Sashe 23
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi ma dariyar yayi ya dauko mata wata sabuwar hira, sai da aka kira sallah la'asar suka daga falon, a shi ya nufi masallacin dake unguwarsu ita kuma ta gabatar da sallah ta a gida kamar yadda Annabi ya umarta. Misalin karfe biyar da mintuna 58 wayarsa ta yi kara alamar kira, a ka'ida idan yana kusa da matarsa baya taba waya saboda ya bata lokacinsa, sai idan kiran ya tsananta ko kuma ya kasance na gaggawa ne, sai dai jiran amsar Turhan ya saka shi mikewa tsaye ta nufi wayar ta dauka sai ya kira ne ta whatsapp kuma video call da wata bakuwar number da be san waye ba. Rejecting yayi ya bude whatsapp din ya duba bakuwar number sai yayi arba da hotunan Emily sun fi guda hansi, Hello Hi kuma ya fi ashirin, kamin ya samu damar reply wani kiran ya sake shigowa. And this time around baya son rejecting domin ya fahimci mai kira, gashi kuma ba zai iya amsawa a gaban matarsa ba, dan haka ya fice daga falon ya haura sama sai da ya shiga dakinsa sannan ya amsa kiran dake shigowa da zarar wani ya yanke. Hello... Fatima ta fada da karfi tana masa waving. Hi ya kike? A take murmushin fuskarta ya gushe ta bata fuska ta fara kukan da babu hawaye. Ba Lafiya ba, Vito yayi min fada sosai har yana cewa sai ya yanka ni, kuma Momy ma fushi take da ni bata so na, saboda na yi mata tsawa lokacin da muke tafiya a hanya dazun kuma, na je gurin titi har mota ta kusan bugeni, muka hadu da wata mata ita ma ta dinga min fada ta kai mu gida, amman ai ina fushi ne na yi, shi ne Vito ya dawo Momy ta fada masa sai yayi min fada, ni kuma na shigo daki na turo maka hotunan Momy ka duba ka gani ko kana sonta Daga idonsa har girarsa da bakinsa a bude suke, ya rasa ta ina zai kama zaren zancen ma, yadda ta aika masa rahonta ya saka ya manta labarin farko da na tsakiya, na karshen kawai ya rike wanda shi ya fi bashi dariya. Wato ya duba ya gani ko yana sonta, ita a tunaninta son mahaifiyarta yake. Me ya faru ma? Ya tambaya domin ya manta labarin nata, yadda ta zayyana masa dazun haka ta sake zayyana masa yanzu. Okay w ait now, yanzu dai me kika yi ma Momy Tsawa Fada Meyasa kika mata tsawa to? Baki san ba ayi ma iyaye tsawa ba? Babu kyau, ko a gurin wanda ba musulmai ba, balle kuma ke da kika fada min ke musulma ce, yana da ace kin fi kowa tarbiya Ai musulmai ba su da kirki haka Momy tace No ta yi ma musulmai mummunar fahimta ne kawai, amman musulmai sun fi kowa kyan hali da tarbiya To miyasa wannan matar girlfriend dinka ta kore Momy? Why? She's not my girlfriend, kawai abokiyar aikina ce, abun da ta aikata ba abu ne mai kyau ba, amman musulmai ba haka suke ba, idan kina son na yi shiri dake to karki sake yi ma mahaifiyarki tsawa Amman ai bata sona Inji wa tana sonki mana, idan kika bata mata rai ni ma raina zai bace, kina son raina ya bace? Momynki ma ba zata jidadi ba idan kika bata min rai, dan haka ki daina bata mata rai kin ji Zan yi tunani akai Yayi murmushi. Okay, zan duba hotunan sai mu yi magana Okay, zan turo maka wasu ma idan ka gani sai ka goge komai kar Momy ta gani zan aje mata wayarta Ba zan iya gogewa ba, ai na nuna miki yadda zaki goge Na manta kawai na iya saka number ne, amman zan bawa Momy ta goge min Tana fadar hakan ta yanke kiran. Nooo nooo nooo nooo Ya fada yana girgiza kai, ya sake kiranta videos calls din amman bata daga ba, ya rasa ya zai yi sai ya zauna gefen gadonsa yana dafe goshi. Oh Allah matsalar yara kenan Ya hade yawu da karfi yana tunanin abun da zai sake yi ba, can wata zuciyar ta bashi shawarar sake kiranta sai ya sake kiran Number ta whatsapp as videos call kamar yadda suka yi da farko. Boom Emily ta amsa kiran ta bayyana gaban screen din wayarsa tana kallonsa da mamaki fuskarta kuma dauke ta hawaye. Shi ma kallonta yake zuciya na bugawa ciki na kukan rashin gaskiya. TURHAN POV. Fara ce sosai, tana da jan gashi da blue eyes amman tana da kima Gaskiya ba mu santa ba, babu mu da marayu masu wannan bayanin da ka bayyana Ba a yanzu ba ne, ta kwana biyu fa, ita kanta yarinyar ta zama babbar mace har da yara Gaskiya ba mu santa ba, amman zan bincika maka, idan na ga wani abu makamancin wanda ka fada zan nemeka sai ka bar mana information din Ya busar da iskar bakinsa ya kai hannunsa a kai, gaba daya ya gama zagaye gidajen marayu dake nan kusa be samu Aisha ba kuma ko'ina yaje cewa ake basu san wata mace mai wannan siffar ba. Kamar yadda suka bukata information din ya bar musu ta yadda idan an samu wani abu game da ita za a iya tuntubarsa. Sannan ya fito jiki a sanyaye ya shiga motar da suka shigo. Ya sauke ajiyar zuciya ya kai sau hudu sannan ya dago hannunsa ya duba wayarsa, babu wani sabon sako bayan wanda matarsa ta aiko masa sai kuma na Aliyu, ya kasa amsa ko daya daga na matar har na Aliyun saboda baya cikin yanayi mai dadi. Faruk ya tashi motar suka fara tafiya, sai a lokacin ya samu sukunin amsawa Aliyu tambayarsa, tare da dora masa da wani bayanin. Abun da Mommy take kokarin yi a yanzu zai iya haifar da matsalar da tafi ta baya, domin har yanzu bana son yarinyar nan, kawai ina nemanta ne saboda Ammy, wahalar neman nan nata da nake sha ya saka na kara tsanarta Ammy ta kasa gane banbanci... Be gama amsawa ba ya dago ya kalli Faruk dake kokarin fakawa gefen titi. Lafiya Toh gamu gani, tsohon nan ne yake ta min hannu Wane tsoho? Turhan ya kalli gefensa, mutumen da ya tarbe su ne a gidan marayun har yayi musu iso a gurin shugaban gidan. Faruk ya sauke gilashinsa. Lafiya? Lafiya dai ranka ya dade, kawai dai ina da bayani ne da zai taimaka maka akan neman yarinyar nan Turhan ya gyara zamansa da sauri yana leken tsohon da yayi jika da shi. Okay Sir muna jinka Tsohon ya kalli hanya gefe da gefe sannan ya sauka daga kan okada da yake ya sallami mai okadan sannan ya matsa kusa da su sosai yace. Ba zai yi na baku bayani akan hanya ba, saboda za a iya ganina a nan, hakan kuma zai iya haifar min da matsala Turhan ya bude motar ya fita ya bude masa gidan baya ya shiga ya zauna, sannan ya koma ya zauna ya juya yana fuskantarsa. Da yaren turanci tsohon ya fara magana yana hadawa da yarbancin kamar yadda yake da farko, daman kana kallonsa kaga bayarabe tsagen fuskarsa ma ya bayyana haka. Na ji lokacin da kake bayani akan matar da kake nema, ai ba a neman mutum haka a babban guri irin wannan, saboda ba mu da tabbacin abun da ka fada akanta haka din ko akasin haka Haka ne Turhan ya fada da sauri. Ba ni da tabbacin neman da kake mata, amman ina fatan ba zaka cutar da ita ba Babu cutarwa a ciki dan Allah idan kasan inda take ka fada mana Ban san inda take ba a yanzu, amman na san matar da ta dauke ta, akwai information din komai a file din gidan da nake, na san Emily farin sani domin na yi shekaru ina aiki a nan, na gane ta ne ta hanyar kamaninta daka fada amman sunanta Emily ne ba wacan sunan daka fada ba Acha Mun gode sosai, yanzu zaka iya kai mu gurin matar da ta dauketa din? Aa zan dai iya neman file din da addreshin matar yake sai na nuna muku ku tafi nemanta, amman a bisa sharadin guda uku Faruk ya kalli Turhan Turhan ma ya kalleshi suka hada ido sannan suka kalli tsohon. Miye sharadin Sai kun yi rantsuwa ba za ku cutar da ita ba, kuma ba za ku bayyana komai akaina ba cewar ni na baku wannan bayanin na yadda za a same ta, na ukun kuma za su biya kudin bayanin da na muku a yanzu, za ku biya kudi idan na kawo file haka ma idan kun tafi gidan matar za ku biya kudi ko da ba ku same ta ba, sannan kuma idan kun ga Emily komai tsawon lokaci za ku biya kudi Turhan yayi murmushi, kudi daman ba matsalarsa bace, ganin Aisha ne abun da yake buri a yanzu, wai hausawa suka ce bukatar maji hajji Sallah. ___________ Kuna ganin Aliyu zai fadawa Turhan ya san inda matarsa take? Anya da gaske tsohon nan yake ko kuma dai ya shiry cin kudinsu ne.? Ya kuke gane za a kare tsakanin Aliyu da Emily? Ga barawo ga mai kaya...! Kallon kallo akuya kallon kura... [4/20, 9:59 AM] : https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w ABOKIN RAYUWA