← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 177

Sashe 36

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 1 Yadda ta bar gidan haka ta same shi domin kusan lokaci daya Emily ta shigo gidan tare da Chidimma da London. "Ina kokarin gyara falon ne da gidan ne yanzu sai na dora abinci" Ta fada ganin yadda Emily take kallonta. "Ina London" "Tare muka dawo an sallame shi" Har Emily ta juya sai kuma ta juyo ta kalli Chidimma. "Baki kira ni na daukoku ba? "Na ga kin fita a cikin fushi ne, shi ma kuma fushi yake da ke, ina gudun bacin ransa ne, shiyasa sai na kira Sir Vito ya kawo mu gida" Emily ta juya ba tare da ya sake cewa komai ba. Ki yi hakuri da abun da London yake miki, kin san yana dauke ta lalura ne, amman a hankali zai fahimta ya daina kamar yadda yake yi abaya" Har ta ci ta cinye Emily bata sake juyowa ba haka kuma bata sake cewa komai ba ta haura sama ta shiga dakinta sai ta samu Vito zaune a ciki yana kallon kofar data shigo. "Ina kika je?" "Inda nake ra'ayin tafiya" Ta amsa masa rudely, kallonta kawai yake har ta nufi closet dinta ta cire talkamin kafarta. Ta saba fada masa bakar magana but like ya tambaye ta wani abu ta amsa masa da wata maganar dabam. Wayar dake aljihunta ta yi ringing ta ciro wayar ta amsa ba tare da fargabar komai ba. "Kin isa gida lafiya?" "Lafiya kalau, na gode da kulawa" Ta aje wayar a gefen closet din bayan ta amsa. Da wa kike waya?" "Will you excuse me? Ina son na huta ne" Ya sake dubanta a tsanake kamin ya mike tsaye ya fice daga dakin. Yana fita ta sauke numfashi da karfi ta lumshe ido tana sauraren yadda zuciyarta take bugawa da karfi. Vito ya sauko yana kallon Fatima dake gabansa kadan tana saukowa, juyowa ta yi tana kallonsa har ya kawo daidai inda take tsaye. Vito... Kasan waye babana" "Emily bata fada miki baki da mahaifi ba?" "Meyasa ni kadai ce a makarantar mu ba ni da Baba? Kowa a duniyar nan yana da Baba amman ban da ni why? Meyasa sunana yake Fatima Aysha Emily?" Ya rage tsawo ya risina daidai ita. Saboda ke kadai aka haife ki, you're special girl with bad attitudes" Ya barta a gurin tana binsa da kallo cike da tsana, fasa sauka ta yi ta koma sama ta shiga dakin dan'uwanta. Wanka Emily ta yi ta fito ta shirya cikin short gown ta atamfa ta zauna gaban madubi tana kallon kanta. Maganganun Tasmia suna ta yi mata yawo akai, sai ta ji ina ma ace wani ya fada mata haka tun a baya, ko da yake a yanzu din ma lokaci be kure ba. Ta yi murmushi. "Ina fatan yadda kalamanki da fuskarki suke, haka zuciyarki ma take" Ta fada sai ta bude aljihun madubin dake gabanta ta dauko wani karamin box ta ciro agogon mutumen da ta kasa manta yadda ya taimaki rayuwarta har ta rayu. Ta shafa agogon tana rausayar da kanta. "Ku biyu ne kawai musulmai masu halin kirki, kai ka bar min shigo Tasmia kuma ta bar min kalamai" Ta karasa tana murmushi, sai kuma ta mike tsaye ta nufi jakarta ta saka agogon ciki ta nufi wayarta da sako ya shigo ta duba. "Zaki iya zuwa office a duk lokacin da kika shirya, Office dinki yana nan yana jiranki" "Why? Saboda kai ma ka yi amfani da wannan damar ka shimfida min dokoki ka mulke ni a yadda kake so?" Ta yi jira har ta gaji be dawo mata da amsa ko wani sakon ba. Aje wayar ta yi ta fice daga dakin zuwa dakin da danta yake, wasa ta samu yana yi da Fatima har da dariya sai dai shigowarta ya saka dukansu su biyu yanayinsu ya sauya, Fatima ta dan hade rai, shi kuma ya juya mata baya gaba daya irin yadda yake idan yana fushi baya son kallon fuskar mutane. Ta zauna akan gadon ta kai hannu ta shafa bayansa. "My babu, har yanzu fushi kake da Momy? Why saboda Momy ta jima bata zo ba? Me Momy ta yi ne London har kaka juya mata baya? Momy da take kaunarka? Taka siya maka abun dadi...? Ina kake son mu tafi? Kana son mu yi wasan ruwa?" Duk rarrashin da ta yi masa da kalamai be juyo ba kuma be sauka daga fushin ba, da ta yi kokarin juyo da shi ma sai ya saka mata ihu ya ruda dakin har sai da Chidimma ta bar abun da take ta shigo ta rumgume shi. Tashi ta yi ta fice daga dakin ta sake komawa dakinta, ta kwana da tunani kala kala a ranta ta kulla wannan ta kwance wacan, daga karshe ta bi tsarin da zuciyarta ta dorata ta hau ta hakikance cewar ba zata koma aiki ba, amman zata nemi wani aikin domin cika burin da take da shi. Washe gari ita da kanta ta shiryawa yaranta abun karyawa, ta zubawa Fatima nata a lunch box na London kuma ta bawa Chidimma ta ba shi, ita kuma ta koma ciki ta saka kanana kaya da sneakers ta fito ta shiga kitchen ta dauki water bottle ta zuba swan water sannan ta fito. Zaki tafi wani gurin ne Ma'am? "Yes zan je motsa jiki ne" Chidimma ta dan tabe baki kadan domin ba abun da Emily ta saba yi ba, Emily ta nufi London da Chidimma ke feeding dinsa ta sumbance shi ta shafa kansa sannan ta fice tana fadawa Fatima ta yi hanzari direban dake kaita school yana jiranta. "Yau ba zan je School ba" "Saboda me?" "Saboda kowa yana tsokana ta a makaranta, idan aka kira sunana" Ta fada tana huci, Emily ta aje gorar ruwan dakin hannunta ta nufi Fatima ta kama hannunta nufi sama da ita. Ta zaunar da ita kan gado. Cikin masu miki dariya akwai wanda ta fiki gata? Ko ta fiki kashe kudin da kike kashewa?" Ta girgiza kai kamar zata yi kuka. Toh karki sake bata ranki idan sun fada miki haka, ai su iyaye maza suke da, ke kuma kina da uwa mace jajirttaciyya mai kokarin sama miki rayuwa mai kyau, mai son abun da kika so, ba kin ce kina son mu bar gidan nan ba.? Ta daga mata kai. Duk abun da nake kokarin aikatawa a yanzu na yadda zan bar gidan nan ne, ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa da abun da suke fada miki, kuma ki daina fadawa kowa labarin ki Fatima ke ma kina da surutu, idan suka miki dariya kice haka kike so, kuma ke baya damunki, ki min alkawari ba zaki sake damuwa da maganaer su ba, ni kuma zan miki alkawarin barin gidan nan cikin kankanen lokaci kuma na siya miki duk abun da kike so, tashin hankalinki tashin hankalina ne Fatima, karki sake min magana makamanciyar wannan Ta daga mata kai sannan ta kai mata yatsa. I promise" "Good yanzu shiga ki wanke fuskarki idan kika yi haka kin wanke bakin ciki babu sauran damuwa sai ki fito da murmushi muje na rakaki mota" Ta tashi da saurinta ta shiga bandaki ta wanke fuskar ta fito da murmushi Emily ta kama hannunta suka fita tana far'a kamar na ita ba. Chidimma na kallonsu har Emily ta dauki lunch Box dinsu suka fice, sannan ta kalli London da fuskar tausayi tace Ka gani Momy bata son London sai fatima, idan London yayi fushi Momy bata tsayawa ta rarrashe shi amman tana tsayawa ta rarrashi Fatima Ya bata fuska sosai yana ta yawo da idonta ta saki baki yawu na sauko masa, ta cire tissue ta goge masa bakin. Amman Chidimma tana son London sosai bata masa fada, Sir Vito ma yana son London amman Momy bata son London" Ta matsar da kujerar ta kusa da tashi ta rumfume shi tana murmushi tare da shafa bayansa alamar rarrashi. Sai da Emily ta ga wucewar motar da aka dauki Fatima zuwa makaranta sannan ta fara tafiya da sassafar, tafiya ta yi mai nisa har ta fita daga unguwar daga daya, daman manufar fitar ba domin motsa jikin ba ne kawai. Unguwar dake kusa da ta su ta shiga tana kallon shagunan da suka gurin wanda ta ga alamar babban shago ne ko super market sai ta dauki hoton gurin saboda kar ta manta. Kusan duk inda ta bi kallonta ake saboda yanayinta, kusan kowa kallon baturiya yake mata saboda yanayin shigarta idonta da kuma gashin kanta dake bude. Taxi ta hau a lokacin da zata dawo gida saboda gajiya da ta yi, cikin gidan ta shiga ta dauko masa kudinsa ta ba shi sannan ta koma ciki ta yi wanka ta karya ta haura sama domin bawa gado hakkinsa. KAMEELA POV. "Na jidadi sosai ko da na iso na tarar an kawo min komai na gode Honey" "You deserve it, Allah ya kara miki lafiya" "Ameen, yaushe zaka zo?" "Soon dear" "Ka kula min da kanka" "I will" Ta sauke wayar tana kallon kanwarta dake tabe baki, Anty Shafa data doro alwala ta tana yarfar da ruwa ta ce. Kina godiya akan abun da kin fi karfinsa, dole ne daman yayi miki hidima tun da haihuwa kika yi kuma dansa kika haifa ba dan wani ba" "Hmmm Anty Kameela da yanzu ke matar Governor ce, da yanzu ke ce first lady, amman kika ki yarda kika watsa mana kasa a ido kika zabi dan makiyinmu" Ta sauke numfashi. Siyasa ce fa, saboda Baba ya rasa kujerar Senator mahaifinsa ya samu ba wani abun ba ne, kowa rabonsa yake ci, kuma zamansu yar jam'iyar hamayya wannan siyace, daman ta gaji haka, ni ba zan iya zaman kishi da sa'anin mahaifiyata ba akan zama first Lady, kuma yadda nake da kishin nan ba zan iya raba kwana da wata mace ba, kuma ba zan iya auren dan siyasa, dan haka ku bar ki na zauna da mijina muna son junanmu" "Ga ki gashi ai idan namiji ne, har da wani yarda da alkawarin da yayi miki saboda baki da tunani, mahaifiyarsa har magana ta fada min wai ban yi aure ba" Cewar Anty Shafa again tana kokarin saka hijab. "Aliyu ya
Chapter 36 · 0% Book details