← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 177

Sashe 18

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 8 Ya furtawa yarinyar yana fa a fuskarsa da murmushi, matsawa ta yi baya ta ta kauce daga mutanen da duke tsaye jiran fitowarsa, hakan ya bashi damar fitowa har ya amsa gaisuwar da ake mika masa, sannan ya kalli yarinyar data matse jikin ginin dake bayanta kamar zata shige ciki, gashi ta hade rai irin na yaron da yayi arba da bakuwar fuskar da be sani ba. Tsayawa yayi a gurin har sai da kowa ya shige cikin Elevator sannan matsa kusa da ita yana murmushi ya mika mata hannunsa. Ta hade hannayenta ta kawar da fuska. Momy na tace na daina magana da wanda ban sani ba, za a iya sace ni Murmushin fuskarsa ne ya fadada ya gingina kai. Gaskiya ne, ni ma ta fada min haka ta fada miki shiyasa ba zaki amsa ni ba idan na miki magana, amman na san ki mahaifiyarki ta nuna min hotonki a wayarta tun da dadewa shiyasa yanzu ma ina ganinki na gane ki Ta juyo ta kalleshi. Da gaske Ya daga mata kai. Uhm- To waye kai? Ni... Ya nuna kansa yana tunanin me zai fada mata, sai ta ce. Are you her new boyfriend? Ya wara ido. Boyfriend? No... Karki ji haushi ki yi kishin Babanki Ni ba ni da Baba ai, Momy na tace bata haife ni da Baba ba, tsaya ma ka ji sunana Fatima Aysha Emily, amman yayana yana da Baba shi sunanshi Londom Hamza, amman shi babansa ya mutu kamar yadda Momy ta fada, amman ni ba ni da Baba, amman ka ga kowa yana sa baba ko a makarantarmu kowa yana da baba ban da ni, shiyasa na matsu Momy na ta yi new boyfriend so that na samu Baba, saboda na tsani Vito bana son shi shi kuma wai yana son Momy ne, amman ni bana son shi.... Sai da ta kai ayar zancen sannan ta numfasa, mamaki da burgewa ya saka Aliyu jan numfashi. Hmmmmm wannan yarinyar ya a je da ke Hi-five Ya mika mata hannu ta mika masa nata suka taba, shi kam abun nema ya samu daman bincikarta yake son yin, sai kuma yayi sa'ar ita din ku ace gurin magana, ya kama hannunta yana murmushi tunawa da yayi da matar dazun wanda tace idan ta sake masa magana ya kirata da aku and he did. Ciki zaki shiga? Eh Momy na tace na zo na same ta a nan saboda yau nannynmu tana gurin London ba shi da lafiya yana asibiti shi sickle ne kuma Autisms, baya yarda da mutane sosai daga Vito sai Nanny Chidimma sai Momy sai ni Ya nufi elevator ya danna ta bude. Sai da suka shiga sannan ya sake tambayarta. Shi Victor shi ne Babanki? Ko saurayin Momy kika ce ko? Ta tofar da yawu. Allah ya kiyaye bana son shi, sunan shi Vito not Victor Vito sunan yan Italian ne da aka samo daga latin word Vita Vito yana nufin rayuwa, sunansa ke nan? Amman miyasa kika tsane shi? Ba shi da kyau ne Yana da kyau, amman baya yin dariya, and wata rana idan Momy ta bata masa rai sosai yana dukanta, i just hate him, kawai ina zama da shi ne dan dole, amman Momy tace da sabon aikin da ta samu yanzu zata siya gida zamu koma can Vito ba zai sake zuwa gurinta ba Aliyu ya daga girarsa sama ya sauke yana tan tabe baki kadan. Wow, okay Ina son haka, and na san idan Momy ta bar gidan Vito zata samu Boyfriend sai ya zama Daddyna, ni ina son Daddy Aliyu ya rage tsayinsa ya kama fuskarta ya rike cike da tausayi, ko bata fada masa uwarta ba ya fahimci akan waye take magana, secondly fuskar abokinsa dake shimfide a yarinyar yake kallo. Amman kai kana da girlfriend? Yayi murmushi kawai ya mike tsaye ba tare da ya amsa mata ba. Ita ma bata sake cewa komai ba har suka sauka a 5floor. Momy na tace a 4 Floor zan sauka office na biyu hannu dama shi ne nata Na sani, ina son na kai ki office dina ne mu gaisa Ya shiga office din yana rike da hannunta, ta bude ido tana ta kallon office din. Amman kai ya sunanka? Aliyu Okay Mr Aliyu are you Muslim or Christen? Muslim amman Momy na Christen ce, but her name is the Aysha Ya bude fridge dinsa ya dauko mata lemu ya bata. Taya kika zama musulma mamarki ba musulma ba? Ta nufi kujera ta zauna ba tare da ta jira ya mata izini ba. Okay, Momy na tace babana musulmi ne shiyasa ta saka min suna Fatima kuma na tashi ta ga ina son musulunci shi ne take barina ina yi, ta koya min sallah, ta fada min ita ma ta taba yin musulunci, amman yanzu ta daina Ya zauna a kujerar dake facing din wanda take zaune. Kin fada min baki da baba? Taya kuma zaki ce babanki musulmi ne? Ni ma haka Momy na ta fada min, shiyasa nake son ta samu new boyfriend ya zama daddy na, amman kai kana da mata? huh-? Ya bude baki not knowing what to say. Ta yatsina fuska. Kana da ita? Uhhhh No Ya amsa mata saboda ta saki jiki da shi ya samu abun da yake so. Okay Good Ta masa thumb up ta fara shan lemun da ya karba ya bude mata ya bata, ya ciro wayarsa ya dauketa hoto. Hoto kake daukata? Ya juyar da wayarsa ya kalli wayar ya manta flashlight din wayarsa a kunne yake. Kin min kyau ne shiyasa nake daukarki hoto, kina da kyau, zan so haihuwar kyakkyawar yarinya irinki, so ina son na dauko hotonki ne na aje ina kallo a wayana, saboda mamanki tana min rowarki ba zata tura min hotonki ba Ya fada mata haka ne saboda ya wanke kansa. Why? Ko zaka sace ni ne? Nooooo ta fada min akwai hotunanki masu yawa a wayarta, nace ta tura min tace aa ba zata tura ba Idan kana so zan tura maka Taya? Zan karbo wayar Momy na tura maka Aa ai ba zata yarda ba, amman ina son ki yi a boye, zan rubuta miki number na sai ki saka a wayar Momynki ki duba whatsapp dinta ki tura min hotunan ta can idan kika tura sai ki goge karki bari ta sani, kin iya turawa ai ko? Ta daga mishi kai. Na iya, amman ban iya gogewa ba Ya bude whatsapp din wayarsa ya nuna mata yadda zata goge. Kin gane? Ya tashi ya bude karamar durowa ya dauko katinsa ya bata. Idan kika gama sai ki jefar da katin a inda ba za a gani ba Okay Samun hotonta da hoton mahaifiyarta zai taimaka masa sosai gurin samawa abokinsa mafita cikin sauki. Ya matsa kusa da ita ya rumgume ya sumbanci kanta, sai ta lafe a jikinsa ta yi shiruuuuu kamin ta dago ta kalleshi ta yi murmushi. Muje gurin Momy ki kar ta nemi ki bata ganki ba, amman wannan sirrinmu ne ba zaki fadawa kowa ba haka ne Yanzu na san dalilin Mamankin na cewa kar ki yi magana da wanda baki sani ba, you're talkative Ya fada a ransa domin samu abun da yake so cikin sauki, ya kama hannunta. Mu tafi Ya rike hannunta suka fita office tana kara masa wasu labarunka da be sani ba, amman hankali ya tafi wani guri he just can't wait ya nunawa abokinsa hoton yarinyar nan da kuma mahaifiyarta, ya san ba karamin dadi Turhan zai ji ba na samun Aysha kawai balle kuma ace ya ga yar nan mai kama da shi. EMILY POV. Ta kalli wayarta dake ringing ganin sunan driver Fatima ya saka ta mika hannunta da yayi tsami saboda typing din da take tun safe ta dauki wayar cike da gajiya. Hello Ranki ya dade gani na iso gurin tare da Fatima Bata wayar Ya mika mata kamar yadda ta umarce shi. Hi Momy Hi Baby ki shigo ciki zaki ga Elevator irin wanda muke hawa a New York da Abuja kin tuna? Sai ki taba number 4 idan ya iso office na biyu hannun dama shi ne nawa Okay Momy Ya aje wayar yana mika ji take kamar ta gudu saboda wahalar typing din da take amman babu saboda muradun dake zuciyarta. Kamin ta kalli kofar office din wata matashiyar yarinya ta turo ta shigo. Hi how can i help you? Matashiyar ta karaso kusa da ita. Sunana Raheenatu, ni ce sabuwar Assistant ta Miss Amal da aka dauka Emily ta gyara zama tana kallonta with little bit of confused. O... Ka..y.... Congratulations Thank you, am an fada min nan ne office dina, na yi tafiya ne yau na dawo shiyasa ban samu shigowa da wuri ba sai yanzu No wata kila sun yi kuskure ko kuma ke din baki gane wane office ba, domin ni ce a wannan office din kuma ni ma Assistant din Amal ce I don't think so, but bari na tambaya Okay Ta juya ta fice, Emily ta bita da kallo har lokacin mamaki take, ana daukar masu taimakar har biyu ne ko kuma dai kuskuren ta yi kamar yadda take zargi? Can kuma wani tunanin ya zo mata, kar dai ace mutumen da ta yi ma magana dazun babba ne a gurin ya saka aka koreta, bata gama raba dayan biyu ba Amal ta turo kofar ta shigo. Emily kika ce ba a nan office din ba ne? Emily ta mike tsaye da sauri domin girmamawa ga Amal. Yes saboda Ni nake nan, sai dan za a kara wata ne, amman na fi tunanin ko ta yi kuskure ne shiyasa nace ba a nan ba ne, maybe office din gaba ne Amal ta yi murmushin rainon wayo. Nan ne, ita sabuwar Assistant dinta Emily ta wara ido irin na mai mamaki Ni kuma fa? Ke ai da ke da babu duk daya, kamfanin nan be san da zamanki ba? Kamar? Kamar yadda na fada miki, tun da aka dauke ki aiki baki sign idan zaki fita ko kuma idan kika shigo, saboda haka ke da babu duk daya a kamfanin nan, shiyasa aka daukar
Chapter 18 · 0% Book details