← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 177

Sashe 87

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... FOLLOW ME ON FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3 Cikin karfi hali da kashe murya ta fara magana tana kuka. "Shekara cikin ta shida nake a gidan nan, idan ina nufin cutar da Emily ko yaranta zan yi tun kamin a kawo yanzu, a janye maganar London tun da shi ba shi da lafiya, amman Fatima tana da wayo tana da fitina, da a ce ina musu wani abun cutarwa da yanzu ta fada, ko kuma ta ki ni, bata kila London be fahimce ni ba ne, shiyasa ya rubuta abun da ya rubuta, amman ni miye ribata idan na rabaki da dank? Idan baki gode min a tsawon shekarun nan ba, toh be kamata ki tuhume ni da wani abun ba" Ta juya gurin Vito. "Ka gafarce ni, ina saka kaina aikin da ba nawa ba, amman ni ina tayaka yaki ne kawai, tun da ka kawo ni a gidan matsayin yar aiki, ma lura kuma duk wanda ya kalli yadda kake nunawa Emily gata ya san kana sonta, hakan yana min dadi, ina sha'awar mace ta samu kulawa a gurin wanda take so kamar uba ko miji ko dan'uwa, domin ni nawa uban be dauke ni a matsayin ya ba, na kan fada maka Emily ta kula wani ne saboda taya ka yakin da baka san ranar cin nasararsa ba, na kan zauna na yi tunani yadda ka yi ma Emily gata ita da yaranta ka nuna mata so da kauna fiye da kowa a duniyar nan, amman ko na rana daya bata taba duba wannan ba, har takan bawa wasu mazan damarda za su iya sonta, bayan kuma kai ka cancanci zama a zuciyarta, na kan fada maka ne saboda ayi ma tukkar hanci, amman son da kake yi ma Emily ya hanaka fahimtata, a yanzu kuma kuna zargina da abun da ban aikata ba, kar idonka ya rufe, ka tsaya ka yi tunani gudun yanke hukunci a ciki fushi domin komai daren dadewa sai ka fahimci dalili kuma ka yi nadamar abun da zaka yi min a yanzu, London ba shi da lafiya ba mamaki lokacin da ya rubuta hakan ba a cikin hayyacinsw yake ba" Duk wani yanayi da muryar da Chidimma ta san zata iya amfani da ita ta siye zuciyar Vito daga yi mata hukunci a cikin fushi sai da ta yi, kuma ta yi nasara domin kuzarinsa na son yanke mata hukunci mai tsauri ya karaya, maganganunta suka shige shi. Emily ta turata ta karfi. "Are you saying all this saboda kina son Vito? Ko kuma saboda ki kawar da laifin da kika aikata?" "Ban aikata ba, idan ma na aikata har kake kokarin kawar da laifin shim bancanci ki taya ni ba? Tsawon shekara biyar da na yi ina kula da yaranki ban cancanci godiya ba? Ko kuma dai ke haka halinki yake? Butulu ce ke? Shiyasa shi kansa Oga Vito kika duba halaccinsa ki kaunace shi ko da na kwana daya ne? Ya so ki kamar zai mutu, ya so yayanki kamar nasa, ko matar governor ba zata nuna miki gata ba, amman duk baki gani ba, ni kuma na bauta miki babu dare ba rana, ni nake kula da yaranki, ni nake girka musu abinci na gyara gidan, na karanta musu storybook ko wane dare, idan ba su da Lafiya ni da ke muke jinyarsu, ki kaddara ma na aikata abun da London ya rubuta shin ban cancanci yafiya ba?" Cikin daga muryar da ya fi kama da tsawa take maganar tana nuna kanta sai kuka take sosai. Emily ta kai hannu zata mareta Vito yayi karaf ya rike, Emily ta kalleshi da sauri tana mamaki. "She's right, shekara biyar ba kwana biyar ba ne, ta bauta miki, ni kuma na so ki fiye da komai da kowa a duniyar nan, ita baki gode mata ba, ni kuma baki ba ni abun da nake so ba, akanki na kusa haukacewa, akanki bana ji bana gani na kyautata miki iyakar kyautatawa, na baki gatan da babu wanda ya taba baki, a tsawon lokacin nan bana son bacin ranki, ban taba cilasta miki kwanciya guri daya dake ba jira nake har sai kin amince da kanki, fada min bayan ni ba zai iya miki? Babu mahaifiyata bata fada min ba akanki amman ban saurareta ba, babu iya cin fuskar da yarki Lisa bata min amman na daure saboda ina sonki, na kashe kudi mai yawa akan maganin danki, Emily ni na inganta rayuwar ki kika zama abun da kika zama a yau, a haka duk ban cancanci tukuicin so ba? Amman a kwana daya ko biyu kin hadu da wani a gurin aikinki kin soma ba shi fuska da kofar da zai so ki" "You take her site?" "Yes saboda gaskiya ta fada, abu ne da ya kamata na gane tuntuni, shiyasa yanzu kika tsane ta ai, kike son a kareta what if you make all of this?" Ya fisge takardar hannunta ya yaga. "Enough is Enough Emily, I'm tired, kuma a yanzu na gane duk abun da ya faru da ke, kin cancanci haka, domin ke ma butulu ce, kin butulcewa addininki, kin butulcewa mutanen da suka dauki a matsayin a suka yi nufin baki gata, shiyasa ke ma kika hadu da tasgon rayuwa, yanzu kuma kina son butulce min bayan duk abun da na yi miki" Kallonsa kawai Emily take hawaye na sauko mata. Chidimma ta zube kasan guiwoyinta ta hadu hannayenta. "Ranar yau ta kasance bakar rana a gurina, domin wannan ce rana ta farko da na ga tsakani tsakaninka da Emily, dan Allah ka gafarce ni bana nufin shiga tsakaninku, ni na aje aiki na bar aikin daga yau" Vito ya saka hannayensa ya dago ta tsaye. "Baki yi laifin komai ba, kuma ba zaki bar aiki ba, amman zan kaiki gidanku ki huta har sai ta gane muhimmamcinki" Yana fadar hakan ya kama hannun Chidimma ya nufi kofar fita falo, Emily na tsaye tana kallonsu har suka fice, sai ta lumshe ido tana jin wani abu mai nauyi yana mata yawo a cikin zuciya, duk abun da Vito yayi mata a yanzu, ko wanda zai mata a gaba ta cancanci haka ko fiye da hakan ma, domin ya sama mata komai ya mata gata amnan zuciyarta ta kasa bata hadin kai gurin mallaka masa abun da yake muradi, ta mari kanta ta sake marin kanta ta sake marin kanta har sau uku sannan ta bude ido hawaye na mata zuba ta hada takardar da VITO ya yaga ta kwashe ta juya ta fara haurawa stairs din idonta na rufewa saboda hawayen da take. Dakinta ta shiga ta kwanta kan gadon ta lumshe ido tana miada numfashi. Bata dago ba sai da wayarta ta yi kara alamar shigowar sako, sannan ta bude ido ta daga kan ta kai hannu ta dauko wayarta ta duba sakon da Aliyu ya turo mata. "Barka da safiya, fatar kina lafiya" Ta girgiza kai alamar no bata lafiya, amman bata iya amsa masa kuma ba zata iya fada ba. Ta koma ta kwanta tana aika masa da sako bayan ta yanke shawarar abun da take ganin kamar shi ya fi a gurinta, domin ganin take rayuwata bata da wani sauran amfani a yanzu, ita kanta ta gaji da shiga gararin rayuwa daga wannan sai wacan, idan Vito ya watsar da ita a gurin wa zata koma yanzu kuma? Bayan shi me sake faruwa da ita.. "Na san na hadu da kai akan kaddara like accident, amman zuciyata ta aminta da kai, idan har bayan rayuwa ta ji cewar Turhan zai iya kula da Fatima, kuma zaka rika dubata toh ka ba shi ita" Sakon na shiga wayarsa ya kirata sai ta ki ta daga, hakan ya saka shi aiko mata da sakon karta ya umarce ce data bude whatsapp dinta. Ta bude WhatsApp din ta shiga chat dinta da Aliyu hotunan Fatima ta fara cin karo da su, sai kuma short Video da yayi mata, gaba daya tana cikin farinciki ne da nishadi. "Emily kin yanke shawarar kashe kanki ne? Kin manta da farinciki Fatima? Wannan farinciki kike son ta rasa? Bayan kin san yadda rayuwa take da wahala ga mutunen da ba shi da uwa a kusa? Ashe ke na jaruma ba ce? Kin ce zaki canja ina canjin yake? Ashe ba zaki iya ba? Akwai abun da yake faruwa ne? Ki fada za mu iya maganin abun a tare, Amman dai ki sani Fatima ta yi kankanta da rasa mahaifiya, ya kamata ki girmama farincikinta fiye da naki" Shi ne rubutun da ya biyo bayan sakon. Sai kuma ga Voice din Fatima cikin murna. "Momy ina jindadin zama a nan, Momy ki bar ni na kara kwana, ke ma ki zo kin ji Momy hahaha" Ta shafa screen din wayar tana kallon Fatima da murmushin da ya fi kuka ciwo. Sannan ta rubuta masa amsa. "Bana nufin kashe kaina" "Akwai abun da ya faru ne? Ina son na ganki mu yi magana" Sanin kanta ne idan ya ga duka a jiki zai iya cewa zai shiga fada da Vito, a yadda Vito yake fusace a yanzu komai zai iya faruwa, dan haka ta haramtawa kanta ganinsa har ma ta bukaci kar ya kawo mata Fatima a yanzu sai nan da kwana biyu. "Aa ba yanzu ba, idan babu damuwa babu takura Fatima zata iya kara biyu a gurinka? Ka yi hakuri na saka ka ba tare da neman izini ba, ban san ko zai kawo rashin fahimta a tsakaninka da Matarka ba" "Aa, zata iya zama har na zuwa lokacin da kike so, amman ina jin kamar akwai abun da kike boye min shiyasa baki son na ganki ko?" "Babu, kawai ina son ta yi enjoying zama da kai, wannan farinciki data rasa na uba ta ji shi a tare da kai ko na kwana biyu ne" "Toh zan iya kiranki Video Call?" "Aa Vito yana yawan zama gidana a kwana biyun nan bana son na samu matsala da shi ko da kai, zan jidadi idan baka takura dole sai ka gan ni ba" "Okay na fahimta, zan jira har sai kin samu natsuwa sai
Chapter 87 · 0% Book details