← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 177

Sashe 15

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

wata kila akwai sirrinki da yan'uwanki da be kamata na ji ba ko na sani, akan hakan ina baki hakuri, wani sako ya shigo ta sama kuma na bude na gani, wata kila saboda na samu damar tunatarki me Allah ya nuna min sakon Kana ta jan sakon da tsaye please minene? Ya aje numfashi a hankali. Na ga wani chat da kike da kawarki Huda, ban san iya aminci ko yardar dake tsakaninku ba, amman Aisha ban jidadin yadda kike fada mata sirrin shimfidarmu ba, ko a musulunci babu kyau, kuma maganganun ne da basu dace ba Ta dan wara ido tana murmushin da ya kusa zame mata dariya. Haba dai, wannan fa duk zancenmu ne na mata, kuma ita da ba ganinka take ba ma Ko dai minene tun da kika ga musulunci ya hana be kamata ki aikata ba, akwai illa ciki? Fadin amfanin me zai mata? Shikenan kin bude mata cikinki ta san sirrinki ta san sirrin mijinki, yadda muke mu'alama da komai ta sani, ban jidadi ba kuma in miki daukar mace mai hankali ne mai sani ya kamata, ban yi tsammanin zan ga haka ba, kuma ban jidadi ba Ya karasa da dan fada domin ya fahimci kamar bata dauki abun a wani abun ba, ganin haka ya saka jikinta yayi sanyi, shi kuma be sake ce mata komai ba ya tashi ya fice daga dakin. Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta dauki wayar felling guilty ta bude chat din tana dubawa tare da mayar da amsar tambayar da Huda take mata, kamin da kara da. Ke yau ya duba wayata ya ga chat dinmu Sannan ta kashe data ta gyara kwanciyarta da kyau, domin abu ne da ta sani idan suka samu tsabani shi yake bata hakuri, shi yake nemanta. Ba dabi'arsa bace bawa miji hakuri idan ta yi laifi, haka kuma ba mace ce mai saurin karbar laifinta ba, idan ma har ta aminta tana da laifin kenan. And to her hira da kawa ko a group chat da mata yan'uwa Normal ne domun suna suna fadar yadda suke tasu mu'alamar kuma dukansu mata ne babu maza, bugu da kari tana ganin aminci da jindadi ke saka irin wannan chat din. Bayan duk wannan ma why zai dauki wayarta ya shiga chat dinta da kawarta ko kawayenta har ya ga abun da suke tattaunawa, a ganinta a nan kam shi yake da laifi, kuma dai chat irin wannan tsakanin mata ai ba wani abu ba ne, dan haka bata shirya ba shi hakuri a yanzu ba. Yadda ta ayyana haka ne ya faru domin bayan ta yi bachi ya dawo dakin ta kwanta a kusa da ita, daman can no matter how suka samu tsabani baya taba raba gado da matarsa balle kuma har ta kai ga ya raba daki. Yayi bachi not like usual yadda ya saba, domin yana son ya nuna mata illar abun da ta yi, dan haka be shirya abun karyawa ko ya jira ta shirya masa ba yayi wanka ya yi shirin office ya fice daga gidan at early morning. [4/20, 9:58 AM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 15 · 0% Book details