← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 177

Sashe 140

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 6 Na tashi a wani aramin gida a Beere, cikin unguwar da ruwa ke ta faman gudu daga bututun da babu mai kulawa da shi, cikin amo da hayaniyar kasuwa, da amshin ewedu da ata rodo na mahaifiyata. Baraka suke kirana iya ga wani tsohon malamin addinin. A cikin al'adun Yarbawa, mata suna da 'yancin yin kasuwanci, sana'a ko aiki tun da dadewa. Wannan ya bambanta da wasu al'ummomi da ke takaita mata ga aikin gida kawai. A yawancin biranen Yarbawa, musamman kamar Legas, Ibadan, da Abeokuta, za ki ga mata masu kasuwanci ko aiki a hukumomi. Iyayen Yarbawa suna koyar da 'ya'yansu mace da wuri cewa ta rike kanta Yana daga dabi'unsu su karantar da 'ya mace ta nemi ilimi ko sana'a domin ta rike kanta, ba tare da dogaro da namiji ba. Wannan ya sa da yawa daga cikin matan su ke da warin gwiwa wajen kokarin ciyar da kansu ko tallafa wa iyalansu. Na koyi juriya daga rayuwa, ba daga littafi ba. Na girma ina kallon mahaifiyata tana dafa abinci a kan itace, tana kula da gida kusan nauyin mu da na mahaifina a wuyanta yake, mahaifina ba shi da wani karfi kuma be damu da nema ba, ta kan ce min: Baraka, mace na da afa biyu aya tana goyon gida, aya tana neman arziki. Na shiga cikin harkar girki wato siyar da abinci, tun ina 15yrs mahaifiyata kuma tana fita shago siyar da kayan masarufi, a lokacin ban fara karatu a kolege ba, na iya hada tuwo da hannu, da kwasar romon miyar ogbono cikin harba guda. Na kammala karatu a wata college Ibadan, amma bayan na gama sai na gane cewa takarda ba ta nufin abinci a kwano. Domin bayan gamawa, ba aikin da ya biyo ba. Na zama kamar mutumin da ya ha iye ashi, ba zai hade wuce ba, kuma ba zai iya fitarwa ba. Na tattara kayan da ba su wuce buhu biyu ba, na tafi Lagos, wurin kanwar mamata, saboda gurin da nake siyar da abinci a da gonati ta kwace, mahaifiyata ta kuma shagonta yayi kasa, ga shi mu bakwai mahaifinmu ya haifa ba daya ko biyu ba, ni ce ta biyu idan ban tallafi mahaifiyar da ta tsaya akan ilimi da abincin na ba me zan yi? Na fara komai daga tushe. Na rika siyar da abinci a Mile 12, da jarin da mahaifiyata ta hada min, wata rana a siyar wata rana ba za a siyar ba, wani sa'in sai na roki kanwar Mamana ta ara min kudi nake samu na kulla wani jarin, gashi mijin aure ya gagareni a lokacin ko da yake ni kaina ban shirya auren ba domin ban tanadi komai na aure ba, haka mahaifiyata ma bata da wani abun aurar da ni a lokacin. Na ci gaba da girki har wani lokaci sai wani NGO ya fitar da talla, na neman ma'aikata, cika da takarduna na karatuna, ban sani ba ashe aikin ne silar wargewar rayuwarki, bayan wani lokaci. suka sanar min sunana ya fito. Na tafi gurin horarwa suka min interview bayan na yi nasara suka sake sanar min an dauke ni, farincikin be bar ni na kwana ba a ranar. Kusan zan iya cewa addu'ace ta ba ni nasara domin babban guri ne da shugaban gurin ya kasance bature jar fata mai tsakanin fari da jan gashi ga kuma blue eyes, kyakkyawa ne mai far'a da son bakar mace kamar ba jan kunne ba, na fara aikin a gurin a matsayin sakatariya ina kula da komai zuwa kan lokaci girmama kowa bawa komai hakkinsa. Sannu a hankali aka na saba da kowa a gurin ba iya ma'aikan gurin ba har da masu zuwa su fita. Daga gaisuwa da mutunci muka fara sabo da Rowan Alaric MacLeod wato shugaban gurin, a lokacin akan masa lakani da bello, domin farar fata idan suka tsallako kasashenmu sukan nemi suna su sakawa kansu saboda ku saje da mu kuma mu saki jiki da su. Bature ne da ya zo daga Scottish, zan sake maimaita miki wannan, Me kyau ne sosai kamar ke kyaunsa ne abun da ya rude ne, na kasa dauke ido daga gareshi shi kuma ya saka min fuska ya rika ba ni damar matsawa kusa da shi, ba kuma zan miki karya ba ta dayan gefen ina hange kudi da yake da su, kamar idan na same shi a matsayin saurayi na huta, domin ba addininmu daya ba, na san abu ne mai wahala mahaifina ya amince na aureshi, ban sani ba ashe yana da mata, nina fara nuna matsa kauna sai ya sanar min yana da mata yar da yara biyu a tsakaninsu, hakan sai ya saka na yi baya, shi kuma a lokacin ne ya kamu da kauna ta sosai, sai kusancinmu ya fara yawa, har ta kai ya kan bukaci na kawo masa abu a gidansa ko kuma ya saka matarsa da kanta ta kira ni ta sanar min idan wani abun ya taso na aikin ko kuma familynsu kamar taron biki ko birthday ko kuma danta idan ba shi da lafiya ko yarta, ban sani ba ashe ya fada mata cewar nice kadai babu ruwana a cikin matan da yake aiki da su, ni ce kadai ya yarda da ni saboda sauran wasu ba su da amana wasu kuma suna nemansa. Ashe yayi hakan ne saboda matarsa ta aminta da ni da shi, ko da an kawo mata wani zance ko ganin mu wani guri ba za a zargi komai ba, da haka muka fara mu'amala yana sakar min kudi yana nuna min kauna, na sake jiki da shi kuma na zama mai fuska biyu domin matarsa da wacce ta fini komai na mata kuma ta kasance yar kabilar igbo ta aminta da ni, amince da har yau bata daina ba. Ban ankaro ba na samu ciki na tafi asibiti da taimakon likita aka zubar da cikin dan wata biyu, muka sake komawa ruwa. Ina samu kudi na aikawa gidanmu a inda nake kuma ina watayawa yadda nake so, rayuwa ta ci gaba a haka wata rana bayan gama al'ada na tafi aka ba ni maganin hana daukar ciki, aka fada min dokokin yadda zan sha kuma na bi ka'ida da haka ba ni da haufi muka cigaba da shedanci, ban sani ba ashe tun kamin na sha maganin na dauki cikin ki amman babu wata alama a tare da ni dake muna akwai ciki, idan lokacin al'adata yayi zan yi idan na gama na yi tsarki. Wata rana, na tashi daga aiki, ina isa gida ciwon mara mai tsanani ya rufe ni, na sha magani be daina ba kuma be saba min haka ba, kusan ma zan iya cewa ba watan al'adata ba ne, da abun yayi min tsanani kamar ana murza mini ciki da mashin din wuta, sai na yi mamaki "yau kuma al'adar ta zo min a tsakiyar wata da fushi ne? Amma me ya sa take murda ni kamar na yi hauka? Na sha paracetamol. Na dinga juyawa a gado. Amma ciwon ya i sakina. Na daina numfashi da kwanciyar hankali. Cikin rudani aka kaini asibiti, bayan an ba ni gado na samu kulawar likita sai, Likitan ya dube ni, ya ce cikin natsuwa: Matar nan, ko kin san kina da ciki ne? Na ce da shi cikin zafin rai Dokta kar ka yi wasa da ciwo, al ada ce kake gani, ba ciki ba ne. Sai ya ce da ni: Toh ina jin heartbeat in yaro ma'ana bugun zuciyar jariri yana da rai a cikinki. Na ce Jariri kuma? Ciki?? Ai ni bana da ciki! Ba ni da wata alama ta masu ciki ma, Ina nono ya kumbura? Ina tashin zuciya? Al ada ma tana zuwa kamar yadda ta saba! Cikin natsuwa ya ce Wannan ba ciki irin na mutane bane. Wannan cryptic pregnancy ne, ciki mai oye kai. Na ga mata irin ki da yawa da ba su san suna da shi ba sai sun zo asibiti. Cikin na girma ne a ciki, yana oyewa a waje. Kuma Jikinki da kwakwalwarki sun hana ki gane cewa kina auke da rai. an tsaya, ya ce: Wasu mata sukan ci gaba da yin jinin da suke auka a matsayin al ada. Wasu ba sa jin canjin jiki saboda hormones insu ba su nunawa. Sai dai kawai wata rana a ga ciki ba tare da an shirya ba. Be gama bayani ba ruwa ya fashe min, a nan na saki hawaye. Ina kallon likitan kamar ace zai iya yin wani abu. Ina tambayar kaina da gaske haihuwa zan yi? Bayan sa a biyu kacal, na haifi wata yarinya da ta fi hasken idanuwa kyau, fara kyakkyawa mai matukar daukar hankali, ga jan gashi da blue eyes, kikashigo duniya cikin sirri, amma da annuri da kuka kamar kowane jinjiri. Baki rage komai daga kamanin mahaifinkin ba, kuma baki dauko komai daga gareni ba, sam ba za a taba yarda ni na haife ki, saboda gene din farar fata yana da karfi, a duk yadda aka haihuwa ko da yara ba su dauko gaba daya ba, su daukon wani kaso, masu gene mai karfi kuma basa raga komai haka kika zo min, kamar dai na rike ki, amman ina tsoron kallon da duniya zata min da kuma abun da iyayena za su ce, kanwar mamana ta siyo kayan jaririya na saka miki na lullube ki cikin zane, tun a asibitin tayi min fada bayan ni ma na yi ma kaina, ni da ita muka shirya ba za mu bar asibitin ba sai dare saboda mun shirya jefar da ke a inda muke ganin zaki samu masu rika ki. Sai karfe 8pm muka fita asibitin muka tari abun hawa zuwa inda ta bincika tun da rana ta samu, nesa da gurin muka mukaci mai taxi ya aje mu, da kafa muka taka muka isa gurin babban gida ne zagaye kuma inguwa ce da babu mutane sosai, na bude jakar da na zo da ita asibiti kuma wanda nake zuwa da ita aiki na dauko pen da farar takardar na rubuta sunanki "Aisha" domin shi ne sunan da na fi so, na saka a saman jikin ki sannan muka zagaya ta bayan gidan muka aje
Chapter 140 · 0% Book details