← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 80

Sashe 77

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasir da ya tafi da niyyar yin sati biyu yau shine har yayi wata uku bai dawo ba, suna ta cin soyyayrsu yayin da Mubina take ta bankar magunguna na hana d'aukar ciki,tayi wata mummunar kiba shi kuwa Oga Nasir yayi wata kib'a shima yayi haske kyawunsa duk ya fito gayu da ak'idun turawa sun kara nun kuwa akan nada, a zahiri ka kalleshi zaka ga kamar babu abunda ya dame shi,a mma a zuciyarsa shi kad'ai yasan damuwarsa,watansu uku da kwana bakwai suka dawo,duk wata ordar da yayi dama tun satin da ya wuce a ka shigo da ita, saboda haka shi kad'ai Abbas yake jira ya dawo sufara raba kaya, kwanasa hud'u da dawowa da yamma ya shirya tsab ya nufi gidan Momy, tunda Tony yayi parking din motar ma aikatan gidan suke sauraren suga waye zai futo saboda ganin wata shegiyar mota sabuwar shugiya, fara kall!! da ita, Giss ne ya fito ya bud'e masa k'ofa ya zuro kafarsa wacce take sanye da wani uban takalmi sau ciki, futowa yayi, Wanda yayi dai-dai da futowar Maryam daga shashen su taje ta gaida iyayen ta,hannuta rik'e da hannun karamin kaninsu,
Idanunnsu ne suka had'e guri guda, cikin dumbun mamaki take kallon yadda ya sauya sai kace wani Bature abunka da farar fata hatta gashin dake kansa sai da ya sauya, badan tayiwa ancle din farin sani ba,da sai tace bashi bane,saboda sauyawar da yayi, shi kuma babu abunda yake kallo a jikinta sai cikin jikinta ganin yadda ya tasa har ana ganinsa, nan take yanayin fuskarsa ya sauya ya sha kunu sosai, cikin yanayinn taf
iyarsa ya nufi part din Momy,Maryam taga lokacin da ya sauya fuska saboda haka kawai sai ta juya, ta koma idan ta futo
Domin bata san irin tarbar da zai mata ba, gashi tasan Momy tana fushi dashi kuma bataso Momy ta dunga yi masa fada a kanta,
Momy na sama lokacin da ya shiga farlo kai tsaye can ya nufa, tana zaune kan dadduma tunda ta idar da sallahr la'asar take lazimi tana sanye da hijab a jikinta yayi sallama ya shiga
Dago kai tayi tana kallonsa batare da mamakin komai ba kawai tafara yi masa kallon rashin sani.

Ganin irin kallon da Momy take masa ne yasa jikinsa yin sanyi ya tsaya bakin Kofa ya cire takalmin sa ya shiga da sallama.

Ciki-ciki ta amsa masa yazo ya zauna kusa da ita, yayi shiru itama shiru tayi masa kusan mintuna goma tukkuna tagama tayi addu'oi ta shafa sai ta mike tana ninke dadduma.

Kafafunta ya rik'e da duk hannuwanshi biyu, ya karyar da kai gwanin tausayi yace"Momyna, na dawo da fatan na same Ku lafiya"?

"Lafiya lau muke Son ashe tafiya kayi babu labari"
Cikin gatse tayi masa maganar.

"Momy naje Japan ne yau wata na uku da kwanaki yau kwanana hud'u da dawowa"
"To Allah ya taimaka"
Abunda tafad'a kenan ta fara k'okarin cire kafarta daga hannusa,sakintq yayi ya mike ya zauna gefen gado, yana kallonta ta aje dadduma ta nufi Kofa,da sauri ya mik'e yaje ya tari gabanta yana marairaicewa yace"Momy please,kiyi hakuri da zan tafi ban fada miki ba,naga lokacin kina fushi dani"
Momy ta kalleshi babu yabo babu fallasa tace"Ai ban isa ba domin ban kai wannan matsayin ba,ni bani hanya in wuce malam"
Hannuta guda ya rik'e tamau suka sauka kasa tare.
[13/08, 02:07] BintaU Abbale Zamani Wrt Marubuciya: *YARO DA KUDI*
*167*
Rarrashin Momy tasa yake, tak'i saurarensa, tace"Tunda ka nuna min ban isa da kai ba me zanyi maka yanzu Myson wato har yanzu ka kasa gane rayuwa lokacin da dady dinka ya mutu ka shiga nutsywar ka ashe duk ta gaibu ce, saboda giyar kudi suna d'iban ka,kaki ka tsaya kayi karatun ta nutsu kayi aiki da hankali kullum kana shirme da neman mata,Myson sai kaje ka kwaso wa kanka cuta ka dorawa baiwar Allah Maryam"
Yanayin fuskarsa ya sauya yace"Momy itace tace miki ina neman mata"?

Harararsa Momy tayi tace"Har sai tace min da dai bansan halinka bane"
Ganin Momy din tana ta fada taki ta saurare shi yasa ya fara bata hakuri tare da amsa mata laifin da take tuhumarsa da shi.

Da k'yar ta sassauta masa tace"Tunda ka karyata ni bari Maryam ta shigo ai akwai sauran photo guda Wanda bata yaga ba,zaka gani ai"
"Shikkenan Momy naji nayi kiyi hakuri insha Allah bazan kara ba"
Shiru tayi masa na minti biyu yace"Momy ke a ina kika samu hotan"?

"Abokin shashancin naka ne ya kawo min har gida"
Cikin damuwa yace"Waye shi Momy"?

"Anwar ne"?

Ranshi yaji ya baci amma saboda b'acin rain Momyn yasa bai nuna nasa ba yace" Momy ashe kin manta dabi! na da Anwar da har zaizo ya fada miki magana ki yarda da ita"?

"Kaga kawai kayi min shiru babu wata kalma da zaka fada in yarda da ita"
Shiru yayi kawai yana kallobta
Wayarta ta d'auka tana kiran Maryam, tace"Dota kizo gida mijin ki ya dawo
Lokacin tana gaban aunty tana cin gyad'a dafaffiya wacce aunty da dafa mata, duk jin jikinta take babu dadi tunda suka had'a ido da ancle shikkenan ta rasa nutsuwar ta.

Wayar ta d'auka ta karata a kunnenta sallama tayi cikin nutsuwa,
Momy tace"Dota kizo mijikin ya dawo"
Dake muryar wayar a bud'e take yasa aunty taji, abunda Momy tace fuskarta ta saki sosai tace" Ashe baya gari shine baki fada ba"
Murya a sanyaye tace"Eh aunty baya gari yanzu da zan shigo ya dawa"
Cikin b'acin rai aunty tace"Kince baya gari kuma kince ya dawo yanzu me makon ki tsaya ki tarb'e shi,wai ke yaushe zakiyi hankali ne"
Shiru Maryam tayi kanta a sunkuye
Aunty tace"Ai zaman banza kike a nan kawai ki tashi ki tafi"
Mik'ewa tayi tana mata sallama, aunty tace"Ku d'ibi gyadar ki kaiwa Momy ko zatayi sha'awar ci"
Wata samira Maryam ta d'auka kicin din aunty ta cika da gyada da zafinta ta futo tai mata sallama.

Lokacin da ta isa part din Momyn Nasir har yanzu na gaban Momy yana aikin rarrashinta,inda Momy tace masa ta yafe masa ammafa sai ya nemi afuwar matarsa kuma su zauna lafiya.

Duk ya dauki alkawarin hakan shine ta sakar masa jiki suke hira sama sama,haka Maryam din ta same su
Momy ta amsa mata sallama ta shiga ta zauna cikin kujera tana dan ya mutse fuska tace"ancle INA wuni ka dawo lafiya"?

Wani irin kallo yake Binta dashi me d'auke da ma'anoni daban-daban.

Yace"Princess kina lafiya ya jikin ki"?

"Naji sauki"
Tafad'a cikin mamaki ,ganin yadda ya sakar mata fuska ba kamar dazu da suka hadu ba lokacin da zai shigo.

Yana mata wani irin kallo yace"Zonan in duba ki,to tunda kince lafiya"
Sunkuyar tayi tana jin nauyin Momy,tasan rashin kunyar ancle zai iya yin fiye da haka.

Hararsa Momy tayi tace"Baka da kunya kai kam, Dota tashi ki bashi abunci nasan babu komai a cikinsa sai shirme.

"Momy ni a koshe nake" yafada cikin shagwab'a
Momy tace"baka isa ba dole kaci abunci yanzu"
"Shikkenan Momy zan ci amma sai dai in ta bani a baki"
Momy tace "Wannan duk me sauki ne,Zaki bashi ko Dota"
A nutse Maryam tace"Me zai hana Momy zan bashi nima bana son yana zama da yunwa"
Mik'ewa yayi ya nufi daining Maryam Din tabi bayan sa.

Tafara had'a masa abunci kenan ya kalleta sama-da kasa yana jin wani mugun daci cikin zuciyarsa yanzu da gaske yarinyar nan so take ta rusa masa tsarinsa,lallai wankin hula yana so ya kashi ga dare.

Kasa -kasa Dan kar Momy taji yace"Ke jeki dauko min wannan hoton da kuka ce Anwar ya kawo muku, munafuka kawai,me fuska biyu, cikin mamaki Maryam ta kalle shi cikin zuciyarta tace akwai babban munafuki me fuska biyu irin ka, a fili kuwa cewa tayi "Wannan hotonan dakake magana a Kansu na yaga su.

" Momy tace akwai guda d'aya shi zaki dauko min ai"
"OK bari in gama had'a maka"
Tafad'a babu wata damuwa tare da ita, shifa gani yake kamar tsari ne sam be yadda da wani photo ba,
Tana gama had'a masa ta bar gurin,
Sama ta nufa minti biyar sai gata ta sauko da hoton a hannusa,mik'a masa tayi,tayi tsaye a kansa, muryarta a dusashe tace"Ko zaka ce ba kai bane,ko za kayi mana rainin hankali irin Wanda ka saba,wannan dai mungani ga zahiri nan".
[13/08, 02:09] BintaU Abbale Zamani Wrt Marubuciya: *YARO DA KUDI*
*169*
Sosai Anwar ya kwanta jinya wacce ta d'auke shi tsahon lokaci, shi ko Nasir rayuwar sa ya cigaba,abun mama Anwar da Indan-dan d'in suka kasa d'aukar mataki da indan-dan cewa yayi bazai yadda ba Anwar yace masa dole su hak'ura domin idan sukace zasuja da Nasir din sune a kasa haka sukq hak'ura sukayi jinyar Kansu,domin Nasir din duka sosai yasa a kaiwa indan-dan Wanda ya sab'a masa kammani.

Bayan wata biyar
Lokacin cikin Maryam ba a gane shi ba,gashi ya fito sosai tayi wata irin kumbura Momy tace"aje ai mata Scaining dole Nasir yazo ya d'auke ta sukaje Hospital akayi mata scaining baby lafiya Lou da alama zata haifi yoro me kuzari.

Sai wani shan kunu yake, haka sukaje suka dawo Sam baya son kallon ta saboda yadda tayi wani muni jikinta duk ya shika.

Yana aje ya juya ya koma harkoinsa, kullum in zai futa zaizo gidan Momy su gaisa tilas Momy zata basu guri wai suyi hira irinta miji da mata,
Maryam kanta na kudu NASA na arewa haka suke magana, sai dunga nuna mata iko da gadara wani lokacin in ya nayi sai ta share shi ya karaci surutunsa ya futa
Shi da Mubina kuwa sun shaku sosai inda suke zuba love kamar babu Gobe
Wata ranar juma'a da dare Maryam ta tashi da ciwon nakud'a shuru tayi bata sanar da Momy ba, har garin Allah ya waye lokacin ta galabaita sosai.
Chapter 77 · 0% Book details