Sashe 138
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 6 Suna sauka Airport Aliyu ya kira wayar direba ya sanar masa. Kamin ya iso Aliyu ya nuna Emily gurin zama. "Zauna a can yanzu zai zo ya dauke mu" Ta kalli gurin ta fara takawa ta isa ta zauna, sai ya shiga ciki ya siyo mata ruwa ya kawo mata da dan abun tabawa ba, ruwan kawai ta karba ta rike bata kallon sai Mama Barakat data kasa hada ido da Emily. "Daure ki sha ruwa kuma ki share hawayenki" Ta fara share hawayen sai ya kar i ruwan ya bude mata ya mika mata ta karba ta sha kadan, ta mika masa. "Thank you" Ya fada da murmushi sai ta dube shi, wai shi yake mata godiya saboda ta karbi ruwa ta sha kuma ta share hawayenta. "Ina kike son tafiya? Gurin Ummi ko gurin Mama Barakat? Tana son ki zauna kusa da ita" "Ban taba samun abun da nake so ba, duk abun da kuka zaba min yayi" "Inda ina raye abun da kike so shi zaki samu Emily, dan haka zaki bi mu zuwa gurin Ummi hakan yayi?" Ta daga mishi kai tana ta kallonshi kamar yau ta fara ganinsa. Ya kai goran ruwan dake hannunsa bakinsa ya sha har lokacin kallonsa Emily take bata ko motsa ido, daya sha ya sauke gorar sai ya sska yatsansa cikin ruwan ya cire ya tsarka mata dogon ruwan a fuska yana murmushi, daman shi yana daga tsaye ne tana zaune, sai ta lumshe ido tana murmushi. Hakan ya ba shi damar kallon fuskarta ya koreta ta kallo har ya gano ramar da ta yi ta kara mata kyau ne madadin ragewa. Tana bude idon sai yayi hanzarin dauke kansa ya kawar da fuskarsa, a nan ita ma ta samu damar maida biki wato ta dasa masa nata idon tana kallonsa, sai dai ita ba kyaunsa kawai take kallo ba, duk kuwa da kasancewar yana da siffa mai kyau da kwarjini, sai dai ita a gurinta yanzu kyau bashi da value domin kyaun ta bi Khaleefa ya cutar da ita, haka kuma Turhan ma yana da kyau amman kyaun dan maciji, ita a gurin hali shi ne komai kuma zata iya fahimta a yanzu Aliyu yana da banbanci da sauran, sai dai bata san gaba ba. "Gashi ya zo tashi mu tafi" Ta mike tsaye tana kallonsa kamar babu wani abun kallo a gurin sai shi. Suka jera a tare suna tafiya har suka isa gurin motar ya bude mata baya ta shiga, Direban kuma ya dauki kayan ya saka a bayan mota Mama Barakat ma ta shiga baya Aliyu ya shiga gaba direban yaja motar suka fara tafiya. A harabar gidan direban ya faka Aliyu ya fara fita ta gefen daya fita Mama Barakat take sai ya bude mata kofa sannan ya zagayaya budewa Emily dake zaune tana jiran ya zo ya bude mata, ta kalleshi sannan ta fito ta ya rufe suka jera shi da ita suka shiga cikin falon da Ummi take tsaye tana jiran isowarta. "Maraba Maraba da yata, yar dake guduwa ta bar yarta" Ummi ta rumgume Emily cike da farinciki, sannan ta kama hannunta suka zauna Aliyu ma ya zauna haka Mama Barakat. Direban ya shigo da manyan akwatunan Emily sai Ummi ta kalli mai aikinta ta ce. "Kulu a dauki kayan nan a shigar da su dakina, daga yau dakina Emily zata zauna" "Dakinki kuma Ummi" Aliyu ya tambaya da mamaki. Ummi ta ce "Eh dakin uwa ai na yarta ne, ba zan sake yin wannan saken da na yi ba kika gudu kika barmu, kika daga mana hankali na fi son kina kusa da ni ina jin motsinki, idan muka tashi komawa Abuja ma dake zan tattara mu tafi, idan ma kin zabi sake buguwa ki fada sai na hada kayana mu tafi kin ga neman zai fi dadi" Aliyu yayi murmushi Emily ma ta yi murmushi tana kallon Ummi. "Ba zan sake guduwa ba" "Zamu gani dai, amman ni dai ba zan sake bari ki gudu ba" Ummi ta tabe baki tana yi ma Aliyu kallon zolaya. Emily ta kalli Aliyu suka sakar ma junansu murmushi mai laushi da sanyaya zuciya sannan ta sauke kanta kasa, Aliyu kuma suna hada ido da Ummi ya ga irin kallon da take masa sai ya girgiza mata kai alamar ba abun da take tunani ba ne domin ya san hasashenta, ya mike tsaye yana murmushi mai sauti. "Bari naje na yi sallah" Ya fice daga falon, Ummi ta kalli Mama Barakat. "Ki shigo dakin kasa sai ki yi sallah ko" "Dare yayi Hajiya zan tafi gida dai, gobe sai na dawo" "Toh ba matsala direba yana waje sai ya sauke ki gida" Mama Barakat ta mike tsaye. "Mu kwana lafiya Hajiya na gode" Bayan Ummi ta amsa mata ta juya ta fara tafiya kamar daga sama ta ji muryar Emily. "Sai da safe" Ta juyo jiki a sanyaye ta kalli Emily. "Na yi tunanin ba zaki amsa ni ba ne, shiyasa ban miki sallama ba, ki gafarce ni" "Zuciyata ta saba da karbar ko wane kalar sako na bakinciki, kaddara ta sunnanta min haka, shiyasa na fahimci rayuwar da nake ciki, ni ce nake son mutane ba wai mutane ne suke so na ba, kuma na yarda zan cigaba da rayuwa a haka" Mama Barakat ta fashe da kuka. "Wallahi ba haka ba ne, karki yi zaton bana kaunarki, ina sonki fiye da tunaninki" Ummi ta kwantar da Emily dake kuka a fadarta sai ta yi ma Mama Barakat alama ta tafi da hannu. Mama Barakat ta fice tana kuka. "Toh miye amfanin kuka? Abun da ya wuce ai ya wuce, ni uwa ce a gareki Emily, kuma ki daina wannan tunanin na cewa babu mai sonki, da kin san tashin hankalin da muka shiga ni da Aliyu da mai gidana na rashinki sai kin tausaya mana" Ummi ta dagata daga kan kafadarta. "Muje ciki ki yi wanka ki ci abinci ki huta na baki labarin yadda aka yi muka gano ki, ko Aliyu ya fada miki?" Ta girgiza yau. "Yauwa aikuwa ni zan baki wannan labarin, daman duk ya bi ya ishe ni komai ya tattare baya barin ma wani ya shiga balle ya kyautata miki, shiyasa ma ya fara ba ni haushi sai ka ce shi kadai yake da ke" Cikin yanayin rarrashi da son faranta rai Ummi take maganar da Emily kamar mai magana da yar yarinya karama sa'ar Fatima. Ummi ta rika ta ta kwantaa fadarta ta rike hannayenta suka fara haurawa sama. "Kudi ya zuba can gurin Office din kamfanin sadarwa, bayan mahaifinsa ya saka baki aka duba wayoyin da kika kira, aka ga layina da na Aliyu da kuma na wannan likitan, aka ce wunin ranar da su kawai kika yi waya, Aliyu na jin haka ya ce duk yadda aka yi kina gurin Dr, ya fara bibiyar layin, amman da yake likitan nan baya son mu da alheri da Aliyu ya tura masa sako be ba shi amsa ba, muka rika sama da kasa sai da muka hada da Hajiya Baraka ta sama mana Information din mahaifiyarsa Aliyu ya dage, amman ni nake taya shi da addu'a fa dan kar ki yi zaton kamar ban yi komai ba, ke daga karshe sai da mahaifinsa ya shiga kuma ita ma Hajiya Barakat ta yi magana da roko da komai aka samu ta amsa mana tace su zo wannan satin Aliyu ya saka date suka tafi, kamar a mafarki sai na ga sun dawo min da ke, na ma yi zaton za ku tsaya ku kwana Abuja, ashe ya damu da halin da nake ciki sai ga shi be tsaya kwana ba ya dawo" Emily tana kwance kafadar Ummi tana bata labarin har suka shiga dakin. "Kin ji yadda aka yi, amman fa mum shiga tashin hankali sosai, ba dan ni ba dan Allah Emily karki sake guduwa ko minene kamata yayi ace kin tsaya kin fuskance shi ba wai ki gudu ba" "Na rasa ya zan yi ne, abubuwan suka hade min ko'ina ba dadi" "Har da gidana? Ko kadan ni fa ban bi bayan Hajiya Barakat ba dama ta ba ni labarin abubuwan da suka faru ke na fi tausayawa, to kin ga ni miye nawa da zaki dora min laifi?" Emily ta dago da sauri. "Ban dora miki laifi ba, ko kadan baki min komai ba" "To miye na duguwa ki bar gidan? Na yi tunanin ko ba zaki iya zama ko'ina ba zaki zauna a gurina, har tambayar kaina nake wai ko dai na miki ba daidai ba?" "Baki min komai ba, kuma ba zan sake guduwa ba" "Alhamdulillah Allah yasa haka" Ummi ta rumgume har ga Allah Ummi tana jin tausayin Emily sosai. Bayan Emily ta yi wanka ta canja tufafi sai ta dauki abaya ta dora saman kananan kayan da suke jikinta domin suturta jikinta, na ci abinci ta kwanta kan gado, babu jimawa Nafeesa ta shigo kiranta wai Ummi ta ce ta sauko kasa idan ba bachi take ba. Babu musu ta fito a dakin na Ummi ta sauko kasa tana jin kamar ta samu gata a yanzu ko da yake bata san me gobe zata haifar ba, amman dukanin wani kulawa da uwa zata nunawa yarta Ummi ta nuna mata a yanzu. Ta sauko a hankali ta karaso ganin kowa yana zaune kasa sai ta zauna ita ma, kusa da Aliyu sosai a gurinta ita ba komai ba ne dan jikinta ya taba na wani wanda ba Muharraminta ba, a addinin data samu kanta ciki hakan ba laifi ba ne, kuma ta saba. A kokarin Aliyu na bin umarni Allah sai ya matsa kadan dan kar jikinsa na taba nata, domin ya san ita din ba halalinsa ba ce. "Muna ta fira muna shan tsamiyar dila baki kusa na ce a kira ki sauka mana cikin dangi, amman na fada mata idan bachi kike ta barki ki huta" "Ba bachi nake ba" "To ga abun da muke ci idan zaki iya ci, saka hannunki ki dauka sai an balle ake ci" Ummi ta fada, kamin ta saka hannunta sai Aliyu ya dauki karamin plate ya aje gabata ya zuba mata wanda ya banbanra. "Sha ki ji ko