Sashe 85
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... FOLLOW ME ON FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3 ALIYU POV. Ya dan ji wani iri shi dai aganinsa babu abun burgewa namiji ya tare da matar da a daura musu aure ba a gida daya da sunan budurwarsa ko wadda zai aura, hakan sai ya saka ya ji addinin musulunci ya kara burge shi domin addinin Musulunci be yarda da wannan ba, a ta dayan bangaren kuma yana tambayar kansa anyaba shi da zunubi na aje mata ya a nan a can kuma ya bata damar shakatawa da yi yadda take so da mutumen da ba muharraminta ba? Ya kalli Fatima dake ta ciye ciyen kayan dadinta hankali kwance. "Fatima mu tafi gida haka nan?" A take ta bata fuska. "No bana so mu tafi yanzu" Ya mike tsaye ya nufi Kitchen, ruwa ya dauko ya sha ya dawo falon ya zauna. "Kai ma baka da kowa kamar Momy na?" Ya dubeta. "Waya ce miki bata da kowa?" "Bata da kowa sai ni kadai" "Sai Vito" Ta girgiza masa kai. "Aa i hate him" "Why do you hate him? Me kake miki ne?" "Baya dariya, kuma yana da fada yana duka, kuma ba ya bari kowa ya zo gurinmu" "Toh mamanki tana da ni yanzu" "Yeehhhhhh" Sai yayi murmushi ya shafa kanta, sai ya ji duk ta burge shi. "Mun zama mu uku ko?" "Yes, zaka zama Babana? Ni kadai ce ba ni da Baba a duniyar nan kowa yana da Baba amman kace zaka maida sunana Fatima Aliyu amman baka yi ba, har yanxu ana kirana Fatima Aisha Emily...." "Ke ma kina da mahaifi Fatima, kuma na san da zai ganki zai kaunace ki sosai zaki ji dadi, da ace mahaifiyarki zata aje abun da ke zuciyarta ta dubi maslaharki da kin yi farinciki sosai, kina da uba sunanshi Turhan" Ta dafa shi, hakan ya farfado da shi daga guntun tunanin da yake. "Ka ji" Ya lumshe ya bude sannan ya daga taya matsa da ita saman jikinsa ya rumgume ta, ba dan ya ji abun da take tambayarsa ba sai dan tausayinta da ya kama shi. Kiran Emily be shigo wayarsa ba sai kusan Isha'i a lokacin da yayi alwala yana warwarar hannun rigarsa Fatima ta shigo masa da wayar da ya bari a falo, har dakin da yake ta mika masa. Ya karba ya kara a kunne, for the first time sai ya ji nauyi fara yi mata sallama. "Salam alaikum" Ta masa sallamar sai yayi murmushi ba tare da ya amsa ba ya ce. "Yau dai kina da nuna min hallayarki na kwarai ashe kin iya sallama" "Na iya mana, ni da na zauna da musulmai kuma Hausawa" "Kina lafiya Emily?" Ya tambaya, sai ta lumshe ido hawaye na sauko mata, ta girgiza kai kamar yana gabanta tana jin kamar ta fada masa ba lafiya ba, amman tana gudun abun da zai je ya dawo. "Anyways na kira wayarki a kashe, saboda hankali na be kwanta ba da yanayin da na barki, kuma da na ji wayar kashe na damu sai na saka Tasmia ta bincika min ke" Da ya kai iya nan sai ya yanke maganar saboda yana son ya gano idan Tasmia gaskiya ta fada masa ko akasin haka. Emily ta hade kukanta ba tare data bude ido ba ta ce. "Me tace maka?" "Me kika ce tace min?" "Ban fada mata komai ba, bata ma min maganarka ba" "Okay, ta fada min ta same ki kin yi ado kina yi ma Vito girki, nace toh ina nan na damu ita kuma tana can tana girki ma wanda ba mijinta ba, Allah yasa dai kar na samu zunubi" Ta cige baki hawaye na sauko mata kana ta bude ta sauke numfashi a hankali. "Ado tun wanda ka tarar na yi ne, ban sake wani ado ba, ina Fatima tana tare da kai" Ya kalli Fatima dake cin apple. "Yeah, amman Aisha na tambaye ki mana" "Uhmmm, ku haka addininku ya yardar ku zauna da mutane musamman namiji kuna tarayya ko daba muharraminku ba ne...? Mu a gurinmu hakan ba abu ne mai kyau ba" "Ban taba tarayya da Vito ba, wani abu be taba shiga tsakaninmu ba, a tsawon zaman da muka yi, yana jiran sai na aminta da soyayyarsa ne, ni kuma zuciyarta ta kasa fahimtarsa, wannan abun yana wahalar da rayuwata yana jefani a matsala, ni ban taba mu'amala da kowa ba sai Khaleepa da Turhan, shi ma Turhan ya fada min kan kuskure ne, kuma bakar rana ta biyu a gurinsa bayan ranar da aka daura mana aure, yana daga cikin dalilin da ya saka nake son gina rayuwata ni kadai ina son na zama mai ikon kaina" Jin cewar bata taba zina ba ya burge shi, haka kuma jin cewa Turhan ya kira ranar da ya aure da bakar rana a gurinsa ya saka shi kara dora ayar tambaya akan zamantakewar aurensu. "Fahimta, I'm sorry for misunderstanding you" "Dan Allah ka bar Fatima ta kwana a gurinka, gobe sai a kawota" "Okay" Ta bukataci hakan ne gudun kar ya zo kawo Fatima ya hadu da Vito ko kuma ya ga dukan da Vito yayi mata yace zai dauki mataki ya jefa kansa a matsala. Falo Fatima ta koma tana kallo, shi kuma ya tsaya a dakin yayi sallah, be dago daga sujudarsa ta karshe ba sai da yayi ma Emily addu'a, bayan ya gama ya sauko falon ya umarce tayi alwala ta yi sallah, ba musu ta tashi zuwa jnda ta yi alwalar magariba ta yi ta dawo falon ta dauki hijab din Kameela daya dauko mata a dazun ta saka ta fara sallah, shi kuma ya shiga Kitchen ya fara gyara tattasai da attarugu da albarba ya kunna gas ya dora nama akai, ya fara yanka vegetables, sai ga Fatima ta shigo Kitchen tana tambayar me yake yi. "Jallof zan girka kina ci?" "Ka iya girki?" "Sosai ma" Ita ta yi ta taya shi hira yana girkin, duk abun da ya zuba sai ya daga ta ta gani da ya gaji sai ya goyata a bayansa ta leko kanta ta saman wuyansa tana kallon yadda yake girki, idan yayi abun da bata saba gani ba sai tace masa ba a haka ake yi ba, shi dai dariya kawai yake ya cigaba, da ya gama hada komai sai ya koma tare da ita falon suka zauna sai da ya nuna sannan ya koma ya zubo musu a plate daya shi da ita. "Kai kadai zaka ci?" "Aa ni da ke" "A plate daya" "eh ko baki cin abinci a plate daya da wani?" Ta yi dariyar jindadi "A gida raba mana ake kowa plate dinsa dabam, amman ina so" Ya zauna ya sake komawa ya dauko ruwa da lemu, sannan yace ta zo su ci, madadin ta zauna a gefensa ko gabansa sai ta tsallake abinci ta zauna a kan ciyarsa, yana ganin haka sai ya aje Spoon daya ya dauki dayan yana ciyar da ita da shi shi ma sai ya ci, ko loma nawa yayi sai ta kirga tun be hankara ba har ya fara dariya, ita da shi suka ci abinci cikin nishadi, har wayarsa ya dauko yayi mata hoto yayi mata video, kusan a lokacin ne ya ji yana matukar kaunar samun nasa yaran, Fatima kuma ta yi enjoying moment din tana jinsa kamar mahaifinta. Bayan sun gama ya bude quran app din wayarsa ya tana karanta dan abun da ta iya yana mata gyara, har bachi ya dauke ta, daukar ta yayi ya haura da ita sama ya kwantar da ita kan gadonsa ya lullubeta ya zauna gafen gadon ya karanta mata addu'a ya tofa mata sai ta bude ido ta kalleshi. "Meyasa kake watsa min yawu" "Addu'a ce ta tsari idan aka karanta ma yara ko suka karanta babu abun da zai same su har safe, Momy ki bata miki idan zaki kwanga bachi?" "Aa" "Toh ki koya ki rika yi ma kanki kin ji?" Ta taso daga kwance da take ta rumgume shi. "Da nan nake zaune tare da momy da mun rika jindadi, kowa yana son ace yana da ba Baba, momy ta maka girma amman zamu iya zama yayanka mu duka biyu" Yayi murmushi ya shafa bayanta a haka ta sake yin bachi sai ya kwantar da ita ya fito falon, ya dauki wayarsa ya kira Mama Baraka, sai dai bata daga kiran nasa ba har ya yanke, aje wayar yayi a tunaninsa ta yi bachi domin tara da rabi har ta gota, yana dauke hannunsa daga mazaunin wayar sai ga kiranta ya biyo baya, sai ya sake dauka ya amsa, tare da sallama ta amsa masa suka gaisa sannan ta tambaye shi. "Aliyu me yake faruwa tsakaninka da matarka?" "Mama Me ta fada muku" "Bata fada mana komai ba, an yi anyi da ita ta ki ta yi magana ba, sai kuka da damuwa abinci ma bata iya ci, gaba daya ta fita hayyacinta" Yayi shiru na dan lokaci tare da tunanin alfanu da kuma rashin sa da zai haifar idan har ya fadi dalilin da ya saka ya turata gida, ba dan Ummynsa ba da babu abun da zai hana ya fadawa kowa abun da ta yi masa ko dan ta shiga taitaiyinta ta hankalta. "Babu komai Mama" "Aa mu fa iyayene, babu komai zaka turo ta gida ko sakinta ka yi?" "Aa" "Toh me ke faruwa tsakaninku? Aliyu ita rayuwar aure sai da hakuri na san ka yi ne, amman ka kara, na san idan ba kai ba ne ba zaka iya zama da Kameela ba, sai dai bana son kana duba sherinta ka rika duba alherinta ko dan ku bawa marasa da kunya, kaga yanzu dawowar da ta yi nan iyayen sun nuna babu ruwansu da ita yan'uwa kuma sai dariya suke mata, dan Allah ina rokon alfarma Aliyu ba dan na isa ba, sai dan na san ka da biyayya da kawar da ido da kuma hakuri da tunani, dan Allah ka yi hakuri ka zo ko kuma ka aiko daukar maka matarka ka bata hakuri ka bawa iyayenta, ku shirya tsakaninku" Ya sauke ajiyar zuciya. "Shikenan zan yi tunani