← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 177

Sashe 50

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a lokacin, amman akwai wani abu da Allah yake sakawa a zuciyar wanda ya so da shirya, na musulumta saboda Khaleefa da aurensa ban san cewar ina son addinin ba sai a lokacin, sai kawai na ji raina ya bace akan me za su ce na koma addinin da bana samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali irin na ruhu sai da na bar shi, ni dai a lokacin na san ina son musulunci dan haka sai na ki yarda, na fada musu ni taimako kawai nake nema ba wai ina nufin barin addinin ba ne, su kuma suka ce ba za su taimaka min ba haka na taso na fito" Ina jin kamar shi kadai ne wani hukunci da na taba yankewa kuma ban yi nadama ba, da kafa na dawo saboda ba ni da kudin da zan hau abun hawa na dawo, sai kuma na sha wahala a hanya saboda ni ba har gari bace hanya da mai achaba ya bi da ni na bi ina tafiya, idan na rikice sai na tambaya mutane da sannu har na kawo kaina unguwar da nake zaune. Na iso ban isha'i sai na samu guri na zauna ina ta jin ciwon cikin da ban gane nakuda ce ba, daker na iya roko ruwa na yi rama sallolin da ban samu yi ba, na kwanta a gurin azabar ciwo cikin bata karu ba sai da dare ya raba. Na koma gurin da nake kwana na kwanta da ji abun ba zai daina ba na taso na fito na dawo gidan matar nan na kwankwasa mata gida sai jikanta ya bude yana haska ni da fitila. "Dan Allah matar gidan nan nake nema" "Lafiya wacece" "Ni ce" Na leka sai ta ga fuskata. "Dan Allah ki taimaka min da ruwa na sha, kuma idan kina sa wani magani dan Allah ki taimaka min na sha, kar na mutu ciwon ciki nake da na mara" "Ba ni da magani amman dai zan baki ruwa ki sha" Ta shiga ta dauko min ruwa na karba da hannu biyu na sha na juya na koma shagon na zauna ina ta kuka domin ciwon ya matsa min ga kuma abu ina ji a kasana kamar zai fito, ban san lokacin da na fara ihu ina rike teburin mai shayin dake gurin ba, sai matse kafa nake ina juyawa, tsabar bala'i da azabar da ciwo har wani juri nake ji ina jin kamar ba a duniya nake ba, ashe haihuwa tana da zafi ban sani ba sai a ranar, gashi babu kowa a kusa da ni, duk zafin nan na haihuwa a haka iyayena suka wofintar da ni? Ina cikin tsananin nakudar dana na farko dan wata bakwai matar da ta taimaka min da ruwa ta iso gurin ta dafa ni, ta haska ni da fitila ina jin jikanta na fadar Gwaggo kika sani ko jikin shege ne. Sai tace. "Ko cikin shege ne ai ba za a kyaleta ba Kabiru rayuwa ce" Ta bude kadata ta haska sai ta saka salati. "Haihuwa ce zaki yi kuma kafa nake gani ba kai ba subhanallahi" Ta rika ni, da taimakon danta suka kai ni gidanta, ita tayi ta fada min yadda zan yi tana taimaka min tana danna min ciki har na haihu, amman na ji azabar da ban taba ji ba, har na ji kamar babu kasana gaba daya a lokacin. Da zanenta ta lullube dana ta yanke min cibi na sake wata nakudar sannan wani abu ya fado wai shi uwa, ta saka a leda ta kulle. Ta dauko wani zane ta lullube ni ta dora min dana a kusa da ni, ni dai ina kwance a gurin bana bachi bana farin ciki haka kuma bana kishiyarsa, hawayena kawai masu zafi suke sulalowa a idona, har ta yi zaton ko na mutu ta girgiza ni sai na kalleta. "Sannu" Na daga mata kai, da safe sai jikina yayi tsami sosai, ta taimaka min da tsumma na tare jini ta gyara dakinta tace na wanke kayan jinina haka na daure da ciwon jiki na da kasa na wanke kayana da kaina na zauna ina jin kamar fata ce kawai ta rage min a jiki, ta kawo min dumame na ci na sha ruwa sannan ta tambayi labari. Na fada mata komai sai ta tausaya min amman ta fada min ba zata iya ba ni gurin zama ba saboda zargi. Kuma ban ga laifinta ba tana da gaskiya ba kowa zai iya rike ni ba, dawainiyar ma ai sai ta yi masa yawa. Ta fada min idan mace ta haihu a musulunci akan yanka mata rago idan yayi kwana bakwai, kuma uba yana yi ma dansa huduba a kunne, amman ni daya be samu ko daya ba, hakan ya saka ni kuka sosai. A lokacin na saka masa suna Ibraheem ba dan na san ma'anar sunan ba, kawai dai na saka masa haka ne. Da dare yayi matar bata bari na kwana a nan ba saboda kukan da London yake ba ji rarrashi ga shi kuma nono na babu komai a ciki, na kwana a ashagon mai shayi kamin lokacin tashina yayi sai ga mutane na gani har hudu ciki har da mai shagon da abun dukansu, suka ce an fada musu a nan nake kwana kar na sake kwana a gurin su yanka ni, dayan ya so ya mare ni wai dan na raina musu wayo wato har haihuwa na yi a gurin. A daren suka kore ni na goya daya da zanen matar na kama hanya ina ta tafiya har gari ya fara haske gashi ko'ina na bi sai an kalleni saboda kukan da London yake domin ba lafiyayyen ana na haifa ba, gashi dan tsito ba shi da girma, ni kaina tafiyar ma daker nake yi ina ta raba kafa saboda zabar da nake ji a kasana. A haka na rika raba manyan gidaje ina yin Bara wani gidan masu gadi basa bari na karasa ba suke korata wasu kuma basa ma bude gate din. Har na fada gidan wata mata mai farar zuciya mai tausayi mai jinkai, da alama da saba taimakon domin na tarar da gate din gidan a bude kuma da na fadawa mai gadin taimako nake nema sai yace min na wuce ciki. Na shiga sai na zauna daga bakin kofar falon ina jiran fitowarta, na dade a gurin sannan aka bude kofar falon, wata matashiyar yarinya ce ta bude kofar ganina kamar tana mamaki ta tambaye ni lafiya. Nace mata taimako nake nema sai ta tambaye ni wane iri na furta abinci domin shi na fi bukata a lokaci, yarinyar ta juya ta shiga ciki bata jima ba ta fito da plate din shimkafa irin wanda aka ci aka rage tace ba a gama shirya mana abun karyawa ba amman ga ragowar shimkafar jiya idan zaki iya ce. Na karba jiki na rawa na fara ci hannu baka hannu kwarya kamin na kwance dana dake ta ihu ga wani zafi da jikinsa yayi na rumgume shi na gyara zama na fara saka masa shimkafar a baki tana kaiwa makoshinsa sai ya dauke numfashi... ***. ***. ***. ***. Ta aje zaren zancen tana neman nata numfashin dake kokarin daukewa saboda kuka na tuna rayuwar da ta dade da rufe shafinta. Aliyu ya matsa baya yana kallonta cikin tashin hankali, a lokacin ne ta fara zaga office din tana neman numfashinta kamar zata mutu, da sauri ya fita Office din ya fadawa Nick ya nema masa wata mace da take kusa ya dawo ya nufi fridge dinsa ta dauko ruwa ya nufeta hankali a tashe, wata mace ce ta shigo dakin tana sanye da suit. "Rikata dan Allah zaunar da ita ki rumgume ta" Ya nuna mata Emily a take ta nufi Emily ta aikata abun da ya fada sai ya miko mata ruwa yace ta bata. Matar ta karba ta kai mata ruwan a baki Emily na shan ruwan ta fara amai babu kakkautawa bata tsaya ba sai da ta amayar da komai na cikinta, matar na rike da ita har ta fara dawowa hayyacinta sai dai kuma jiki babu kwari. "Shiga da ita ciki ki wanke mata baki" "Okay Sir" Matar ta rika Emily suka shiga bathroom dinsa dake office din ta taimaka mata ta wanke baki da fuskarta sannan suka fito, Aliyu ya mikawa Emily Tissue da hannunsa. "I'm sorry" Ta karba kawai tana kallonsa da idonta da suka kumbura fuskarta da hancinta suka yi ja. "Anna ki rikota ku fito ku same ni gurin mota" Ya fice yana fadawa Nick ya sa a gyara masa office dinsa. Anna din ta taimaka mata suka sauka kasa suka isa har gurin motar da Aliyu take ya bude backseat Anna ta shigar da Emily ta rufe sannan ya shiga gaba yaja motar suka fice. Madubin gaban motar ya saita saitin da Emily take jingine da motar tana hawaye kana ganinta kasan tana cikin bakin ciki da rashin kuzari. "Kina da likitan da yake dubaku?" Bata amsa masa ba tana ta kallon gefen titi ta yi samo kamar ba ita ba. Shi kuma be fasa kallonta ba har ya isa bakin gate din gidan yayi horn mai gadin ya leko ya kalleshi... Sai ya sauke gilashin ta gefen da Emily take. "Ba sai ka shiga ciki ba" Ta bude motar ta fito da kafafuwanta ta yi tsaye kamar zata fadi, Aliyu ma ya bude ya fito ya zagayo inda take. Tasmia dake zaune a can gefe cikin mota ta bude motar ta fito da mamakinta tana kallonsu, tun kamin ta kawo Emily ta mika mata hannu domin jin take kamar zata fadi, Tasmia ta karaso da sauri ta rikata, ta kalli Aliyu. "Me ya same ta? Wani abun ka yi mata" "Eh fyade na yi mata" Ta amsa mata da gatse, sannan ya rufe gefen da Emily take tsaye ya zagaya ya shiga motarsa yayi reverse. Tasmia ta bishi da kallo mamaki domin ta gane waye shi. Emily ta dafata suka shiga cikin gidan ta zaunar da ita falonta. "Emily kin san wannan mutumen da ya kawo ki ne?" Emily ta kalleta hawaye na sauko mata. "Dan Allah karki tambaye ni komai a yanzu, ki tafi gida ki bari sai gobe zamu yi magana"
Chapter 50 · 0% Book details