Sashe 118
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 5 Nafisa ta shiga ta sanar da Ummi hukuncin da Aliyu ya yanke akan Khaleefa, Ummi ta dan yi jimmin sannan ta ce. "Shikenan zan yi magana da shi" Ummi ta tashi da kanta ta dauko kudi mai kauri ta sauko kasa sai kyalli take tana zuba kamshi saboda kwalliyar da ta yi ma mijinta kai kace ba ita ya haifi Aliyu da Yayansa Yusuf ba saboda yadda take kula da jiki, kuma bata taba yarda cewar ta tsufa da yi ma mijinta kwalliya ba. Kamin ta karasa fita falon aka turo kofar falon aka shigo daman ta ji tsayarwa mota. Yusuf ne tare da matarsa suka shigo, Ummi ta saki baki "Ah ah ikon Allah yanke tafiyar kuka yi kuka dawo??" Ummi ta rumgume surukarta tana murmushi, Khadija ta yi dariya "Shi yace kar a fada miki, wai zaki ce ba sai mum dawo ba" Ummi ta dago tana kallonsa da harara. "Daman baka yi nufin hutun ba ko?" Yayi dariya. "Ummi ke da kike mahaifiyarsa kika gagara jurewa ki zauna Abuja sai da kika zo nan balle ni da nake yayansa na san zafinsa fa, ita kuma wannan kin santa da lakuwa duk inda ta ji dake a guri sai ta zo" Ya karasa yana nuna matarsa. "Eh mana ai ita ce yata, kai miye hadina da kai" Yayi murmushi ya daga kafadunsa ya nufi cikin falon. "Toh ga ka ga guri nan, barka da zuwa" Ummi ta fada tana murmushi ta kalli Yusuf kadan ta dauke kai domin bata wasa da shi sosai, ba kamar Aliyu ba da ta dauka tamkar kanenta, Yusuf ta aje shi a muhallin an fari ne. Shi ma kuma ya dauke ta uwa ya dauki mahaifinsa aboki shi kansa ya fi sakewa da mahaifinsa kusan duk wani abu da ya shafi kasuwancin mahaifinsa shi yake tafiyar da shi, sukan tattauna abubuwa da dama ba tare da Aliyu ko ita kanta Ummi ta sani ba. "Zauna Khadija bari na sallami wani na dawo" Ummi ta nufi kofa ta fita, sai da ta fita harabar gidan daya daga cikin yaran gidan ya zo da sauri yana tambayar wani abun za'ayi mata. "a Khaleepa nake nema direban da muka zo da shi ina yake?" "Oh Khaleefa" Yaron ya kwala masa kira, sai ga Khaleefa ya fito daga BQ da saurinsa ya karaso gurin Ummi ya gaisheta. Ta amsa sannan ta ce. "Ai kauyenku a Kaduna nan ne kace ko?" "Eh Hajiya" Ta mika masa kudin hannunta. "Ga wannan, ka yi na mota ka tafi gida ka duba su kuma ka tsaya a can ka kwana biyu, har sai ka ji daga gareni" Gabansa ya fadi ya kalli kudin jiki a sanyaye. "Hajiya wani laifin na yi?" "Aa ba laifi kai yi ba, ba korarka aka yi ba, za'aci gaba da biyanka albashi nan da kwana biyu kuma zaka dawo aiki" "Hajiya saboda na yi magana da Emily ne? Wallahi baki san abun da yake tsakanina da ita ba wata kila da ba ki fusata har haka ba" "Ba saboda ka yi magana da ita ba ne" "Ku kuke da komai na ku, duk hukuncin da kuka yanke yayi daidai, amman ina rokon alfarma daya dan Allah a ba ni damar magana da Emily akwai abubuwan da nake son na tambaye da yawa, kuma akwai wadanda nake son fada mata" "Ita ce bata bukatar ganinka shiyasa aka bata hutu" Khaleefa ya zube kasa ya hada hannu biyu. "Hajiya ki dubi girman Allah ki taimaka ki roki Emily ta saurareni, kusan rabin rayuwar nan na karar da ita gurin neman Emily ne, dan Allah Hajiya ki taimaka min na yi magana da ita, akwai zuri'a a tsakaninmu ina son na tambaye ta, kuma Wallahi a musulma na santa ya aka yi ta zama haka? Dan Allah Hajiya ki ba ni dama" "Damar ba daga ni ba ne, daga ita ne bata bukatar magana da kai a yanxu, ka tafi gida idan ta bukaci hakan zan maka waya, yanzu dai ka tafi dan Allah kar na fito na same ka a nan" Ummi ta duka ta aje masa kudin ta juya yana ta mata magiya kamar zai zauce har da kwalla a ido. Ko da Ummi ta shiga falon ta samu Yusuf ya haura stairs, sai Khadija a falon da Nafisa suna hira. "Ke baki kawo mata komai ba? Ke kuma kamar bakuwa ba zaki shiga ki dauko ruwa ki zuba abincin ba" "Ni na ci abinci, Abban Maama ne dai be ci komai ba" Ummi ta zauna tana tambayar jikokinta. "Ni na manta ina kuka bar yaran?" "Suna can gida, tare da nanny" "Wai ku wannan rayuwa da kuka daukarwa kanku anya zata yi? Ku gaba daya rayuwar turawa? Komai dai nanny? Haihuwar ma tun da aka haifi biyun nan shiru ba kari? Kuma kuna kallon yadda muke a gidan nan daga Aliyu sai mijinki sai Ramla da bata yi aure ba, Aliyu kuma shi Allah be ba shi haihuwar ba, ku kuma daga yin yan biyu sai ku tsaya haka? Muna son zuri'a gaskiya" Khadija ta yi murmushi. "Allah ne be kawo ba Ummi" "Ku yaran zamani masu dabi'ar turawa ta ina za a gane ko daga Allah ne ko kuma daga ku ne, mu dai na mu daga Allah ne ai" Ummi ta mike tsaye tana murmushi domin ta ji tsayarwa motar mijinta, da ganganta ta fada ma Khadija haka domin tana son ta ga tarin jikoki saboda Allah be fata yara da yawa ba, ba kuma zata iya zauna da Yusuf ta yi wannan maganar ba amman zata iya da matarsa. A ranar gidan ya cika da jama'a saboda dawowar Daddy masu zuwa gaishe shi da suka zaba suka zo, wasu ba su san ma abun da yake faruwa ba sai da suka zo wasu kuma yan'uwa ne da abokan arziki suka zo masa jaje, da yammancin ranar Yusuf ya tafi asibitin duba dan'uwansa tare da matarsa da wasu daga cikin yan'uwa, Daddy kam sai dare ya samu zuwa tare da Ummi saboda mutane ba su bar shi ba sai bayan sallah isha'i. Aliyu ya gaisa da mutane ciki har da abokai wasu ma ba a bar su sun shigo ba, yayi farinciki sosai da ganin dan'uwansa, Khadija sai zolayarsa take tana tambayar ina Kameela domin bata san wainar da ake toyawa ba, Aliyu dai daya gaji da tambayarta a fada mata sun rabu. Subhanallahi daga haka bata sake cewa komai ba, daga asibitin suka wuce gidansu dake Kaduna daman suna hutun Anniversary ne abun da ya faru da Aliyu ne ya saka suka yi dawowar gaggawa. Da dare Ummi suka zo duba shi tare da Daddy Ummi ta zo masa da wani abincin da ta girka masa, sun sha hira da daddynsa sosai na abun da ya same shi da wanda yake zargi da kuma abun da yake hararowa nan gaba, har statement din da police suka dauka sai da ya fadawa Daddynsa kuma a kaurara lamarin saboda yana son a dauki babban mataki. Daddy ya shaida masa already hukuma sun fara aikinsu, a nan ya kara warwarewa Ummi zare da bawa a game da Emily sannan ya kara fayyace musu abun da ya faru tsakaninsa da Kameela. Aliyu yana son ya tambaya ya Emily take yana gudun Ummi ta masa fahimta ba daidai ba, alhalin shi kuma ya damu ne kawai ya san halin da take ciki. "Idan ba mataki aka dauka ba ita kanta ba zata samu salama ba" "Ai dole ne wannan, indai har aka tabbatar shi ne to ya kai karshe, ni da har na fi zargin Kameela saboda yarinyar bata da hankali, indai har zata iya saka maka guba to zata iya komai" "Abu ne mai wahala Kameela ta yi haka, kuma bana zargin Turhan even though yana cikin bacin rai, amman bana tunanin zai saka ayi min haka, domin na fito gidan kenan ma ba a jima ba, lokacin be isa ace ya je ya samu wasu su yi min wannan dukan ba, na fi zargin Vito ne yake bibita saboda na zo da yarta kuma gashi ta biyo bayana and ita kanta ya saba dukanta balle kuma wani" "Bincike dai zai tabbatar da komai In Shaa Allahu" Ummi ta fada sai Daddy ya ce. "Yanzu ita yarinyar tana Lafiya?" Aliyu ya kalli Ummi da sauri yana jin amsar da zata bada daman tun shigowarsu yake son ya tambaya sai kuma ya danne zuciyarsa saboda Ummi. "Tana lafiya" "Amman ta fito waje?" Aliyu ya tambaya, sai Ummi ta yi kamar bata ji shi ba. Daddy ya ce. "Amman Aliyu kana tunanin Turhan zai fahimce ka kuwa?" "Abu ne mai wahala mahaifiyarsa ma dazun sai da ta fada min magana" Ummi ta fada, Aliyu ya tambaya. "Me ta fada miki?" "Shirmen mata ne, kasan mu sa kananan maganganu" Aliyu yayi shiru slowly slowly ransa ya fara baci amman be ce komai ba. Daddy kawai ya koma gida Ummi a asibitin da kwana tare da dan'uwansu Muktar duk kuwa da irin yadda Aliyu ya so ta tafi ta bar Muktar din ya kula da shi, Daddy har zolayarta yayi wai ta zabi a ta bar miji, ta fada masa ana canja miji ba a canja a ba. EMILY POV. Wannan ne dare na farko da bata ji dadinsa, saboda ta kwana da kewar Fatima sosai, gashi ta yi bakunta a gidan da mutumen data sani baya cikin gidan sai bakin fuska. Abincin ma bata wani ci abun kirki ba abun duniya ya taru yayi mata yawa. Tun gabanin Asuba bachi ya yanke a idonta sai hawaye ne suke ta aikinsu ta yi iya tunanin ta yi iya hangenta amman ta gagara samun mafitar da zata iya amfani da ita yarta ta dawo gareni. Wannan dalilin ya saka duk yadda ta hana zuciyarta daga ganin laifin Aliyu sai ta kasa domin shi ya janyo mata komai. Ba zata hana zuciyarta aminta da shi ba, amman bata da tabbacin abun da yake zuciyarsa da na mahaifiyarsa, domin Ammy da Khaleefa darasi a rayuwarta. Bata sauko kan gadon ba har sai da Ummi ta dawo daga asibiti ta leko dakin daman tun fitar Nafisa a jiya babu wanda ya sake lekota duk wani kai da kawo da ake a