← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 177

Sashe 20

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 9 EMILY POV. Suna isa gate Fatima ta fisge hannunta daga na Emily. Bana son tafiya gida yanzu An koreni a kamfanin ko baki gani ba? Asibiti zamu tafi yanzu Emily ta sake kama hannunta da karfi ta jata. Sai ta fisge tana daka mata tsawa. Bana son zuwa Ta nufi titi da gudu zata tsallaka ba tare da ta tsaya dubawa ba, Emily ta yi hanzarin bin bayanta, motar dake dafe da gudu ta taka burge domin kadan ya rage ta buge Fatima. Emily ta kamo Fatima ta riketa da karfi gabanta na dubawa, gilashin motar aka sauke wata matashiyar yarinya ta leko tana kallon Emily. Allah yasa ban taba ta ba Emily ta girgiza mata kai, ta matsa gefe, hakan be gamsar da matar ba har sai da ta faka motarta kusa da gurin da Emily take tsaye tare da Fatima ta bude motar ta fito. Kin tabbata bata ji ciwo ba? Ban kula ba ne, ina amsa waya Cewar matashiyar budurwar dake sanye da gown din atamfa sai fashion cap a kanta, tana jin babu dadi a tunanin kokarin amsa wayar da take a lokacin da take tukin motar ne ya haddasa matsalar. Ba laifinki ba ne, karki damu ita ta fisge hannunta a nawa zata gudu Matashiyar ta kalli Fatima dake ta huci kamar wani karamin zaki ta sake kallon Emily. Amman lafiya Haka take min, bata jin magana Emily na rufe baki Fatima da saka ihu tana son fisge hannunta a na mahaifiyarta. Ki kyale ni Momy ki sake min hannu, akwai ciwo ina son na tafi gida yanzu Matashiyar ta dan zaro ido tana kallon Fatima da mamaki, ganinta karamar yarinya amman da take yi ma mahaifiyarta ihu. Ya sunanta? Fatima Emily ta amsa mata idonta na cika da kwalla. Matashiyar ta rage tsayinta tana kallon Fatima. Sunana Tasmia, please Fatima ki daina yi ma mahaifiyarki rashin kunya da tsawa kin ji babu kyau, ba ayi ma iyaye tsawa da uwa da uba dukansu abun girmamawa ne A madadin Fatima ta amsa mata da OK sai ta fada mata abun da ba kowa ya kamata ya sani ba. Ni ba ni da uba haka nan aka haife ni babu uba, can you imagine? Matahsiyar ta kalli Emily sannan ta mike tsaye ta yi mata sallama. Allah ya tsare gaba bye Ta juya ta fara tafiya Emily ma ta fara takawa tana kokarin ganin hawayen dake idonta basu zubo ba. Can you take us home? Cewar Fatima tana kallon Tasmia da already ta bude motarta zata shiga. Yes darling ku shigo sai na sauke ku No mun gode zamu hau okada Ni ba zan hau okada ba ni mota nake son ta kai ni gida Ta fada a tsawa. Is okay Fatima ba sai kin yi tsawa ba, zan sauke ku, please ki shigo ko dan masalahar yarki Tasmia ta karasa tana kallon Emily, Emily bata da sauran tace bayan abun da yarta ta take so kuma ta zartar, dan haka ta nufi motar ta bude gidan baya suka shiga ita da Fatima, Tasmia ta shiga mazaunin direba ta ja motar. Ina zan sauke ku? Fatima ta fada mata unguwar da Number gidan, Emily kuma ta maida fuskarta gefen titi tana kallon ababen hawa, sai dai a badini, zuciyarta zafi take mata tunanin rayuwarta na baya ya dawo mata, damuwa ta baibaiye mata zuciya. Har suka isa unguwar Emily bata ce komai ba haka ma Tasmia Fatima ce kawai ke nuna inda za'a bi har suka isa kofar gidan. Bata jira komai ba ta bude motar ta fita ta rufe gambun da karfe ta doshi gate din gidan ta fara kwankwasawa. Emily ta bude dayan gefen ta sauke kafafuwanta. Mun gode, ki yi hakuri da abun da ta yi miki, haka take bata jin magana, yaran yanzu sai a hankali Haka ne amman yana da kyau mu rika tsawatar musu, idan har bata tsoronki ko ki hada da wanda take tsoro yayi mata hukunci ko yayi mata fada, kamar yayanki ko kanenki ko mijinki ko saurayinki, su yara wani lokacin sai da mai tsawatawa, amman fa ki yi hakuri na shiga abun da babu ruwana Tun da Tasmia take magana Emily ke jin wani abu na mata yawo a zuciya, har ya saka ta kasa rike hawayenta sai da suka zubo. Wata kila ke kina da duk abubuwan da kika lissafa saboda haka ba zaki gane komai ba, na gode sai anjima Ta share hawayen sannan ta karasa fita ta rufe mata motar a hankali. Tasmia bata wuce ba sai da Emily ta shiga gidan, sannan ta ja motarta. Emily na shiga falon ta jefar da jakarta a saman kujera ta zauna ta dafe kanta sai hawaye. Duk abun da nake kokarin yi a yanzu, ina yi ne saboda ku da kuma rayuwarku ta gaba, kin ce baki son zama a gidan nan baki son Vito, ina ta kokarin ganin na tsaya da kafafuwana saboda ku, yau kina kallon yadda aka koremu gurin aikin nan kuma mun kama hanyar gida kina min tsawa kina neman ki daga min hankali, dole sai kin fadawa kowa baki da uba? Fatima dake zaune a kujera rumgume da hannayenta ta kalleta tana turo baki gaba irin na fitsararun yara. Toh ai bani da uba, ba karya na yi ba Emily ta dago ta kalleta cikin bacin rai ta daka mata tsawa. Kar bakinki ya sake furta haka ga kowa, baki san zafina ba ne shiyasa kike fadar hakan, lokacin da nake kamar ke da ace na samu wata macen a matsayin uwa ko yaya take zan rike ta Toh miyasa baki da uwa? Ni ina ruwana da hakan? Ta fada tare da mike tsaye ta dauki remote dake gefenta ta jefar a kasa sannan ta nufi upstairs tana tafiya da karfi kamar wata babbar mace. Emily ta bita da kallo hawaye na sauko mata zuciyata na zafi sosai, ko da damba ne kake wahala da shi kake kokarin ganin ka faranta masa, idan ka fahimci ba kai ne a gabansa ba dole hakan zai maka zafi, balle kuma ace mutum ne, mutum ma yarka jininka. Ta girgiza kai ta share hawayenta ta mike tsaye nufi dakinta, keys din mota ta dauko ta sauko ta sake daukar jakarta ta fice daga falon. Tafi minti goma a motar zaune tana sauke ajiyar zuciya sannan ta murza key ta yi warming dinta ta juyar da ita mai gadin ya bude mata ta fice, restaurant din dake kusa da su ta fara biyawa ta yi takeaway sannan ta karasa asibitin da danta yake, dukanin abun da take tana kokarin ganin ta boye damuwarta ne, so take ta zama jajirtacciya, wannan dalilin ne ya saka take tare hawayenta a duk lokacin da suka so zuba. Ta shiga dakin da danta yake tana murmushi kamar babu damuwa a zuciyarta, Chidimma ta gaisheta ta amsa tana kallon danta daya dauke fuska alamar baya son ganinta. My Boy how are you Ya sake juyar da fuskar dayan gafen, bata damu ba ta aje takeaway dake hannunta ta juya gefen da fuskarsa take ta zauna tana masa murmushi sai ya sake juyar da fuska ya matsa gefe. Tun da ya tashi yake kiran sunanki Chidimma ta fada mata. Baki fada masa ina gurin aiki ba? Na fada masa, maybe yana son ganinki ne a lokacin be samu damar hakan ba, saboda baki kusa Emily ta sauke dogon numfashi sannan ta dawo gabansa ta tsuguna ta rike kunnuwanta, tana neman yafiyarsa kamar yadda ta saba yi idan ta bata masa rai. Okay I'm sorry, Momy ta bata maka rai ka yafe min I'm sorry No i hate you A take yanayinta da fuskarta suka sauya, ta kalli Chidimma ta sake kallonsa, sai dai wannan karon bata sake cewa komai ba ta mike tsaye tana jin zuciyarta kamar zata rufe, domin be taba furta mata kalmar i hate you ba sai a yau, ta fice daga dakin ta sake komawa cikin motarta ta zauna tana ta hade wani abu da ya tsaya mata a zuciya. Bata yarda ta yi kuka ba sai shafa fuskarta take tana kokarin kwantar ma da kanta hankali. Ta sake yi ma motar key ta fice daga asibitin tana tukin motar zuciyarta na kara yin nauyi har ta iso gida, ta faka motar a gun da ta dauke ta, sannan ta bude ta fito tana rike da jakarta har ta isa balcony din kofar falonta ta zauna a gurin ta sauko da kafafuwanta kan interlock tana kallon harabar gidan kamar wata bakuwa. A lokacin da wayarta ta fara ringing sai ta saka hannunta a jakar dake bude ta dauko wayar ta duba, V ne rubuce a jikin screen din. Ta amsa wayar ta kara a kunnenta ba tare da tace komai ba. How are you? Kamar jira take sai kawai ta fasa masa da kuka, kuka sosai mai dauke da ihu kai kace yayi mata bushara da mutuwa ne, har sai da mai gadin da mai sharan harabar gidan suka mike tsaye suna kallonta. Be sake furta komai ba ya kashe wayar, ita kuma ta cigaba da kuka da karfi har numfashinta na rawa tana shafa sarkar Cross din dake wuyanta. Da sauri Mai gadin ya karaso kusa da ita yana tambayar lafiya, bata amsa masa ba ta mike tsaye ta shige falonta a kan kujerar falon ta jefar da wayarta da jakar ta haura sama ta shiga dakinta ta kwanta saman gado tare da jan filo ta rumgume tana cigaba da kuka sai dai wannan karon babu kururuwa... VITO POV. Ya aje bottle din Hennessy XO dake hannunsa that's Worth 430k, ya gayen dake kusa da shi. A siya min ticket din tafiya ina Port Harcourt yanzu nan Okay Sir Ya jingina da kujerar da yake zaune gaba daya ransa ya bace jin kukan Emily da yayi, after like 10m gayen ya dawo ya sanar masa babu flight din da zai tashi daga Lagos to Port Harcourt yanzu sai gobe. Ya dago ya kalleshi. Ka fadawa manager Happy Home Hotel ya siya min ticket din tafiya Port Harcourt, a siye tickets din duka ina son tafiya yanzu nan Okay Sir Ya sake komawa ya kwanta jikin kujerar
Chapter 20 · 0% Book details