta dauka ta fito daga dakin ta sauka kasa. Har ta nufi kofar fita sai kuma ta dawo ta sake haurawa sama zuwa dakin Fatima ta tura kofar a hankali ta leka sai ta hango Fatima kwance a jikin Chidimma, jan kofar ta yi ta rufe ta sauko ta fice daga gidan gaba daya. Ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu abun hawa, ta kwatanta masa inda zai kaita wato gidan Tasmia, domin bata manta inda suka hadu ba har ta yi mata tayin shiga gidanta bata yarda ta shiga ba a wacan karon, da suka isa ta sauka ta bashi kudin da bata san nawa ba ne ta doshi gurin da kofar gidan mai kama da BQ yake ta kwankwasa, babu jimawa aka bude mata bayan Tasmia ta tambayi waye tace mata ita ce. Da maimaki take kallonta. "Lafiya? Me ya same ki?" "Zan iya shigowa?" Emily ta furta muryarta na rawa. Tasmia ta matsa jikin kofar ta bata hanya kana ra leka waje ta ga ko tana tare da wani ne. Ta shiga ta zauna sai wani sabon kuka ya zo mata. "Lafiya?" Tasmia ta tambaya tana dafata cikin tashin hankali. "I lost my Son" "Subhanallahi yaushe? Me ya faru?" Cikin kuka Emily ta fada mata yadda London ya mutu. "Na fi son yaron nan fiye da komai na duniya, saboda lalurar da take tare da shi, ina matukar tausayinsa" Tasmia ta kwantar da Emily jikinta tana hawaye. "Ki yi hakuri Emily amman na tausaya miki" Sai da ta yi kukanta ta koshi sannan ta fada mata dalilinta na zuwa gidan a cikin daren. "Gaskiya ban san wani makabarta ta musulmai ba, ban san inda za a iya binne shi ba, kin ga ni ma bakuwa ce a garin, ban da gidan yar'uwa da kuma wata kawata ban san kowa a nan ba sai ke, ita kuma kawar tawa bata nan ma kuma ba zata yarda ba, yar'uwa ta ma bana saka ran haka, saboda ba jini daya muke ba, cousin dita ce, kuma kin ga a yanayinki nan ba kowa zai yarda danki musulmi ba ne" "Ni ina jin kamar be dace a rufe shi a makabarta da ba ta musulmi ba, domin na san ni kaina ba a daidai nake ba" "Toh yanzu ya zamu yi?" Emily ta share hawayenta. "Akwai wanda nake saka ran zai iya taimaka min amman yanzu ban san inda zan same shi ba, saboda dare ne ya bar gurin aikinsa kuma ban san gidansa ba" "Wanene?" "Mutumen da ya kawo ni dazun ogana ne a gurin aiki, kuma mun taba haduwa da shi tun da dadewa, yana da kirki da zuciya mai kyau wata kila zai iya taimaka min" "Aliyu..?" Emily ta kalleta "kin san shi?" "Ba wanda na tambayi me yayi miki ya min bakar magana ba?" "Eh" "Mijin kawata ne, na san gidansa amman da gaske ba wani abun yayi miki ba?" "Be min komai ba, tuna rayuwarta ta baya ne da kuma mutuwar da London zai yi, ya taba ni yasa na zama yadda kika gan ni, kina da number wayarsa?" "Aa ke baki da ita?" "Ban san inda wayata taka ba, ina zan same shi yanzu" "Muje na kai ki gidansa, daman kuma matarsa bata nan" Sai da ta mike tsaye sai kuma ta fara tunanin inda za su samu abun hawa. "Amman anya zamu samu abun hawa yanzu?" "Ina motarki?" "Ba motata bace ta yar'uwa tace nake karbowa ina zuba mai sai na yi yawo da ita, amman muje wata kila ba zamu rasa samun abun hawa ba" A tare suka fito Tasmia na sanye da abaya da mayafi Emily kuma da tufafin jiki, sun yi tafiya mai nisa sannan suka samu texi suka shiga, Tasmia ce ta yi jagora har suka isa kofar gidan. Emily zata bawa mai motar kudi Tasmia ta hana ta biya kudin motar sannan suka fara kwankwasa gate din gida. Mai gadin ya bude yana musu kallon rashin sani. "Mai gidan yana ciki?" Tasmia ta tambaya da turanci be amsa mata ba sai ya tambayi lafiya. "Ka fada masa Emily tana nan waje tana son magana da shi" Ya juya ya koma ciki, babu jimawa ya dawo ya bude musu gate din suka shiga, Tamia ta wuce gaba domin ita ta taba zuwa gidan sai da suka isa gurin kofar shiga sannan ta koma baya ta bar Emily a gaba, Emily ta tura kofar falon ta shiga Aliyu na tsaye sanye da jallabiya yana raga volume din wa'azin da African Tv suka saka, sannan ya juyo ya kalli kofar yana amsa sallamar da Tasmia ta yi domin Emily bata yi sallama ba ta shiga. Be gama mamakin zuwansu gidan cikin dare nan ba, yayi arba da Fuskar Emily da idonta da suka kumbura. A take zuciyarsa ta raya masa mutumen nan ne yayi mata duka wata kila saboda ya kaita gida. "Me ya same ki? Ko dukanki yayi?" "Danta ne ya mutu" Tasmia ta amsa masa sai yayi kalmar shahada ya zauna ya dafe kansa cike da tausayinta, yaron data gama bashi labarin wahalar da ta sha akansa shi ne kuma ya mutu a yanzu. "Mun zo nan ne saboda tana son ayi masa jina'iza irin ta musulunci, ni ma kuma bakuwa ce a garin nan ban san kowa ba amman ita tace...." Tasmia ta fada masa abun da yake tafe da su domin Emily bata komai sai hawaye. Aliyu ya sauke ajiyar zuciya. "Yaron yana ina yanzu?" Sai a nan Emily ta iya amsawa muryarta na rawa. "Yana can dakinsa yana gida" Aliyu ya dubeta duban da ya dauke shi tsawon dakika 120 yana kallonta. "Emily" Ta dago ta kalleshi ba tareda ta amsa ba, a zatonta zai ce mata ba zai samu damar aiwatar da kudirinta ba ne. "Mu a musulunci akwai shika shikan imani da akan gindawa kowane musulmi, ina kyautata zaton lokacin da kika musulunta an fada miki su? A ciki akwai imani da kaddara mai kyau da marar kyau, na san kin tsani musulmi kin tsani musulunci amman ni ina ji a jikina wannan imanin da kika yi da Allah har yanzu yana nan cikin zuciyarki, kuma ban kara tabbatar da hakan ba sai a yanzu, dan haka ki yi hakuri da wannan rashin Emily, kuma na jidadin shawarar da kika yanke na yi masa sutura irin ta musulunci, shi kanshi da ace zai dawo yanzu zai miki godiya na abun da kika yi masa, kuma ina tabbatar miki zan yi masa duk wani abu da ake yi ma musulmi In Shaa Allahu" Ta amsa masa da kai tana matse jikinta wani yanayi take ji marar dadi. Aliyu ya shiga dakinsa sai gashi ya sauko sanye da kananan kaya. "Zan tafi da mai gadi na mu dauko gawarsa, zan masa wanka a yau da duk abun da ya dace In Shaa Allahu, da safe sai ayi masa sallah a kai shi makwancinsa" Ta mike tsaye. "Idan ba mu je tare ba, ban san iya abun da zai faru tsakaninka da Vito ba idan ka tarar da shi a gidan ba" "Karki damu ina addu'a aljani ma be isa ya cutar sa ni ba sai da izinin Allah balle Vito" "Baka sanshi ba ne, baka san irin hadarin da yake da shi ba" Ta fada tana kuka. "Idan na je na tarar yana gidan ba zan dauko ba zan dawo