← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 177

Sashe 86

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama" "Aa ba tunani nake son ka yi ba, idan ka tsaya tunani ai sai shedan ya samu damar baka wata gugurwar shawara, domin shi kullum burinsa ya lalata rayuwar aure, dan Allah ya shirya cikin weekend din nan ka zo ka dauki matarka, gobe friday zuwa assabar ko lahadi sai ka shigo ka koma, ka turo min number Mahaifiyarka na kira ita ma na bata hakuri" "Aa ba sai kin kira ba, bata ma san abun da ya faru tsakaninmu ba" "Tohm ai haka ake so, ana son ma'aurata su zama masu sirri, Allah ya hada kanku ya baka hakuri da wuyan dauka, kuma maganar nan ta tsaya daga ni sai kai dan Allah, domin Kameela da iyayenta ba su san na kira ba, ni ce kawai na damu da halin data shiga shiyasa na kiraka mu yi magana, number ka ma a boye nasa yara suka dauko min, ba tare da sanin Kameela ko iyayenta ba" "Na gode Mama" "Toh Allah ya maka albarka, kuma ka kara hakuri domin matarka tana kaunarka sosai" "In Shaa Allahu" "Na gode" Ya sauke wayar, ya amsa mata ne kawai saboda yana jin nauyin ce mata aa ba zai iya ba, haka kuma yana tsoron matsalar da fadin gaskiyar abun da Kameela ta yi masa zai janyo, ita yake tausayi ba kansa ba, domin ya san tana son shi, kuma ya san irin gwagwarmayar da suka sha kamin aure, kana ya san idan har aka ji abun da ta yi abu ne mai wahala wani namiji ya sake aurenta, shi kansa ya san auren Kameela jarabawa ne a gurinsa ba dan baya kaunarta ba sai dan zafin kishinta da kuma halin da take kokarin jefashi kuma ta jefa kanta. EMILY POV. Bata farka ba sai karfe takwas na safe, saboda tunani da kuma dukan da Vito yayi mata be barta ta sami bachi da wuri ba, daker ta iya saukowa daga kan gado saboda tsamin da jikinta yayi ko'ina ciwo yake mata. Bathroom ta fara shiga ta wanke bakinta ta yi wanka da ruwa mai zafi sosai saboda ta gasa jikin sannan ta fito daure da tawul, rass gabanta ya yanke ya fadi ganin Vito tsaye a dakin yana jiran fitowarta. Tsayawa ta yi cak a jikin kofar bata karasa fita ba kuma bata koma ciki ba sai kallonsa take. "Good Morning" Ya tako zuwa inda take sai ta yi baya baya zata koma ciki, ta bata fuska sosai alamar zata yi kuka. "Tsorona kike ji? I'm so sorry i didn't mean to hurt you ke kika janyo, jiya ban yi bachi ba saboda tunanin abun da na yi miki" Ya karasa ya rikota ya fito da ita sai ya rumgume ta a kirjinsa. "I'm sorry" Sun dade a haka kamin ta dago daga jikinsa ta nufi kujera ta zauna. "Jikinki da zafi zan kira Likita ya zo ya duba ki" "Bana bukata" "I'm sorry Emily am sorry" Ya karasa kusa da ita sai ya zauna a kasa ya kama hannunta ya rike. "I'm really sorry, zuciya ce ta rufe ni" "Wannan ba shi ne karon farko ba" "Na sani, kuma ba zai zama karon karshe ba matukar baki daina kula wasu mazan ba, kuma baki cire ranki akan addinin nan ba" Ta fisge hannunta daga rikon da yayi mata ta mika tsaye, short gown ta dauko ta saka ta daure kanta da ribbon tana kokarin juyowa ta ji shi bayanta tsaye. "I'm sorry Emily I'm sorry, i didn't mean to hurt you" Ya juyo da ita yana kallon fuskarta dake zubar da hawaye. "But you already hurt me, baka da banbanci da Khaleefa shi ma dukana yake, Turhan ma ya dukene, kowanenku yana juyani ne son ransa, idan kuka gaji da ni sai ku watsar, ina ta fadawa hannun mutanenda babu komai a gabansu sai son zuciya, na tabbatar da ace ni kanwarka ce, ba zaka yarda wani yayi mata wannan dukan ba, jiya ban iya bachi da wuri ba saboda radadin dukan da ka yi min, takamarka kawai saboda ina karkashinka ne, saboda kana ganin ba ni da kowa, da ace ina da gata ba zaka min wannan dukan ba Vito" Ta wuce shi ta fice daga dakin, zaunawa yayi a kujerar data tashi dazun ya dafe kansa, babu abun da ya tsana kamar ganin hawayen Emily, a yau da ace wani ne yayi mata abun da yayi ba zai kwana duniya ba, but still yana jin babu dadi meyasa ba shi da hakuri why yake da saurin hannu? Yana son Emily yana mutuwar sonta yana kishinta wannan ne abun ne ya ci shi da yaki ya gagara fin karfin zuciyarsa har gobe... Tana fita dakin ta nufi downstairs, sai kuma ta fasa sauka ta dawo saman ta nufi dakin London ta shiga, saboda tana bukatar gurin da zata kebe ta tausayawa kanta. Sai dai kuma shiga dakin ya dawo mata da tunanin danta da kewarsa, dakin yana nan yadda ya bar shi babu abun da aka cire ko aka sauya, sai datti da yayi domin Chidimma ta daina share dakin. Kwalliyar dakin ta fara kallo sannan ta sauke idonta gurin hotonsa ta karasa gurin gadon ta zauna a kasa ta dora kanta akan gadon tana hawaye. Can kuma ta dago tana kallon study table dinsa dake gefe daya, ta tashi ta koma kan teburin ta zauna saman kujera tana duba takardun da yake zane da su da rubutu, wani gurin ya zana ta ya zana kansa da Vito da Fatima da Chidimma ya rubuta sunan kowa, ta kai hannu tana shafa zanen, ta bude wasu takardu ta dauko tana dubawa, wani gurin ya rubuta, na yi fushi wani gurin ya rubuta i hate Momy, wani gurin ya rubuta I'm sick har ta kai gurin da ya rubuta. "Chidimma tace Momy bata so na, bata so na bata so na bata so na, tana son Fatima Fatima bata son London, Chidimma tace Momy bata son London, Momy bata son London Momy ta tsani London" Tana karantawa hawaye na sauko mata kamar ruwa, ta girgiza kai da sauri. "Ina son ka dana, ka fi soyuwa a raina fiye da Fatima, baka fahimce ni ba ne" Ta kwala wani uban ihu cikin kuka, ta mike tsaye da fito dakin da gudu kamin ta sauka kasa Vito ya fito dakinta ya biyo bayanta Chidimma dake mopping ma ta tsaya tana kallon Emily dake saukowa tana kuka rike da takardun. "Meyasa kika saka dana ya tsane ne? Me na miki? Me yasa kika tsane ni? Me na miki? Kin sa ana ya mutu da tunanin bana son shi, baki kalli lalurar da take tare da shi me yasa kika cusa wannan a kwakwalwarshi? Yanzu ta ina zan fada masa ina kaunarsa? Ta ina zan nuna masa kaunar da nake masa? Why Chidimma why? Shiyasa ya daina son na rabe shi na baya yarda da ni sai ke? Why Chidimma why?" Kalaman Emily ba su daga mata hankali ba kamar kallon da Vito yake mata. " Ki amsa me yasa kika yi?" Ta girgiza kai jikinta na rawa numfashinta na gargada. "Ba haka ba ne, wata kila be fahimta ba shiyasa yake rubuta wannan, amman ban fada masa cewar baki kaunarsa ba, ba gaskiya ba ne" "Meyasa Matata tsone miki ido? Na sha fada miki ki daina fada min idan Emily ta yi wani abu, kamar jiya, ke kika fada min ta shirya ta shirya Fatima cikin abaya sun fita, kika sa na zo na mata duka da ya tsaya min a rai yanzu yana ci na, kuma na gargade ki ba tun yau ba akan ki cire idonki akan Emily, the more kika fada min laifinta the more zan tsane ki, me yasa kika shiga tsakaninta da London why? Answer me....!!! Da farko cikin natsuwa ya fara magana da mugun kallo, daga karshe kuma ya karasa da tsawar da ta saka Chidimma sakin fitsari... Hmmmmmm, masu karatu wai ba ku ganin Aliyu yana wuce gona da iri ne? Ina Team Vito? Ni fa iya wuya muna tare wanda ya so ka taimaka a lokacin da baka da komai ai shi ne naka. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [6/22, 6:33 PM] : https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 ABOKIN RAYUWA
Chapter 86 · 0% Book details