Sashe 174
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawo kayan har sai da Emily ta rasa bakin yi ma Aliyu godiya. A haihuwar Abulkhary Emily ta san ta ci naman sunan anta, ta san a aje mata nama mai uban yawa ace nata ne ita kadai bayan an bawa mutane, duk abubuwan da aka yi babu wanda ya fi burge ta kamar taron suna, saboda ta ga mutane sosai wasu ma bata san su ba sai a lokacin, wasu kuma sai a lokacin suka san Aliyu ya sake mata ba Kameela ba, kuma ya sauya gida. Ammy bata zo mata barka ba, amman ta aiko mata da Fatima an yi komai da ita kamar yadda aka yi na aurenta. TURHAN POV. Saboda hankalin Emily dana mahaifiyarsa ya kwanta ya yarda ya bar Fatima a gurin Ammy, ba dan baya son zamanta a kusa da shi ba, ga kuma karatunta da baya son ya rabu biyu idan bata zauna gu daya ba. Yakan ziyarce ta a duk karshen wata, wani lokacin ma ba'ayin wata idan yayi marmarin ganinta zai zo ya ganta. Yana yawan zuwa ne saboda yana tsammanin jin kyakkyawan labari daga rayuwar Aliyu da Emily, tun a wacan ranar da yar'uwar Ammy taje daukar Fatima ta fada masa ta ga Emily na kuka da alama sun samu matsala da Aliyu ne ko sun fara samu. Sai zuciyarsa ta masa dadi yana jin kamar amanar sa da Aliyu ya ci zata fita, yana jiran ranar da Emily zata fito ta dawo masa. Be taba yarda ya tambayi yarsa labarin Emily ba saboda be son ta yi subutar baki ta fadawa Emily cewar Turhan yana tambayarta. Haka kuma yana tsoron ya tambaya ya ji wani labarin da ba haka ba. Be tana tsinkewa ba sai da Fatima take fada masa momynta tana da ciki, a waya suka yi maganar da Fatima amman a ranar be iya kwana ba, sai juyi yake yana tunanin yadda abokinsa zai zauna da matarsa har ta samu ciki. Be kara tsanar Aliyu ba sai da yayi waya da Ammy ta fada masa Fatima na gurin Mamanta saboda ta haihu. A ranar ji yayi kamar ace Aliyu yana kusa da shi ya daba masa wuka ya mutu, domin ya fahimci Aliyu ba shi da niyar sakin Emily ko da yake ai yayi wuri yanzu, ya ba su lokaci zuwa gaba mana idan ta canja. KAMEELA POV. "Kin san fa yau ba girkinki ba ne, ki bari sai girkinki ya juyo sai mu tafi tare, saboda yanzu dare yayi kar mu shiga hakkin madam" Ta dauke hannunta daga jikin angon nata tana murmushin karfin hali. "Shikenan Allah ya tsare" "Ameen" Ya juya ba tare da ya damu da ya sumbance ba kamar yadda Aliyu yake ya shiga motarsa ya daga mata hannu ta daga masa ya fice. Falonta ta dawo ta zauna tana hawaye, wai yau ita ce take son fita wani Namiji ya kalli kwayar idonta ya fada mata yau ba kwananta ba ne, ita take sharing miji da wata a yau, ita take raba girki da kwana da kwana da wata, a yanzu su biyu ne a zuciyar mijinta ba ita kadai ba. Lallai mace yar gaba da baya ce, hakika ta yi aure amman ba ga wadda take so ba, ba ga wanda zuciyarta ta natsu da shi ba, ta yi ne kawai saboda yan'uwanta da kawaye da kuma zuciyata suna zugata ta manta da Aliyu, kuma ta auri wanda ya fishi kudi kamar yadda aka so da farko. Ta yi auren, amman ta rasa soyayya da kulawa da kauna irin wanda Aliyu yake nuna mata, a nan ta san banbancin ba ko wane mai kudi ba ne yake da lokacin iyalinsa lallai irin Aliyu daya ne cikin dari, ya bata dama ta san shi ciki da waje, ta dauki wayarsa ta bincika duk abun da take ra'ayi, wannan kuma ko kusa da wayarsa be yarda taje ba, ga shi yana masifar tsoron uwargidansa fiye da ita. Gaba daya irin zaman da ta yi da Aliyu ya sha banban da wannan da take aure. Sosai da sosai take marmarin mijinta take kewarsa da rayuwarsu, take nadamar abun da ta aika a baya, wata kila ta bata biye zugar zuciya data yan'uwa ba ta tsaya jira wata kila Aliyu zai iya sake zama da ita a matsayin mata ta biyu har ma ya saki Emily tun da ta san yana kaunarta. Ganin kamar zaman ba zai mata dadi ba, tsarin rayuwata be dace da nashi ba ya saka ta fara shirye shiryen barin gidan ko ta halin yaya domin komawa tsohon mijinta, kwatsam sai ga ciki ya bayyana a dole ta zubar da makamanta ta maida hankalin gurin rainon cikinta ta kuma kai zuciya nesa akan kishiryarta if not zata iya mutuwa lokacin be yi ba. Ba laifi da ta haihu ya nuna mata kulawa sosai domin kusan wannan ce haihuwar farko a gurinta saboda wacan an be rayu ba, da yanzu ita ma tana da jini da Aliyu. A yanzu kuma idan ta tuna wata ce ta haihu da shi ba ita ba sai ta ji kamar zata mutu, ga shi ta bangaren mijinta ma ba ita ta fara tara masa yara ba. Tsoron kar ta fita gidan mijin ta sake afkawa wani wanda ya fi shi munin hali, gashi bata da tabbacin ko Aliyu be zai maida ita, ko kuma aa ya saka ta hakura ta zauna gidan sabon mijinta ta rumgume yarta data haifa to her it's not an easy thing ta bar gidan ta bar yarta, bayan kuma bata fuskantar wata matsala a gurin mijinta sai kishiya, sai kuma rashin kulawa kamar Aliyu da yake nuna mata, dadin dadawa kuma tana zargin kamar wani auren yake son karawa su zama su uku, kuma bata isa ta hana ba, domin ba ita ce ta farko ba. Daman hausawa sun ce idan baka yi sharar masallaci ba sai ka yi ta kasuwa ko gidan giya. EMILY POV. "Yace idan an yi hutun karshen shekarar nan zai tafi, daga nan ya nuna masa matarsa" Ta fada tana kwance kan ciyarsa yana wasa da gashin girarta. "Ba za ki bari sai Abulkhary yayi wayo ba?" "Wayo na nawa kuma? Wannan yaron ko kai ya tsofeka" "Eh tun da kakana ya haife shi ba" Ta yi dariya. "Amman za mu je tare da kai ko?" "I don't know kin san yayanki nan ba wani, yi na yake ba, ya kusan sakawa na rasa ki fa, kuma na lura kamar baya son ina shigar masa lamurra tun da yake kira be taba cewa a ba ni mu gaisa ba" Emily ta bude ido. "Kai kasan shi fa rayuwar turawa ce da shi ba wani damuwa yake da mutane ba, shi ne kawai, auren nan ma ban dauka zai yi ba, shi kansa yace be dauka zai yi aure ba sai gashi ya hadu da wanda ta yi masa" "Dan ta kife ne wannan yayan naki, Allah ya so ni aka gano dan'uwanki ne da na sha wuya a hannunsa" Emily ta sake bushewa da dariya har da kyalkyatawa Aliyu sai kallonta yake with affection yana murmushi. "Wallahi ba shi da matsala, ka ga ko bikin nan da aka yi, shi yayi ta gabatar da ni a gurin mutane a komai baya bari a bar ni baya, na jidadin yadda ya nuna min kulawa, shiyasa ban wani damu da yadda mahaifiyarsa ta nuna min bata son ganina ba, saboda naje saboda Dr A-B ne da kuma zaton mahaifinsa zai zo bikin sai gashi be samu zuwa ba" Ya ja mata kunne. "Mahaifinsa ke ba da ke ba?" "I don't know ko ya karbe ni ko be karbe ni ba yet" "Mun gaisa, na gan shi ta system din Dr A-B ya gabatar masa da ni, ya kar i numberta amman ai har yau be kira ni ba" "Amman da ya ji cewar ke yarsa yayi mamaki?" "Eh Dr A-B yace yayi mamaki sosai, yace shi be yarda ba, da farko har yayi denying cewar ya taba zama da Mama Baraka sai da Dr ya gabatar masa da hujoji sannan ya yarda, amman da muka gaiwa na ga dai kamar damuwa a fuskarsa sosai, amman har yanzu be kira ni wata kila baya so na" "Aa ko dai yana jin kunya ne ba, ko kuma be san yadda zai kalli abun ba, amman yanzu idan muka je zamu gani ai, kawai abun da nake so da ke duk wani abu da zai biyo baya na rashin dadi ba za ki damu ba ki min alkawari" Ta dago ido ta kalleshi a shagwabe. "Ina da kai a yanzu Aliyu me zai saka na damu" Ya kama bakinta ya matse. "Aliyu ko?" "Nooo My Soul Mate" Ya saki bakin ya kai mata rankwashi a kai. Ta da ga jikinsa. "Ka yi na kudinka" Ya san me take nufi dan haka ya kalleta da sauri. "Yi hakuri, zo ki rama" Ya kai hannu zai rikota ta matsa da sauri ta tashi a guje ta bar masa gurin tana dariya. Murmushi ya mike tsaye ya bi bayanta. Before time din da Dr A-B ya tsara yayi, Aliyu yayi nasa tsare tsaren ta yadda zai samu damar raka matarsa, sai kuma aka yi sa'a a lokacin ana hutun karshen sabuwar shekara ne. Ana gobe za su tafi Abuja, Aliyu ya kaita da anta gurin Mama Baraka gurin mata bakwana, ta zaren labari yayi tsawo Emily ta bayyana mata fargabarta na tafiya tana ganin kamar ba zai karbe ta ba. "A gurin Bature haihuwa babu aure ba illa ba ce, kusan ma sun fi yin haka, ina da yakinin zai karbe ki" "Idan ya tambayi labarinki fa?" "Ki fada masa komai, amman ban da mutuwar aurena" "Why? Za ki komawa mahaifinsu Kameela ne?" "Ba lallai ba, na lura kamar ya dauki abun da zafi sosai, ni kuma ban shirya auren kowa a yanzu har sai na aurar da duka yarana, by that time kuma na san aure ya fita kaina" "Amman da yanzu ace Mahaifinsu Kameela zai dawo zaki koma masa" "To me zai hana?" Ta amsa tana murmushi, Emily ta kalleta ta sauke kai ga dukan alamu tana son tsohon mijinta, sai dai kuma zama ya kare a tsakani. Sai dare Aliyu ya