← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 177

Sashe 168

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 7 TALIYAR HAUSA YAR MURJI Abinci na gargajiya, ano na musamman, jin da in iyali! Idan kina/kanason abinci mai ano na musamman wanda zai tunatar da kai da in gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al ada ce mai ha a iyali, auna da jin da i a teburin gida. Me yasa za ka za i Taliyar Hausa Yar Murji? An yi ta da tsafta da inganci Ta dace da kowanne irin miya: miya mai wai, miya taushe, ko miya mai Sau in dafawa cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa Lafiyayye, mai sau in narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman Muna a Kaduna amma anonmu ya zarce iyaka! Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). Idan kana son jin da in abinci na gida wanda ke ha a zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa Yar Murji yau! wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. Ka more anon gargajiya mai tsafta, mai da i, mai orewa! "Okay bari idan na duba zan miki magana" Ya amsa sannan ya kashe wayar ya aje sannan ya dauki comb din yana gyara mata gashi, suna zaune a falo, shi kan kujera ita kuma tana kan kasa. "Daga gurin aiki ne" Ta dago ta kanta ta kalleshi. "Ban tambaya ba ai, Aliyu i trust you, kullum aka kira idan agabana sai ka ce min ga wanda ya kira, ina son ka san kai ka aje ni ba ni na aje ka, kuma kana aiki dole mu'amala zata hadaka da wasu wani lokacin, dole na yi hakuri, kuma kana da yancin haka, matukar be tsabawa addini ba kamar yadda kake yawan fada, kuma be tsabawa zamantakewarmu ba, ba zai kawo matsala ba, ni na yarda da kai, na san wa na aura" Ya ja hancinsa yana murmushi kadan. "Kin ance hadarin da ya baka kashi, gobe idan ka gan shi gudu kake, na dan shiga damuwa ne, saboda irin haka, kuma ya haifar da matsala kala kala a zamantakewata ta baya, na yi iya yadda zan iya wajen ganin ba a samu matsala ba amman hakan be samu ba, kuma ba a raba mata da kishi dole za ku yi kishi ai, kawai dai ba a son ya wuce gona da iri ne saboda yana haifar da matsala, ko ga matar ko ga miji ko kuma duka" "But don't get mad at me idan na yi kishi" Ta fada a shagwabe tana turo baki. Yayi murmushi ya saka hannayensa ya dagota "Come here" Ta daga ta koma saman jikinsa ya rumgumeta irin yadda ake ma yara har ya dan girgiza ta a hankali. "Thank you for trusting me, i love you Qalbin, ba zan ji haushi ba idan kin yi kishi, ke ma ina hango kishi a idonki, amman ki iya rike shi ki yi controlling dinsa kar ya cutar da ke" Ta lafe a jikinsa tana ta zuba shagwaba. Ya cigaba da shata mata kan a haka tana masa raki har da kuka wai da zafi. "Shiyasa ai nake miki a gida, ba zan yarda kina tafiya shagon gyaran gashi ana kalle min kaya kuma jansa da karfi ana wahalar min da mata ba" Ta kai hannunta tana taba chin dinsa zuwa wuya. "Babe..." "Mhn" "Ina son na yi ma Dr A-B maganar tafiya gurin baban shi ina son na gan shi na ji yayi shiru be sake min maganar ba" "Lallai kuma ya kamata ya hadaku ko a waya, kuma ina son idan kin samu time ki tafi ki gurin Ammy ki bincika Fatima ko lafiya" Ta kara daga kai ta kalleshi. "Ba matsala?" "Bana jin wata matsala to matsalar me? Ni da na rike na mallake ki na malleke zuciyarki, na san kin damu ki san halin da take ciki ai, kina da aurena yanzu idan ma Turhan yana gidan dole ya daga miki kafa, balle na san ba ya nan, kuma ba ni da hujjar hana ki ziyarta su tun da Fatima ta shiga tsakani, kawai dai abun da ba zan yarda ba shi ne ki shiga ki dade ko ki wuni, ni zan kaiki na jira ki gama abun da za ki yi na dawo da ke" "Na damu sosai na san halin da take ciki" "Na sani, ina karantar damuwarki ko ba ki fada min ba, ya kamata ace ko sau daya ne ta zo gidan nan ai" "Za mu iya tafiya gobe?" "Mu tafi anjima da dare" "Da gaske?" Ya kai mata rankwashi a kai. "Ina miki karya ne?" Ta dafe kan "Da zafi fa" Ya kara mata wani, da ta ga zai kara mata na uku sai ta sauka jikinsa da sauri ta dauki fillon kujera ta jefeshi da shi. "Zan kama ki ne ai" Ta masa gwalo ta gudu. Bayan Sallah isha'i ta shirya, Aliyu ya sakata mota suka dauki hanyar gidan Ammy. A waje ya faka ta bude zata fita sai ya sumbanci hannunta dake cikin nasa. "Ko da Ammy ta fada miki wata magana marar dadi karki ce za ki yi fada da ita a gaban Fatima" "Okay" Ya sake mata hannun ta fita ta rufe motar, sannan ta kwankwasa gate din gidan aka bude mata. "Ammy na ciki?" "Eh tana nan" Emily ta shiga tana sayen da hijabinta na islamiya da ya kai mata har kasa, cike da zumudin son ganin Fatima ta kwankwasa kofar falon, aka bude mata ta shiga. Da sallama yan matan da suke nan suka amsa mata bata zauna ba sai da ta tambaya ko Ammy na nan aka ce mata eh tana nan, sannan ta zauna zaman jiran fitowarta. Ammy ta dade sosai kamin ta fito falon ta zauna fuska ba yabo ba fallasa ta zauna tana kallon Emily dake gaisheta. "Lafiya kalau" Emily ta dan yi shiru na lokaci kamin ta ce "Daman kwana biyu ban ga Fatima ba, shi ne na zo na dubata" "Fatima kuma? Ba Turhan ya fada miki zai tafi da ita ba? Ai Fatima bata gidan nan tana gurin Babanta" "Gurin Babanta kuma? Ya fada min amman ban ce masa na amince ba, kuma ko bankwana bata zo yi min ba" "Bankwana me ko? Ba an kai miki ita kun yi biki ba?" Idon Emily ya cika da hawaye. "Amman sai a dauke ta a tafi da ita ba tare da an fada min ba, kamar na ni na haife ta? Wannan wane irin abu ne haka? Yarinya karama a dauke ta a kaita gurin larabawan da basa son kowa idan ba jinsu su ba? Kun zalince ta kun zalince ni" "Kin damu da ita kika bar ubanta kika auri makiyinsa? Ko kuma saboda ke sai ya fasa tafiya da yarsa gidansa? Ita ba jininsu bace? Yadda Turhan yake son Fatima ai ba zai bari a cutar da ita ba, ba fin shi sonta kika yi ba" Emily ta mike tsaye tana hawaye. "Ke ma fa uwa ce, zafin nakuda zafin haihuwa wahalar raino duk kin sani, da aka dauke Turhan daga gurinki ina ne baki shiga kin fita ba saboda ya dawo gareki? Miyasa ni zaku azabtar da ni da wannan?" Ammy ta mike tsaye. "Fita ki bar gidan nan, na girmi na tsaya sa'insa da ke, kuma karki kuskura dora misalinki da nawa, dan muna da banbanci, da kina son Fatima da labarin yanzu ai ba haka yake ba" Emily ta dubeta tana hawaye ta sake dubanta sannan ta fice tana hawaye har ta fita gidan. Ko da ta iso gurin motar Aliyu na tsaye jikin motar yaja jiranta, ya ga hawaye a fuskarta amman be ce mata komai ba ya bude mata motata shiga, ya zagaya ya shiga yaja motar, sannan ya kai hannunsa ya kwanto da kanta jikinsa ya rike hannunta yana tukin da hannu daya. Daman ya raya a ransa Fatima bata gida, ya san da tana gidan ta yanzu ta matsa an kawota gurin Emily ko dan ta ga sabon gidan da Emily take. Aliyu be tambaya me ya faru ba, hawayenta kadai sun sanar masa ba ayi da dadi a gidan ba da suka iso gida ya faka motar sai ya fito ya bude mata ya riko hannunta ta fito yana janye da ita har cikin falonsu. Saman kujera ta zauna shi kuma ya risina gabanta yana kallonta. Kamar jira take kawai ta fashe masa da kuka tana fada masa abun da ya faru. Yanayin fuskarsa ya sauya zuwa damuwa, sai dai be ce mata komai ba ya mike tsaye ya shiga dakinsu ya dauko wayarta data bari a gidan ya dawo falon, da kansa ya saka number Turhan dake wayarsa cikin wayarta yayi dialing sannan ya mika mata. Kallo daya ta yi ma wayar ta gane number Turhan ce saboda number bata Nigeria ba ce kuma akan rigimarsu ake ta san ba zai wuce ya kira mata Turhan din kai tsaye ba. "Are you okay with that?" Ta tambaya cikin kuka ya daga mata kai, sannan ta karba shi kuma ya zauna gefenta ya saka hannunsa daya cikin nata domin karfafa mata guiwa. "Hello..." Ta fada cikin sautin dake nuna ta yi kuka. Turhan yayi shiru be ce komai ba, ba dan kuma be fahimci mai magana sai dan kiran ya zo masa ba a lokacin da yake tsammani ba. "Turhan Aisha ce Emily" "Me ya faru? Me yasa kike kuka?" Ya tambaya daga dayan bangaren. "Na tafi ganin Fatima Ammy tace ka tafi da ni? Meyasa?" Ya lumshe ido ya shafa goshinsa a tunaninsa zata fada masa Aliyu ya mata butulci ne. "Bata min bankwana ba, tun da na yi aure bata zo gidan nan ba, a can bata san kowa sai kai, ta yi kankanta ta fuskanci kalubalen masarautarku a yanzu, kuma ni ina son ata, karka raba wannan soyayyar dan Allah, idan ma ba zaka yarda ta zauna a gurina ba, ka barta ta zauna a gurin Ammy mana, idan na so ganinta sai na tafi can na ganta, ka ce ba zaka sake cutar da ni ba miyasa ka yi haka?" Tun da ta fara maganar be ce komai ba sai da ta gama.
Chapter 168 · 0% Book details