← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 177

Sashe 71

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 3 "Me kika saka a miyar Kameela?" Ta juyo a firgice tana kokarin dakewa domin bata yi zaton ya biyo bayanta ba. "Me zan saka a miyar Aliyu?" "Miyasa kika zubar?" "Saboda ta yi sanyi" "Wannan cooler ba yau na fara cin abinci da ita ba, kuma yanayin miyar be nuna yayi sanyi ba, kuma tun da nake dake ai baki taba sauya min miya ba, dan haka ki amsa min tambaya ne kika saka a ciki Kameela?" Ya daka mata tsawa yana hade fuska kamar be taba dariya ba. "Me zan saka a ciki? Ni ban saka komai ba" "Guba kika saka a ciki? so kika yi na ci na mutu? Da kika ga na miki rantsuwa ina baki hakuri sai tunaninki ya sauya ko?" Ta dafe kirjinta ta zaro ido. "Guba kuma? Me zai saka na saka maka guba a cikin abincinka Aliyu?" "Saboda rashin hankalinki da bakin kishinki, shiyasa na yi mamaki da baki yi hauka kin nuna halinki a lokacin da kika ga Emily ba, saboda kin san abun da kika shirya?" Ta fara hawaye jikinta na rawa "Ka zarge ni da kowane irin abu saboda kishina Aliyu amman ban da kisan kai, kuma a kisan ma na rasa wa zan kashe sai kai da nake kauna?" "Abun da kike yi bana masu hankali ba ne, kwakwalwarki ta samu matsala ki shirya gobe zaki koma Kaduna idan kin je can zan samu likitan kwakwalwa ya duba ki" Yana kaiwa nan ya juya ya fice daga Kitchen din, ta bishi da kallo kamin ta jefar da kular hannunta kasa da karfi ta fara bin kayan Kitchen din tana watsewa tana kuka, sai kuma ta bi bayansa tana kuka ta shiga dakinsa. "Ni babu inda zanje, lafiyata kalau ba ni da hauka Aliyu, idan ma wani abun kake zargin na aikata saboda wa na aikata ba kai ba? Yaushe muka yi aure da zaka fara barin wata ta shiga rayuwarka? Idan kuma na yi fada ka buga min warning ko ka dauke kafa kana nuna wata banza ta fi ni?" Ya katse wayar da yake ya matsa kusa da tsinka mata mari. "Karamin yaro kika dauka ko marar wayo? Yaushe zan zauna na miki rantsuwa na miki alkawari kuma ki rika dawo da magana baya? Okay saboda ina fada sai kika zabi ki yi poising dina? A tunaninki idan na mutu ke zaki huta ne? Hakki rai ai ba zai barki ki samu salama ba" Ta zube a kasa gabansa dafe da kunci tana kuka. "Wannan ba kishi ba ne Kameela, hauka ne kina bukatar likita ya duba kwakwalwarki, wato ki kashe ni kije ki auri wani?" "Ko mutuwa ka yi Aliyu ba zan iya auren wani ba, ina sonka ka sani ko wata mace ka kalla Aliyu jin nake kamar zuciyata zata fito, idan har ba son yarinyar nan kake ba me yasa baka hadata da Turhan din ba? Me kake jira?" "Yanzu duk wannan ya wuce na fada miki ki shirya gobe zaki koma Kaduna" "Ni babu inda zan je, na koma na cewa Hajiya Me?" "Ki fada musu guba kika zuba min a abinci, kina kokarin kashe ni, dan haka ni kuma yanzu ba zan yarda dake ba, ba zan iya kwana gado daya dake ba, ba zan iya sake cin abincinki ba, zamanki a gidan nan ba zai taba bani kwanciyar hankali ba, tafiyarki gida shi zai fi a gareki da kuma ni" "Ni ban saka maka guba ba, sai idan daman kana neman dalilin rabuwa da ni ne kawai saboda ka kawo wata, Wallahi Aliyu ba zan taba kyaleka ba, Wallahi ko mutuwa na yi ba zan barka ba, sai fatalwata ta addabi rayuwarka, saboda kai ka daukar min alkawarin da ba zaka iya cikawa ba, Aliyu ko rabuwa ka yi da ni ba zan iya kallon ka yi rayuwa da wata macen ba" Aliyu ya saki baki yana kallonta. "Ah lallai baki da hankali, ashe abun na ki ma ba kis hi ba ne, hauka ce, ilminki be miki amfanin ba tun da har kika iya bari zuciya da shedan suka rinjayeki, abun da kike yi a yanzu Kameela yana nuna min zaki iya kauce hanya kam kishi, zaki iya komai ido rufe" Ta lumshe ido tana sassauta kukanta ita kadai take iya fahimtar kanta ita kadai tasan halin da take ciki, wata kila ita kam tata jarabawar kenan so da kuma kishin Aliyu. "Ka yi hakuri Aliyu" "Ba abu ne da za'ayi hakuri ba, maganar rai da mutuwa ake, kin san idan Ummi ta san da maganar nan aurena da ke ya kare? Kuma ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba sai ta kai ki kotu" "So kake na tafi Aliyu? Haihuwa daya ka fara juya min baya? So kake na tafi na barka da wata banza mushirika karuwa macen da akanta babu kalar fadan da baka min ba? Idan na kome me zan fadawa Abbana? Miye ma'anar na koma gida? Ka sake ki ne kenan?" Ya nufi closet dinsa ya canja tufafi jikinsa ya dawo ya dauki keys dinsa da wallet sannan ya ce. "Bana son na dawo na tararda ke a gidan nan gobe da safe" Ya nufi kofa yayi ficewarsa tana kallonsa har ya rufe kofar dakin. Wani bakinciki ta ji ya ratsa zuciyarta, ta raba kafafuwanta tana kuka mai taba zuciya, iyakar karatun data iya na son mijinta ne da kishinta, irin kishin da hankali yake rumgumar tunani su gudu a kwakwalwarta ta aikata abun da bata san inda inda illarsa zai kaita ba, da ace Aliyu be bata hakuri ba a yau da ya ci abunda zai yi sanadin ajalinsa, saboda tana ganin kamar hakan ne mafita a gareta da kuma shi, duk kuwa da ta san ba lallai hakkin rai ya barta ta huta ba. Sai dai sanin bata da wata mafita sai wannan ya saka ta cire batirin agogo falonta ta daka ta saka masa a miya, saboda ta gane hargowa bata canja komai, domin da ta yi haukanta na farko bata samu abun da take so ba. Yau kuma zuciya taso ta kai ta baro, saboda ta biyan mijinta kuma ta tararda abun da take zargi, idan tace bata yarda da shi ba a yanzu bata yi ma kanta adalci ba, amman sanin a guri daya suke aiki da Emily ya fi komai daga mata hankali ko ba komai zai ganta kullum kuma za su yi magana, daga haka bata san iya inda abun zai tsaya ba, musamman data lura kamar Emily tana da muhimmanci a gareshi ko kuma shi din yana da wata manufa akanta, idan ba haka ba miyasa ya sama mata aiki a kusa da shi? Meyasa ba zai hadata da mai nemanta ba? A wane dalili yayi mata tsawa yayi fada da ita saboda kawai ta kira Emily a waya. "Zan iya rayuwa ko babu kai Aliyu, gidanmu kuma ba gidan yari ba ne da zaka ce na tafi na kasa tafiya" Ta fadawa kanta sannan ta mike tsaye ta fice daga dakinsa zuwa nata, tana shiga dakin sai kuma ta nemi courage din ta rasa, kawai sai ta rushe da sabon kuka, tana matukar son mijinta tana matukar kishinsa wannan abu ne da ya ke rubuce a cikin littafin kaddararta, rashin aiki da lissafi zai saka ta kashe aurenta da kanta yan'uwa kuma za su mata dariya su ce daman sun fada, ta tashi ta fita dakin da sauri ta dawo seating room gurin da wayarta take ta dauka ta aikawa Aliyu sakon ban hakuri da rokon kar ya saketa. "Ba zan iya rayuwa babu kai ba Aliyu, ko sakina ka yi ba zan iya rabuwa da kai ba, idan ma har kana tunanin ina kokarin kashe ka ne ka yi hakuri ka yafe min dan Allah" Ta jira be bata amsa ba, hakan ya saka ta kira shi be daga ba kuma be kira ba, ta san halinsa ta san idan yayi fushi yana da wahalar saukowa, ita ma dai jin ta yi bata bukatar zaman gidan dan haka ta sauya tufafin jikinta ta fice duk kuwa da kasancewar ba kowa ta sani a garin PH sai Tasmia. ALIYU POV. Hotel ya kama domin ba zai iya kwana a gidan ba matukar Kameela na ciki hankalinsa be taba tashi ba irin yau, ba dan komai ba sai dan ta fi kowa kusanci da shi ta san lagunsa ta kowane gefe idan har zata iya saka masa guba a abinci to zata iya masa komai ma. A hotel din ya karasa dan yammancin da ya rage masa, kansa a kulle tunanin idan yayi baya tsayawa shi dai gaba daya ya gagara fahimtar kalar kishin Kameela shi ko a tarihi be taba jin irin nata ba, ko da yake a yanzu yana dora abun ne a babin matsalar kwakwalwa. Ya ga kiranta ya kasa amsawa haka ma sakonta be amsa rokonta ba. Ya sani idan be daukar mata mummunan mataki ba abun da zata aikata sai ya fi wannan. Sosai yayi ma matarsa addu'a a sallarsa da Isha'i ya roki Allah ya sassauta mata wannan mugun kishin ya saka mata natsuwa da kwanciyar hankali a zaman aurensu, ya son matarsa kusan son ne dalilin da ya saka yake mata komai kuma yake daga mata kafa har take kokarin wuce gona da iri. Sai da ya hau gadon dake dakin na Hotel ya kwanta sannan ya kira Family Friend dinsa Nura da suka kwana biyu ba su yi waya ba tun bayan da ya kira yayi masa gaisuwa da barkar haihuwar da aka yi masa. Nura ya amsa wayar yana zolayarsa. "Manya masu kasa baku nema sai dai a neme ku" "To yanzu kai ka nemi ki ni na nemeka?" Nura yayi murmushi mai sauki. "Malam har garin Abuja ka shigo fa baka neme ni ba, sai da na hadu da Ummi take fada min ka shigo" "Tafiyar ta kwana biyu ce kuma ban shirya ba tafiyarce kawai ta zo a haka, ka san yanayin aiki ba ko da yaushe muke samun time ba" "Haka ne, aikin ne kusan da yanke mana komai ai, zumuncin ma idan ba mu yi da gaske ba sai mu bar shi saboda neman duniya"
Chapter 71 · 0% Book details