← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 177

Sashe 170

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 7 Kin dade kina sha awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba? Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na yarki? To, ga sau i ya iso! ADASHE NE NA GATA! Ki zuba ku i, ki auki abin da kike so daga: Sutura da zannuwan gado Kayan kitchen Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu) Talkami da jaka Zanen gado Frames (flowers decoration ko standing ones) Console mirror Boxes na Lefe ko na traveling. Warmers iri-iri Food flask iri daban-daban Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so! i ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa. Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati. Akwai sharudda da ka idoji. Domin arin bayani, ki/ka tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660 Ko ta hanyar WhatsApp Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1 Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t Thank you Yana warware hannunsa da yayi alwala ya ce. "Ki shirya ina dawowa daga Sallah za mu tafi mu kaita" "Da gaske wai ba zata kwana nan ba? Ni ma fa ina da hakki da ita" Ta fada a shagwabe. "Toh haka Mama Ta fada min, za su aiko a dauke ta da karfe 9pm" "Kai ba zaka saka baki ba? Yaushe rabon da na ga yarinyar nan ta zo kuma sai ace ko kwana ba zata yi ba?" "Yanzu indai ba son kike Turhan ya zo gidan nan da wukarsa ya kwantar da kaina ya yanka ni ba, ina ni ina saka baki a lamarin yarsa? Hakuri za ki yi idan suka ga kamar ba ki damu ba za su daina, damuwar suke so daman ai, ni na tafi masallaci" "Allah ya dawo min da kai lafiya" "Ameen I love you" "I love you" Fadawa junansu kalmar suna son junansu wata sara ce da Aliyu ya koya mata, ba ya fita be ji kamar daga bakin matarsa ba, ita ma bata yarda ya fice be fada mata ba, furta kalmar i love you yana kara danko kauna da soyayya a tsakanin masoya ko da yaushe musamman wadanda suke son junansu. Kamin da dawo ta zubawa Fatima abinci ta kara ci ta shirya ita ma ta shirya. Key ya dauka da wallet ya rike mata kofar falon ta fita sannan ya fita ya rufe, mota ma shi ya bude mata ta shiga ta rumgume Fatima a jikinta. "Ba zaki barta ta zauna baya?" "Aa na fi son ta zauna a jikina" Ya kalli yadda ta lankwashe kai tana ta zuba masa shagwaba. Ba zai iya hanata ba, duk yana ganin kamar zaman zai taba ta, sai kawai ya kai hannunsa ya gyara zaman Fatima daga jikin Emily zuwa kafafuwanta. Sannan ya zagaye ya shiga dayan bangaren ya tashi motar yana tukin yana kai hannunsa ya daga Fatima idan ya ga ta kwanta jikin matarsa. Gaban wani katon shagon kayan alatu ya faka ya shiga yayi manyan ledodi uku ya dawo da su bayan mota ya zuba sannan yaja suka cigaba da tafiya. Harabar gidan Mama Baraka suka faka Aliyu ya fara fita ya zagaya ya bude mata ya riko Fatima ta fito sannan ya riko hannun Emily ta fito ya bude back seat din ya dauko ledodin biyu ya rike. "Ba uku na gani ba?" Ya ja hancinta sannan ya rufe motar. "Daya ta ki ce" Ya dafa kafadarta kamar wata kawarsa. "Uhm Qalbina, dazun Mama ta kira ta ce muna da bako tace na kawo ki bayan na dauki Fatima, sai na ce mata ta mana hakuri har sai idan zan kawo Fatima" "Waye?" "Sai kin shiga zaki gani" "Turha?" "Maybe..." "Ba zan shiga ba, idan ya fada maka wata magana marar dadi fa? Kasan ba zan kyale ba" "Ke yanzu kin shirya fada da kowa akaina kenan?" "Har da kai kanka ba zan bari ba" Ya bude ido. "Eyyyy" "Uhm" "Ba za ayi komai ba, muje ciki dai" Ya sauke hannunsa daga kan kafadarta suka jera suna tafiya, zuciyarta bata hararo mata kowa ba sai Turhan, wata kila zai fada mata wasu dokoki ne ko kuma yace zai sake dauke Fatima gaba daya. Shi ya fara rike mata kofar ta shiga sannan ya shiga, daman Fatima ta dade da shiga ta bar su a waje. Ta shiga da sallama tana ta rabon ido bata ga kowa a falon ba sai Mama Baraka da Fatima ke jingine da ita suna gaisawa. Emily ta kalli Aliyu yayi mata murmushi ta yi zaton karya yake dan kawai ya daga mata hankali ya fada mata haka, saboda haka ta taka masa kafa da kafarta sannan ta wuce kusa da Mama Baraka ta zauna suna gaisawa. "Ya ce mim wai ina da baki, ashe ba gaske ba ne" Mama Baraka ta kalli Aliyu. "Gaskiya ne, Aliyu je ka shigo da su, suna nan BQ da ka zagaya baya ta nan kadan zaka gansu" Sai da ya mike tsaye ya fice sannan Emily ta kalli Mama Baraka ta ce. "Su waye Mama?" "Wai tsohon mijinki ne... Ko Hamza ko Khaleefa, Ummi ta turo su gurina, saboda sun tafi can ita kuma bata nan sai ta kirani tace wai sun zo gidanta ne suna son magana da ke, ita kuma bata ma garin yanzu kuma tana ganin duk wani abun da ya shafe ki mijinki ya kamata a tuntuba ko ni" Fuskar Emily ta sauya sosai zuwa wani yanayi mai kama da fushi da damuwa. Sai dai bata ce komai na har aka turo kofar falon Aliyu ya fara shigo sannan mahaifiyar Khaleefa ta shigo tare da shi da wani kawonsa, duk a kasa suka zauna sai Aliyu ne ya zauna a kujera, Emily ta kalli Khaleefa da rabin fuskarsa take a kone idonta na cika da hawaye rayuwar data manta take tunawa a yanzu. "Toh ga su nan, sun min bayanin komai kuma sun roki alfarmar a kira ki su roki yafiyarki, na yi magana da Aliyu yace yanzu kina murnar zuwan Fatima a bari sai dare idan kun zo kawowata kar a yi ruining din moment dinku" "Ina wuni Aisha" Cewar Mahaifiyar Khaleefa. Emily ta kasa amsawa hawaye na sauko mata, kewar anta ya dawo mata farko. "Wata kila la lallai ki gane mu ba, duk dai Hajiya ta miki bayani kuma ta mana bayanin komai, ashe kin gane mahaifiyarki Aisha, muna miki murna ta fada mana kin yi aure shi ma muna miki fatan alheri, mun zo nan ne saboda neman yafiyarki, abubuwan da suka faru wadanda ba su yi dadi ba, musamman tsakaninki da Hamza, ki yi hakuri ki yafe masa dan Allah, Wallahi abubuwa masara dadi sun faru kuma mun san hakkinki ne, rayuwa ta zama babu dadi, musamman ma yanzu da ya koma gida saboda mai gidansa ya koresa saboda ke, ya fada mana ya ganki amman an hana shi magana da ke, tun da ya koma kullum cikin maganarki yake, daga karshe muka yanke shawarar zuwa kai tsaye mu nemi yafiyarki" Cikin tsoro da fargaba Mahaifiyar Khaleefa take magana. Khaleefa ya dago idonsa da suka zare tsabar yunwa da wahalar ciwo ya kalli Emily da a yanzu ko kafarta be isa ya taba ba ya ce. "Ki yi hakuri Aisha na san ban kyauta ba, na san na zalunce ki na cutar da ke, amman ki yafe min, Wallahi na yi nadama kuma na yi ta nemanki amman ban same ki ba, ban san inda zan ganki ba" "Kowa ya cuceka sai kawai ya zo ya ce ka yi hakuri shikenan aikinka? Ka cutar da ni, ku biyun nan baku ragawa rayuwata ba, kara Ammy ta nuna min soyayya a baya, amman kai mahaifiyarka tana kallo ka tsake ni, na bar gari na kama hanyar da ban san kowa ba, kuka wulakanta ni kuka wofintar da ni saboda kawai ba ni da kowa, kasan ina da cikin anka amman baka damu da halin da zan shiga ba, idan jininku ce za ku yarda ayi mata haka? Na haihu a titi kamar na haifi shege, na dinga wahala da shi kamar ba shi da uba, har ya bar duniya be san ubansa ba, wai saboda kawai ni mushirika ce na musulunta na bar addini na bi na ku, kuka rika kirana tubabbiya kowa ya kasa tsaya min, kuka hade min kai bana jin sanyi kowa, bayan kuma kai ka rabo ni da inda nake da gata, ka yi aure baka fada min ba sai da na ji, kuma haka be maka ba, kuka bini da gori kuka koreni gidan, sanadin wahalar da ma sha na haifi ana ba lafiyayye ba" Tana maganar tana kuka sosai kukan dake taba zuciya, Aliyu kallonta kawai yake yana kara jin tausayinta da kaunarta suna shiga ransa. Khaleefa ya girgiza kai yana kuka. "Wallahi hakkinki be barmu ba, bayan kin tafi rayuwa bata mana dadi ba, gidan da kika bar ni ciki ni da matar da na aura gobara yayi komai ya kone, ni kaina daker aka fitar da ni ciki, kalli yadda jikina yayi fuskar babu rabi Aisha, matata bata fita ba, sai yara biyu kawai data haifa min aka samu ceto wa, bangaren mahaifiya aka siyar a gidan aka shiga nema min magani amman har yau ban warke ba, saboda ba ayi treatment din yadda ya dace ba, yanzu haka idan yanayi ya sauya na zafi wutar tana taso min, sun ce akwai cutar har a cikin cikina, Wallahi ba mu da komai a yanzu Aisha, kuma na san hakkinki ne dan Allah ki yi hakuri ki yafe min, aiki ma ya gagara samuwa a gareni sai daker aka dauke ni a gidansu Alhaji Aliyu, ashe shi ma rabon na ganki ne, tun bayan da ya tura ni gida kuma ban sake samu komai ba, ana ba ni da albashin amman kullum gurin magani suke karewa, abun da za'a ci ma wahala yake mana, shin duk ba hakkinki ba ne? Ki yafewa min na zo neman yafiyarki ne da tambayar cikin da na barki da shi" "Na haifi anka da wahala da bakinciki da ciwo, ya rayu da rashin sanin waye ubansa, ciwo ya wahalar da shi,
Chapter 170 · 0% Book details