← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 177

Sashe 48

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

an daina wannan dabi'ar ta kauye, sai na fada mata mijina ne be aminta ba yanzu ma ba da saninsa na zo ba. Ta auna ni bayan na fada mata abun da nake ji tace naje na yi hoto a yau din na kawo mata, na je na yi hoton wa inda aka fada min na biya 1200 a lokacin na dawo Allah yasa na same ta da ta duba sai ta fada min abun da ke ciki jirkice yake madadin kan yaro ya juyo ta gurin marata sai ya zama kafafuwansa ne a nan. "Hakan yana da wata matsala ne?" Na tambaya domin ban san kan abun ba. "Sosai kuwa mace zata iya mutuwa ko ta kasa haihuwa sai an fasa ta, ko kuma ta samu matsala ko danta ya samu, za a iya rasata ko a rasa dan, gashi kuma baki da jini sosai ba ki da ruwan jiki da yawa baki cin abinci mai kyau" A take hankalina ya tashi, zancen abinci mai kyau kam bata taso ba domin abinci ma bana iya ci na koshi balle wani mai kyau ko mai gina jiki. "Za mu dora ki akan magani, kuma kije ki shirya ki dawo gobe, akwai abun da zamu fara miki da juyo da kan yaronki kamin ki cika wata tara, dan yanzu cikinki yana da wata bakwai da kwana sha takwas" Na mata godiya na fito jikin a sanyaye domin na san babu wani kudi da zan samu a gurin Khaleefa, ashe ma abun da ban sani ba gidan yana nan ya kusa kamawa da wuta saboda na fita tun safe ban dawo ba har la'asar. Dan canjin da na rage min ne na hau achaba da shi na iso gida sai da na fara biyawa na fadawa Malika halin da nake ciki ina kuka sannan na shigo gidan. "Idan uban wa kika fito?" Ita ce madadin amsa sallamata da yayi kasancewar yana cikin dakin na yi sallama. "Asibiti" Na amsa jiki ba kwari murya na fita daker. "Ina kika samu kudin zuwa asibiti? Da izinin wa kika fita" "Idan na tambaya ba zaka bar ni ba, kudin kuma daman ina da shi" "Karya kike sai dai idan satar min kika yi ko kuma kin fara bakin halinku na kafirai, wato yanzu ya kai ki fara fita baki fada min ba" Na kalleshi cike da takaici da nadama da bakinciki na ce. "Wai kai Hamza wane irin zuciya ce a kirjinka? A matsayinka na musulmi mai addini be kamata na same ka haka ba, dabi'unka da ka nuna min ba su na tarar ba, ka zalince ni kai da iyayenka kunci amanata" Ban gama rufe baki ba ya rufe ni da duka. "Me kika sani akan addini da zaki tsoma baki a ciki? Kafira diyar kafirai? Bubabbiya marar alkibila, rashin kunyarki ya kai ki kira da Hamza gatsatsa ko? Irinki ma son haihuwa ake da ke? Mugun iri irin kafirci wadanda basa tuban Allah da ma'aiki, na haihu da ke kije gaba ki maida yarana kafirai" Ban taba sanin rashin imanin Khaleefa ya kai haka ba sai ranar, baya ji baya gani duka yake ina tare cikina yana kai masa halbi da kafarsa, Matar nan da ta taimaka min da kudin tafiya asibiti Maman Luratu ita ce ta shigo tana ba shi hakuri tana jansa sannan fa sauran suka shigo suna jansa suna fadin ban kyauta ba amman dai yayi hakuri ko dan cikin dake jikina. "Na gaji da ke na gaji da halinki kowa ya san ba haka na tsara rayuwar aureba amman ji yadda kika maida gidana, Aisha na sake" Maman Luratu ta yi hanzarin rike shi. "Abun he kai can ba Hamza ka yi hakuri ga ciki kuma ta tafi ina?" "Ta tafi duk inda zata tafi, ba gaji da halinta bata da tarbiya" Nasan ma'anar saki a musulunci kamar yadda na san ma'anar aure, wato ya barranta kansa daga gareni, ni din nan na haramta a garesa, sanin ba ni da gurin zuwa ba ni da kowa ya saka ni ba shi hakuri ina rokon mutanen gidan su ba shi hakuri na zauna. Sai suka ce na bari sai ya huce na zauna a gidan idan ya huce zai maida ni. Na san yadda suke kina sai zuciyata ta raya min kamar abu ne mai wahala su saka ya maida aurena. Dan haka na tashi cikin daren nan na tafi gidan mai gari na fada masa halin da ake ciki, ashe fita ma matsala domin har an kira an fada masa, mai garin ya aiko kiransa ya zo take a gurin kamin a mana umarni da komai ya ce. "Da zu na sake ki ne da nufin saki daya, toh yanzu na kara miki na sake ki saki uku babu aure tsakanina da ke har abada" Na rude na kama kafafuwansa na rike ina kuka ina rokon gafara, ban wayi addinin sosai ba saboda haka ban san idan an yi saki uku aure ya kare ba kenan. "Khaleefa ka san ba ni da kowa ba ni da komai dan Allah karka min haka, Alkawari be ce haka ba, ka yafe min Wallahi ba zan sake ba" Ni kam rokonsa kawai nake ina son ya maida sai da matar mai garin tace min ai auren ya kare kanan babu zancen gyara. Na yi tunanin ko mai garin zai ce na zauna a gidansa har sai na haihu, daman iyayensa kam ban saka ran za su ba ni gurin zama ba. Ina dawowa gidan na ji na zaba bukatar kowa a tare da ni sai na shiga dakin na dauki can chanjina da fitila da number da Maman Luratu ta ba ni na fice ba tare na dauki komai daga suturar da na samu a gidan ba. Na karasa inda yake zaune a kofar dakin mahaifiyarsa sai duk idon yan gidan ya koma kaina wata kila suna tunanin ko zan rokeshi gafara ne ko kuma ya bar ni na zauna a gidan ne, na tsaya a tsaya ina kallonsa ido cikin ido na ce. "Ka ci amanata Khaleefa, ka yaudare ni, ba ni da kowa ba ni da komai wannan tabbas haka ne, saboda kai na zo gidan nan kuma yanzu aure ya kare zan tafi, ka sani na rayu kamin na hadu da ni, na rayu babu uwa babu uba, babu daya daga cikin danging uwa ko uba, yanzu ma zan rayu domin mai rayawa ya kashe be manta da ni ba, Hamza na barka da Ubangijin da ya aiko Annabinsa da Addinin Musulunci, na barka da Ubangijin da be kwana be haifa ba ba a haife shi ba, Hamza na barka da ALLAH... " Mikewa yayi tsaye yana kallona baki a sake, matan gidan kuma kowa yayi tsit kamar babu abu mai rai a gidan. Bayan wannan wata kalar bata sake fitowa daga baki ba har na doshi kofar fita gidan na fice, ban yi nisa ba na ji ana kirana Maman Luratu ce ya biyo ni tana kuka. "Aisha ina zaki" "Koma ina ne zan tafi Wallahi yau ba zan kwana a gidan nan ba" "Toh Allah ya miki mafita, dan Allah idan kin samu waya ki kira ni, Allah ya sauke ki lafiya, ungo ga dubu biyar ki rike" Ina karba kudin na fashe da kuka sai ta rumgume ni tana kuka, na dago godiya ma kasa yi mata na yi na kama hanya, achaba na fara hawa ya kai ni tashar garin, ina zuwa kuwa na samu mota sanin kudin ba zai ishe ni na je Lagos ba na hau motar Kaduna, idan ma naje Lagos din gurin waje zan je? Matar da na yi butulci? Ko gidan marayun da ba lallai su karbe ni ba zan koma? Lokacin da na hau motar ba zai wuce karfe goma ba kasancewar garin da kowane lokaci ka je ana samu direba saboda akwai masu cin kasuwa, kuma ranar da abun ya faru ranar kasuwa ce. A ranar ban kwana a garin ba da cikina da ciwon da nake ji da kuma bakincikin dake kumshe a zuciyata na kwana a tashar Kaduna... Follow my channel domin samun update https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 And don't forget to SHARE [5/6, 8:51 PM] : https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 ABOKIN RAYUWA
Chapter 48 · 0% Book details