← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 177

Sashe 66

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

abun da ya tsaya mata a makoshi. "Amman dawowa zai yi ne da ya ce ta zo ta girka masa abinci?" "Yana nan daman, na boye miki ne saboda ki zo" Tasmia ta ji yan hanjinta sun ka a ta mike tsaye da sauri gumi na karto mata, bata ko tsaya yi ma Emily sallama ba ta rumgumi jakarta ta nufi kofar falon ta bude Emily na mata magana bata kulata ba, da sassarfa ta isa gate tana samun ficewa sai ta ranta a na kare ta aina da gudu tana yi tana waiwaye har sai da ta yi nisa da gidan sannan hankalinta ya kwanta. Emily ta dauki shawarar Tasmia na cewar kar ra koma aiki, duk kuwa da irin kyautatawa Aliyu zato da take, amman zai iya amfani da damar ya dawo da Turhan a rayuwarta ita kuwa a yanzu bata bukatar kowa, sai dai ta dayan bangaren ta san taba bukatar aikin haka ta kwana da tunanin yi ko bari har garin Allah ya waye bata samu matsaya ba. Bayan Fatima ta wuce school, Emily ta shirya ta sauko rike da jakarta da wayarta, kallo daya ta yi ma Vito dake zaune yana karyawa ta dauke ido ta nufi kofa. "Zaki je neman aiki ne? Har shaguna nawa zaki rika bi kina neman su dauke ki aikin da ke kanki zaki iya daukarsu? Idan har baki son kudi da nake aje miki ne toh a shagon siyar da talkami da kika nemi aiki ne, shi ma nawa ne, kudin dai still daga karkashina za su fito" Ta juyo ta kalleshi ta dauke ido ta yi ficewarta. Da gaske gurin nasa ne ko kuma dai ya san mai gurin wata kila kuma yana mata barazana ne kawai saboda ya daureta a guri daya, har ta isa gurin aikin na su Aliyu bata daina tunanin maganar Vito da kuma Tasmia ba, ta duk inda zata auna Vito ya cancanci zama da ita, kuma sakamakon da zata masa na mallaka masa zuciyarta ne da yake bukata kamar yadda Tasmia ta fada, wata kila zata iya shawo kan Fatima ta amince da shi. Ta shiga gurin da ake aje motocin kamfanin tana duba motarta domin ta manta gurin da ta faka ta a wacan karon. Sai da ta yi rabin gurin sannan ta ga motarta ta matsa key din hannunta ta bude motar a gurin da zata zauna ta yi arba da wata farar takardar dauke ta rubutu, hannu ta kai ta dauki takardar sannan ta shiga ta zauna. "Idan kin riske sakon nan, ki shiga office dinki ki yi signing cewar kin bar aikin a hukumance kamar yadda kika karba a hukunce" Ta daga kai ta kalli harabar sannan ta aje takardar ta fito motar ta rufe ta nufi cikin ma'aikatar, bata sha wahala gurin haura sama ba domin ba wannan ne zuwanta na farko ba, ta shiga Elevator har hawa na 4 ta fita ta doshi hanyar da office dinta yake, kallo daya ta yi ma kofar office din Amal ta dauke kai ta murda office din da yake zaman nata a da ta shiga. Ga mamakinta sai ta sami Aliyu tsaye a gaban teburinta yana saka two cube of sugar a tea dake kan teburinta. "Babu gaisuwa?" Ya fada ba tare da ya kalleta ba. "Ina kwana" "Lafiya kalau" Ya saka Tea spoon ya motsa tea. "Zauna" Babu musu ta nufi kujera dake facing din gefen teburin ta zauna, ya dauki tea din ya aje a gabanta. "Na san baki karya ba, dauki ki sha" Nan ma kasa musa masa ta yi, sai ta saka hannu biyu ta dauki cup din ta kai baki ta fara sha. "Sai kawai kika ji kira daga sama ko? Ana zaginki?" Ta sauke tea din ta rike a hannunta. "Ki yi hakuri laifina ne, ya kamata na fada miki waye ni tun farko, ko da yake baki bukaci jin haka ba" Ta dora idonta akan ragowar tea din dake hannunta. "Amman kamin wannan fada min miye aikin Vito?" Ta kalleshi da kyawawan idanuwanta ta sauke kai kasa, ba tare da ta amsa masa ba, domin ba zata iya tonawa Vito asiri agurin kowa ba. "Dialer ne na Drugs?" Ta sake dubansa. "Ba fashi yake ba, da boyo zai rika yi ke ma ya boye ki, ba zai iya shiga ciki mutane kamar yadda yake yi a yanzu ba, kuma ba matsafi ba ne da yanzu ya bada ke ko kuma ya mallake ki sai yadda yayi da ke, idan kuwa baya duka biyun nan to yana siyar da kwaya, shiyasa yake samun mahaukanta kudi ko? Kuma shiyasa ya mallaki bindiga ta hanyar da be dace ba, saboda shirin ko ta kwana, domin ya san a tsakaninsu ma suna iya samun matsala da junansu, kin san sana'ar da yake ba sana'a ce mai kyau ba, shiyasa kike kokarin gina kanki kina son ki bar karkashinsa? Siyar da kwana ya kara masa karfi sosai da mutane ko? Da kuma jami'an tsaro shiyasa yake yadda ya ga gama? Kuma yana sha shiyasa bakinsa yake baki idonsa yake da ja kuma yake saurin fusata idan kika masa laifi sai kwakwalwarsa ta nuna masa dukanki ne kawai mafita" Kallonsa kawai Emily take tana mamakin yadda yake cankar abubuwa line by line a daidai. "Na zo nan ne saboda mu yi maganar Vito?" "Aa kin zo nan ne saboda mu yi maganar ki da kuma tawa" Ya zauna. "Mutane za su yi mamaki idan suka tarar da ni a office dinki, na sakan shiga office kowa na so karbar abu ko hannatawa da kaina idan bana bukatar wani ya shiga tsakani, amman ban taba zama office din kowa ba sai Emily" Ya duba agogo hannunsa. "Da farko zan fara da baki hakurin abubuwan da suka faru, matata bata fahimce ki kuma tana da zafin kishi" Yayi shiru na wasu dakiku sannan ya cigaba. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [5/22, 7:54 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 66 · 0% Book details