Sashe 133
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 5 BAYAN WATA UKU... ALIYU POV. Ya sauke wayar tare da sauke kafafuwansa dake kan karamin taber. "Tun da aka sallamoka asibitin nan baka zauna ba Aliyu kullum cikin neman yarinyar nan kake" Ya kalli Ummi. "Tun kamin na dawo daga Asibiti abun da nake ta kokarin yi kenan, kuma ai baki yarda na bar asibitin ba sai da na ji sauki radau idan ma akwai abun da ya fi jin garau na ji" "Allah yasa a dace har yanzu babu wanda ya samu labarin Emily" "Ameen, zan tafi gobe, tare da Mama Barakat ki taya mu da addu'a" "Allah ya tsare amman da ka hakura har sai ka samu kwanciyar hankali tukuna, bana son ka jefa kanka a cikin wata matsala" "Babu wata matsala In Shaa Allahu, kwanciyar hankalina yana tare da samun Emily matukar ban san halin da take ciki ba ba zan taba samun kwanciyar hankali ba, wata kila tana cikin mummunan yanayi shiyasa har yanzu bata waiwayi yarta ba, wata kila kuma ta gaji da rayuwar ne ta hakura a haka" "Jikina ya fi ba ni kamar tana tare da yaron nan da ya saka aka doke ka" "Abu ne mai wahala ta koma gurinsa, balle kuma shi da a yanzu yake boya? Daddy ya fada min dan Information kadan ake nema ana samu za a kama shi domin an tara masa duka laifukan da ya aikata kuma yake aikatawa, kin ga abu ne mai wahala ace yana tare da ita" "Haka ya fada min, yanzu haka baya gidansa, babu wanda ya san inda yake, shiyasa nake jin tsoron tafiyarka Aliyu, kar ace shi ma yana nan yana neman hanyar da zai cutar da kai" "In shaa Allahu babu abun da zai iya" "Idan ka je a kwana daya zaka dawo?" "Eh zan dawo a kwana daya saboda ke Ummi saboda ki samu natsuwa" Cikin yanayin damuwa da rashin son tafiyar Ummi ta ce "Tohm Allah ya tsare, ya kaika lafiya amman da jami'an tsoro zaka je?" "Aa zan tafi da addu'a dai" Ummi bata sake cewa komai ba ta mike tsaye ta. "Aliyu kana son yarinyar nan ne?" Ya daga kai ya kalli Ummi sai kuma ya kalli wani gefen alamar nazari. "Aa iyakar abin da na sani shi ne, ina matukar tausayinta, ta shiga mawuyacin hali tun daga haihuwa uzuwa yanzu, kuma ina ganin a yanzu babu wanda ya kamata ya kyautata rayuwarta irin musulmi, ya kamata ta san muma akwai na gari cikinmu, ban ce zan iya ba amman ina son na ga na maye mata gurbin wasu abubuwan da ta rasa ne" Ummi ta sauke numfashi a hankali ya fara takawa cike da girma ta fice daga garden din. Ta yi mamakin ganin bakuwar mota a gidan, duk kuwa da ta san gidansu gidane dake yawan samun baki koda yaushe amman wannan motar ta musamman ce domin sunan mahaifin Kameela ne a jikin number motar, hakan yana nufin motar gidansu ce daman su plate din motarsu ma da sunan familysu ake yi. Ta hau entrance din ta tura kofar falon da ba a gama rufewa ba ta shiga, ta gangan ta yi kamar bata san da kowa a falon ba har sai da Kameela ta mika mata gaisuwa. "Ummi ina wuni?" Ummi ta kalli gefen da Kameela take zaune. "Kameela? Ina ce dai lafiya?" Cikin yanayin damuwa Kameela ta amsa. "Lafiya kalau Ummi, na je asibiti ne gurin Aliyu aka ce an sallamo shi, shiyasa na zo gida" "Okay, akwai wani hakki naki da yake kansa da be sauke ba ne?" Ta girgiza kai kwalla na taruwa a idonta. "Aa na zo na duba lafiyarsa" "Baki bukatar duba lafiyarsa Kameela domin a yanzu babu wani abu a tsakaninku, amman duk da haka mun gode da ziyara zaki iya tafiya" "Sau ba goma ina zuwa ganinsa asibiti ba su bar ni na shiga ba, yanzu kuma na zo gida ba zaki bar ni na ganshi ba Ummi? Wata uku har da sati a sama ban saka Aliyu a ido ba wannan ma azabtarwa ce, saki daya yayi min Ummi ba uku ba akwai sauran gyara" Ta fada cikin kuka. Ummi ta taka zuwa inda take tana kallonta. "Haka ne, akwai sauran gyara a halayyarki Kameela, tun da har son zuciya zai iya daukarki ki yi kokarin kashe mijinki, kuma zuciyarki ta raya miki mahaifiyar mijinki zata yarda ki sake zama da danta saboda hauka ce ta haife ni, kuma zuciyarki ta raya miki wai akwai sauran gyara tsakaninki da mutumen da kika so ki shafe rayuwarsa daga doron kasa, har kika ikirarin an azabtar da ke da rashin ganinsa, ada can kina tunanin idan kika kashe shi gawarsa za a aje miki kina kallo?" Kameela ta kara fashewa da kuka. "Wallahi Ummi ina son Aliyu... Kishi ne Wallahi, kowa zai iya kuskure ki dauke ni kamar..." Ummi ta nuna ta da yatsa da taka mata tsawa "Ke yarinya kama hanya ki fice, idan kishi ne miyasa ita mahaifiyarka bata kashe mahaifinki ko kishiyarta ba? Abunda nake gani a labarai kika so ko wace jarida ta yi ado da fuskar dana a jiki? Lallai har yanzu baki da hankali" Ummi ta nuna mata kofa da yatsa. Kameela ta nufi kofar tana kuka ta fice, Ummi ta tsaya jiki windows har sai da ta ga ficewarta a gidan sannan ta juyo ta nufi stairs. TURHAN POV. Wani irin kuka sosai Fatima take da daukar numfashi tana kiran sunan Momy. "Momy... Momy..." Ammy ta kalli Fatima dake kwance kan godonta tana bachi a motse saboda tunani da rashin cin abinci. Sai kuma ta kalli danta da ya fi Fatima rama da shiga tashin hankali saboda damuwarsa da Fatima take da tambayar ina Momynta, ga kuma rashin sanin halin da Aisha take ciki domin tun da ta tafi har yanzu ba a samu wanda ya ji duriyarta ba, kuma bata dawo gurin yarta ba. "Da ace na san haka rayuwa zata zame maka ta zame mata daban hada auren nan ba" Ammy ta fada cikin tsananin damuwa, abu ne da yake bayyane a gurin kowa babu wanda zai ce ya taba ganin Turhan a cikin wata matsala da ta haifar masa da rashin cin abinci na kwana daya, sai ga shi a yanzu baya iya cin abin kirki bachi ma wani lokacin sai yayi da gaske yake yi, saboda tunanin tambayar da Fatima take masa, da kuma tunanin a wane hali Aisha take ciki, a dayan bangaren kuma yana auna tsakanin tsanar da ta yi masa, saboda kawai yarta ta zaba shi sai ta tafi ta bar shi da ita har na tsawon lokaci babu sako ba aike babu wata hanya da za a iya samunta. "Haba Ammy be kamata wannan kalamin ya fito bakinki ba, ai ke alheri kika yi nufin aikatawa kuma shi kika aikata kuma alheri ya samu tun da gashi ina da Fatima, ni ne na kawo duk wata matsala da muke ciki yanzu, tunani ne sai na rasa wane zan yi, kullum da fargaba nake farkawa a guntun bachin da yake daukata a karshen dare, fargabar tambayar Fatima, ga shi ta dauki damuwa ta saka a ranta yanzu ta daina sakewa da kowa ta daina walwala, kuma ita kanta Aisha yanzu ba mu san wane hali take ciki ba, kuma ina fargabar kar ace ta fada wani hali saboda rashin Fatima idan har haka ya faru laifin a kaina zai sake komawa" Ta kalleshi cike da tausayi. "Ka yi iya kokarinka kuma na baya ba, ka nemeta a lokacin da baka san tana tare da yarka ba, a yanzu kuma da ban saka ka ba, ka saka kanka ka je har garin da ta zauna baka sameta ba, a garin nan bana tunanin akwai inda kafarka be taka ba gurin nemanta, nan ma baka dace ba, tun da ka baro Sudan baka koma ba saboda Aisha, a haka ma ka biya Turhan kuma ina alfahari da kai, jikina yana raya min kamar tana wani guri kusa ta boya ne kawai saboda ta fitine mu, tun da gashi yanzu Fatima kullum sai ta daga mana hankali saboda neman mahaifiyarta" "Amman me yasa bata dawo ba?" "Saboda ta azabtar mu mana, saboda idan ta waige mu sai mu mika mata Fatima jiki na rawa" "Da ma dai ban sake ta ba, zata iya zuwa fa ta dawo da auren wani akanta" "Zuciyar yarinyar nan bata da kyau, duk wata uwar kirki ba zata iya tafiya mai tsayi haka ta bar yarta ba, saboda kawai ubanta yayi mata ba daida ba, ni miyasa ban kyale ka ba? Bayan duk abun da ubanka yayi min? Wani lokacin idan na tsaya ina tunani sai na rika ganin kamar ba Aisha bace ban yi zaton zata iya aikata haka ba" "Na fi tunanin kamar bata lafiya, ko kuma wani abun ya same ta, wata kila da yanzu ta dawo, domin yadda nake jin Fatima ni kam ba zan ma iya sati ban saka ta a ido ba" "To ya sani tun da ta zabarwa kanta guduwa? Wani abun ba kaddara ba ce har da hali" "Kuma ni sai nake ganin kamar Aliyu ya san inda take, kawai dai yana wasa da hankalina ne ko kuma yana jiran na nemi taimakonsa ne wanda abun ne da ba zai taba faruwa ba har abada, gashi ba wani tufafin kirki take sakawa ba yanzu" Yana maganar cike da zafin kishi marar misaltuwa. "Idan har abun da kake zargi ya tabbata to ni ina baka shawarar ka hakura da yarinyar Turhan, shi kuma sai mu ga idan dan halak ne" "Ai be san kunya ba Ammy ina cire kafa tasa zai saka ya taka, da ace ya san kunya ba zai aikata abun da ya aikata min ba, domin no matter what ya fi kusanci da ni fiye da Aisha, amman ya zabi ya ci amanata, na san ban kyautata ba amman dai ai ni abokinsa ne Aisha kuma be da alakar komai da ita" "A wani mutum makiyinka ne Turhan a cikin yan'uwa ma akwai su kuma munafikin mutum yana da wahalar zama da ganewa, amman ba zaka taba sanin sai wani abun ya faru, wani zaka samu yana maka hassada ne domin idan babu wannan ban da