Sashe 19
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
min sabuwar ma'aikaciya, dan haka ki hannata mata komai ki bata office Wani abu da bata yi tsammani ba ne ya zo mata a zuciya ya raunatata yayi nasarar saka ta tara ruwan gishi idonta wato hawaye. Emily ta bude baki ta fara magana a daidai lokacin da Aliyu ya shigo office din da Amal ta bari bude yana rike da hannun Fatima. Ban san ana sign in and out idan za a fita ba? Ni zan fada miki? Ban baki dokokin kamfani kika karanta ba? Kamin Emily ta amsa Amal ta kalli Aliyu cikin girmamawa ta gaisheshi. Good Afternoon Sir? Ya kalleta ya kalli Emily dake hawaye ya kalli matashiyar yarinyar sannan ya kalli Amal with seriousness. Me ke faruwa a nan? Ranka ya dade tana cikin sabin ma'aikatan da aka dauka ne, amman bata zuwa tun da aka dauke ta yau kwana uku, shiyasa kamfani ya dauki wata What-... Wallahi ba gaskiya ba ne, ina zuwa tun da aka dauke ni, kawai bana sign in and out ne shi ma ban sani ba, bata fada min ba Ba a baki file mai dauki da dokokin kamfanin nan ba? Baki karanta ba? An bani amman Wallahi babu gurin a ciki, ban ganshi ba ban sani ba, kuma bata fada min ba, abun da kawai ta fada min idan na shigo na goge mata office dinta na gyara, kuma na rika shigowa karfe 6:30am na safe, jiya ma na yi typing har na 4pm sai da na gama na tafi, gashi a Systems dita, and yau ma gashi ka ga ina yi Cikin kuka Emily take maganar ta juyar masa da system din. Aliyu ya kalli Amal. Cire takardar kika yi a dokokin kamfani? Aa Sir karya take min sheri ne kawai Amman a dokarmu babu aikin saka ma'aikanmu aiki, idan za'ayi gyara ko wani abun akwai masu yi, har sai idan mutum yafi sha'awar aikatawa da kansa zai aikata, muna da masu aika da zasu siya muna abu, muna da clearness masu gyara guri kullum da safe, and time din shigowa kamfanin nan ga ma'aikanta mu is 8am, masu shara ne suke shigowa 6:30am haka ne? Jikinta ya fara rawa. Haka amman karya take min, daman tun da aka dauke ta na lura haushina take ji so take kawai ta kulla min sheri Emily ta share hawayenta. Na kulla miki sheri? Saboda me? Ina da wata alaka da ke ni bayan ta aikin da ya hada mu kwana biyu zuwa uku? Aikin ne baki son na yi shiyasa kika ce na rika shigowa karfe 6 na safe? Kika sakawa ina goge miki office alhalin ba haka dokar take ba? Kika sakawa ina tafiya mai nisa na siyo miki abun da zaki ci? Kuma baki taba fada min ana sign ba? Aikin ne baki son na yi? To na bari daga yau, ni ban shirya tarwatsa rayuwar kowa ba, daman tun da na ganki na san ba za mu jitu da juna ba, saboda ke musulma ce, musulmai ba su da halin kirki sai karya alkawari sai wulakanci sai kyama da nuna banbanci, daman ai ba zaki taba abun kirki ba saboda ke musulma ce, musulmi be taba min abun kirki ba, sai zalinci shiyasa na tsane ku na tsani addininku Ta karasa cikin kuka da tsawa sannan ta cire id din da yake wuyanta ta jefar kasa ta dauki jakarta ta nufi yarta da Aliyu ke rike da hannunta ta fisge ta fice daga office din. Aliyu ya kalli Amal a tsanake ya fara mata magana. Ba iya suturarmu ce take walkiltar addininmu ba, har da mu'alama da kalamai da dabi'u, kasancewarmu musulmai kawai ta hanyar shigarmu ko sunanmu ba zai wadatar ba, har sai dabi'unmu da mu'amalarmu ta banbanta da ta kowa, ta hanyar kyautata, tausayawa, adalci da kuma bawa kowa hakkinsa, ni musulmi ne ke ma haka, addini ya koyar da mu yadda zamu zauna da wanda ba musulmai ba mu ba su hakkinsu, idan musulmi yayi mummunan aiki, to yana wakiltar duka musulman duniya ne a idon wanda ba musulmai ba, su basa banbance akwai na gari akwai bata gari a cikin addininmu, haka kuma idan musulmi daya yayi abun kirki to a idonsu duk musulmi na gari ne, sai su ji suna sha'awar koyarwar addininmu da dabi'unmu, ban jidadin abun da kika yi ba, ya kamata mu zama jekadu na gari ko'ina I'm sorry Sir, amman sheri take min ba gaskiya ta fada ba Be sake ce mata komai ba ya fice daga office din, office dinsa ya nufa kalaman Emily na masa yawo, ya tsinci na tsinta ya watsar da wasu, abun da ya fi tsaya masa a rai kuma ya sosa masa zuciya furucinta na cewar musulmi ba su taba yi mata abun kirki ba, musulmi ba su da tausayi, kuma ta tsani musulunci. Ya yarda da kalamanta ne sama da na Amal saboda ya ganta sau biyu a kamfani ta siyo abu kuma ya ga shigowarta a yau da sassafen nan kamar yadda ta fada. Ya zauna a kujerarsa yana mamakin wani abu. Anya wanda ya tsani musulunci zai iya bari yarsa ta yi addinin musuluncin har ta koya mata sallah? Kuma ta sakawa yarta sunan Fatima? Ita ya aka yi ta samu suna Aysha? Ta tsani musulunci ta tsani musulmai ko kuma dai mu'alamar wasu daga cikin batan garin musulman ne ya saka ta tsani musuluncin? Yana ta sake sake a zuciyarsa, for the first time ya ji yana sha'awar jin full dalilin rabuwar Turhan da matar da yake ta nema yanzu, domin ya tabbatar ita ce wannan duk kan wata alama ta bayyana hakan, dole akwai wani babban dalilin da ya saka ta boyewa yarinyar cewar tana da uba, and dole akwai dalilin da ya saka ta tsani musulunci. Har yanzu dai ba zai karyata ba tana da masifar kyau fuskarta ta tsaya masa a ido, and when ever idanuwansa suka sauka a fuskarta sai ya ji kamar ya santa, wadannan blue eyes din nata suna raya masa saninsu but be san a ina ba, maybe kyaunta ne yake rudarsa. Har ya daga wayarsa zai kira Sahibar tasa sai kuma ya tuna horo yake mata saboda ta gane girman laifinta, kuma ya ladaftarta ita da abun da bata saba ba saboda ta kiyaye a gaba. ________________ Masu karatu ya kuke ganin Turhan zai yi idan ya samu Aysha? Kamar dai Aliyu Ni ma ina son sanin dalilin Emily na tsanar musulmai kuma ina son sanin a ina sunan Aishar nan ya samu asali? [4/20, 9:59 AM] : https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w ABOKIN RAYUWA