← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 177

Sashe 159

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 7 TALIYAR HAUSA YAR MURJI Abinci na gargajiya, ano na musamman, jin da in iyali! Idan kina/kanason abinci mai ano na musamman wanda zai tunatar da kai da in gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al ada ce mai ha a iyali, auna da jin da i a teburin gida. Me yasa za ka za i Taliyar Hausa Yar Murji? An yi ta da tsafta da inganci Ta dace da kowanne irin miya: miya mai wai, miya taushe, ko miya mai Sau in dafawa cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa Lafiyayye, mai sau in narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman Muna a Kaduna amma anonmu ya zarce iyaka! Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). Idan kana son jin da in abinci na gida wanda ke ha a zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa Yar Murji yau! wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. Ka more anon gargajiya mai tsafta, mai da i, mai orewa! _________ Karfe 4:30pm aka daura auren Aliyu da Aisha, bayan sauke sallah farilla ta La'asar. Daddy da yan'uwansa suna gurin, yan'uwan Ummi ma wasu daga ciki suna gurin. Dr A-B ne ya bada auren Daddy da kansa ya karbawa dansa auren Emily, masu shaidu suka shaida aka yi addu'a sannan masu tafiya suka tafi, Daddy da Dr A-B suka nufo cikin gidan da ragowar goro da dabino. Daddy ya nufi bangarensa Dr A-B kuma ya shiga falon Ummi ya tambaya ina Aliyu yake. "Baya gidan, amman yanzu zan kira shi ya zo" "Emily fa?" "Tana sama, Nafeesa tashi ki kai shi" Ummi ta umarce ta, Nafeesa ta mike tsaye ta wuce gaba Dr A-B na bayanta har suka shiga cikin dakin da Emily take zaune tare da Mama Baraka. Nafeesa ta juya ta fice, Dr A-B ya zauna kusa da Emily sai ta dube shi idonta a kumbure ta yi kuka sosai har ta gode Allah. "An daura aurenki da wanda kike so yau, ina miki addu'ar Allah ya ba ku zaman lafiya, kuma ya saka mutuwa ce za ta raba" Ta kara matsawa kusa da shi ta rumgume shi tana jin sanyi. "Na gode, wannan karo na farko da jinina ya bada aurena..." Ta furta murya na rawa tana kuka, ita kadai ta san me take ji, tana son Aliyu kuma tana tsaron abun da gaba zata haifar, gashi ta watsa kasa a idon manyan mutane babu wanda ya fahimce ta, shi kansa Dr A-B ganin take yayi mata abun da take so ne kawai ba dan ya gamsu da zabinta ba. Ta dago kanta amman ta kasa kallon kowa. "Allah ya ba ku zama lafiya" Cewar Mama Baraka tana share hawayenta. Sun kusa rabin awa a dakin har aka fara kiran Dr A-B saboda Alhaji Bulama zai bar gari kuma tare za su tafi. Ya mike tsaye kenan sai ga Aliyu ya turo kofar dakin ya shigo da sallama duk suka amsa masa ban da Emily da kanta yake kasa, tana ta lissafin rayuwa. Idan Aliyu ya juya mata baya shi kan ita kam ta gama rayuwa kuma makiya za su mata dariya. Dr A-B ya kama hannun Emily ya mikar da ita tsaye ya kama hannunta ya kama hannun Aliyu ya saka hannunta cikin na Aliyu. "Ga amana an baka, ta wahala ka sani, muna fatan daga kanka ta dace, a gaban iyayenmu ta zabe ka ta bar wanda shi ya so ya aureta a yau, dan Allah karka bata kunya. Sannan zan tunatar maka a yanzu Emily tana da uwa, dan'uwa da kuma uban da zata sani nan gaba kadan, karka kuskura ka ce zaka taba ta. Ta fada kai take so kuma na tsaya har yanzu ne saboda na tabbatar da cikar burinta, na sauke nawa nauyin, ni zan tafi ina muku addu'ar Allah ya baku zaman lafiya na bar ku lafiya" Ya dauke hannunsa daga kan na su ya nufi kofa ya fice daga dakin, Mama Baraka ta mike tsaye ta bi bayansa. Aliyu ya kama hannaye Emily duka biyu ya rike yana kallon yadda take hawaye. "Na san nisar tafiyar da kika yi, a hanya kin taka kaya, kin tsallake rame, kin yi dingishi kin karaya, na san zafin wutar data kona ki, na san buri da mafarkinki, ka karanci zuciyarki na san kudurinki, kin yi rayuwar kadaici. A yau ni da ke mun zama iyali, zan zame miki mijin da baki taba tsammanin samu ba, zan cika duniyarki da farinciki har sai kin manta da damuwarki, kuka ya kare hawaye, ba zaki sake zubar da hawaye akan a namiji ba, fargaba ba zata sake kusantarki ba, kin zama jinina, farincikina, kaunarki ce rayuwarta, ina mai tabbatar miki baki yi kuskuren zabe ba" Ya sake hannunta ya matsa baya kadan ya zube kasan guiwoyinsa ya hade hayyansa. "Na gode da kika yarda da cewar zan iya! Na gode da kika ba ni wannan damar, na gode da kika yarda a dora min wannan nauyin na gode da kika yarda na zama silar warakar duk wani ciwo naki, na gode da kika so ni, na gode da kika aminta da ni, na gode da kika aure ni, na gode Saruniyar mata, mace mai hakuri da kyakkyawar zuciya, na gode Ayusher na gode... Na gode... Na gode na gode..." Ta kasa komai wasu hawaye na dabam suna sauko mata, sai ta lumshe ido tana maida numfashi. Aliyu ya mike tsaye ya matsa daf da ita har yana jin fitar numfashinta. "Bude idonki ki kalli mijinki, mijin da be san komai sai aunarki, mijin da samunki ya zama babbar kyauta da rahama a gareshi" Ta bude idon ta kalleshi ido cikin ido daf da daf gab da gab das da das... "Ayusher ina aunarki, ke tawa ce ni ne ABOKIN RAYUWARKI" Ya rada mata cikin wata murya da be san yana da ita ba, furucin yana fitowa ne har can kasan kasan kogon zuciyarsa. Ya kai bakinsa ya sumbanci goshinta. Sannan ya ware hannayenta. "Ina tsarin Allah daga shedan la'ananen, duk wani abun kin, ko na cutarwa da zai shiga tsakanina dake, ina neman tsari Allah daga duk wani abun da zai saka na bata miki rai, kuma ina rokon duk wani alheri da zai kara mana zaman lafiya da kaunarnan junanmu, ina neman rahamar Allah a duk inda za mu saka gaba, ina neman rahama daga Ubangijin da shi ya hada mu, ya kawo mu a nan kuma ya nuna mana wannan ranar mai muhimmanci a rayuwarmu, Allah na gode da wannan kyauta da ka yi mini, da sunan Allah mai rahama mai jinkai" Ya rumgumeta halal hug ya saka a kirjinsa, wani irin rumguma yayi mata sosai kamar za a kwace masa ita, ya yi squeezing dinta har sai da abayar dake jikinta ta dage, yayi sama da ita kafafuwanta suka dage. Emily ta yi shiru..... Hawayen suka yanke mata, numfashinta na fita a hankali yana shiga da kamsh in turaren jikin mijinta, ba a taba rumgumarta ta ji damuwarta da fargaba sun gushe mata ba sai a yau. Babu wanda ya taba rumgumarta ta ji hankalinta ya kwanta ya samu sukuni ba irin Aliyu. Yanzu ta san me ta rasa, sai a yanzu ta san what truly halal hug means, ka so a so ka so na hakika dabam yake, auren wanda yake kaunarka kaunar ta gaskiya ta hakika a dabam take, son wanda yake sonka so na hakika dabam yake, lallai akwai wata irin rahama da farinciki, jindadi da cikar buri a auren soyayya. Ranar yau kadai ya nuna mata tana da muhimmanci, wunin yau kadai ya shafe duk wani fargaba da take, ta share duk wata damuwa da ta fuskanta. Lallai macen da miji yake so Sarauniya ce, a yau Aliyu ya furta mata kalaman da babu wanda ya taba yi mata su a ranar aurenta, shi da kanshi yake gode mata, a yau ta shaida soyayyar gaskiya marar algussu. Aliyu be kalleta a matsayin mace da ta taba aure biyu ba, be kalleta a matsayin ta haihuwa biyu ba, ya kalleta a matsayin macen da yake so, lallai mai son be ganin ramarka, a yau ta dandanin miye auren so da masoyin gaskiya. "Meyasa ban hadu da kai ba tuntuni?" Ta tambaya tana murza kanta a kirjinsa kamar zata tsaga kirjinsa ta shige cikin zuciyarsa. Sai ya bata amsa cikin rada shi ma idonsa a lumshe cike da kwalla, auren soyayya suka yi da Kameela amman ko ita bata nuna masa kaunar haka a ranar aurensu ba kamar Emily. "Ita ce tambayar da na dade ina yi ma kaddara, miyasa bata hada ni da ke, tun farkon da ta bude miki shafi" "Aliyu ina aunarka" Ya bude ido ya sauketa ya rika fuskarta yana kallon cikin kwayar idonta. "Duk wata kauna ta furuci ko ta aiki, ko wanda take zaune a zukanta masoya, Ayusher na fi kauna, kaunarki, na fi numfashinki son kasancewa da ke, ni da ke ABOKAN RAYUWA ne, sai da mutuwa" Ta yi sauke wani sanyayen numfashi ya lumshe ido tana murmushi. Madalla da kasancewarka cikin rayuwata, ka zamo min tauraro mai haske. Madallah da ABOKIN RAYUWA irinka" Ya kai goshinsa ya hade da nata, hancinsa a saman nata, ya saka yatsunsa na dama cikin nata, na hagu ma haka suka tsarkafe yan yatsunsu cikin juna. "Abokiyar tafiyata, har tsawon rayuwa, Madalla da ABOKIYAR RAYUWA irinki" Sun dade a haka sannan ya sake ta ya matsa baya. Ta kalleshi tana murmushi a yau ta san yadda rumgumar masoyi take mantar da damuwa, ya sameta tana kuka ya maye mata gurbin hakan da murmushi. "Idan akwai abun da kike son aikatawa, ni halalinki ne just do it" Ta taka one step forward kamar ya san manufarta sai ya maida hannayensa baya ya duko da fuskansa ta sumbanci gefen fuskansa da sauri, ta juya baya tana jin kunya. Murmushin dake fuskarsa ya fadada har ya bayyana hakoransa. Ya nufi kofar fita har ya kusa isa sai kuma ya yanke tafiyar ya juyo ya dawo gurin masoyiyyarsa ya rumgumeta ta baya, sai kuma ya juyo da ita, da
Chapter 159 · 0% Book details