← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 80

Sashe 29

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasir da ba'a fada masa ya kyale ,ya kalli Uncle din nashi sheqeqe ,yace"in har dady ya mutu ,to kwananshi ne ya kare bawa bai isa ya kashe wani ba, in lokacin mutym yayi dole ya mutu,sabida haka kar ka kuma dora min,ai ba Ku fini jin ciwonsa ba"
Dukkaninsu mamakinsa suka yi to amma dake sun San halinsa ,babu Wanda yakara cewa ufan a cikinsu,suka kama Dan uwansu , da nufi tafiya asibiti
[06/06, 00:44] +234 808 996 5176: [15/05/2019 1:57 PM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*
*73*
Hankali a tashe Malam Ya'u ya karaso gurin da nufi kama Alh Huseen ,Nasir ya daka masa wata muguwar tsawa tamkar bai san daga inda yake ba tace"karka kuskura ka ta bashi Malam ,duk wani surkule irin naku na fulani kaje ka kwance ,shi sabida dama na lura tun tuni kuka asirce dady ,shiyasa kwata-kwata bayason Bacin ranku kai da iyalinka, sabida haka ka rubuta ka aje ,zamanka a gidanan ya kare"
Mahaifin Hanifa yace"kayi min dai-dai Nasir dama nima tuntuni nake zargin haka, dole subar gidan nan,ni ina zarginsa gurin rashin lafiyar dan uwanmu,dole ya bar gidan domin ba mu hada zuri'a dashi ba ,
Malam Ya'u yayi tsamo-tsamo tamkar Wanda a ka watsawa ruwa a jiki ,sai gumi ne yake zuba a jikinshi, lokaci guda ya muzanta,bakinshi yana rawa yace"ku fahimce Alh babu wannan abu mai muni a tsakanina da Alhji Huseen sai alkairi,uba na dauke shi ,babu cutarwa tsakanina dashi sabida yayi min abinda bazan taba mantawa ba a rayuwata"
"Rufe mana baki dattijon banza da Wofi"!!

Nasir ya katseshi cikin tsageranci ,yana masa wani banzan kallo"
Maryam ranta yayi mugun baci!

A gabanta Nasir yake kiran Ubanta da dattijon banza Lallai bazata lamunta ,dole a kwai ranar da zata amayarwa da uncle duk cin mutumchin da yake mata
Duk wannan abinda yake faruwa Dady ya naji ,ranshi yana mugun zafi,da irin rashin kunyar da Nasir yakeyi,anrasa mai tsawatar masa ,a cikin "yan uwanshi,sabida sunajin tsoransa,wanan yana nuna cewar ko mutuwa yayi haka zasu wofintar da jininsa,tabbas zumunci bai ce haka ba tunda shi ba haka ya musu ba
[15/05/2019 2:18 PM] Binta U Abble: Tari! ne ya sarqe shi ya riqayi babu kakkautawa ,nan da nan suka mayar dashi suka kwantar,Nasir ya nufi frji da sauri ya ciro ruwa mara sanyi sosai yazo ya na sama a baki,
Dady ya ki karba ,idanunshi tsaye kan Malam Ya'u, yana kallonshi ,da kyar ya daga hannunshi da yayi masa bala'in nauyi yayi masa alama yazo gareshi ,Malam Ya'u ya karasa kusa dashi jikinshi a sanyaye,yace "sannu Alh Allah ya baka lafiya"
Dady ya bude baki da kyar yace"Malam Ya'u ko bayan babu raina ban amunce ka bar gidanan ba ,shashen da kake ciki na mallaka maka shi ,halak malak, sannan , inaso kayi min wannan alfarma ga amanar Nasir nan na damka maka ita a hannunka kar ka wofintar da shi,ka cigaba da yi mishi addu'a Nasir naka ne dama can "
Malam Ya'u yace"na karbi Amana Alh ko da ranka ko babu jinnika ba abin gudu bane a gareni,in sha Allahu zaka tashi ka cigaba da rayuwa, nagode da karamchin ka a gareni ubangiji Allah ya biyaka da aljanar fiddausi"
Cikin zuciyarsa yace ameen,sannan ya kamo hannun mahaifin Abdul latif ya ruke gam!

Yace"ni Hussen in dai na isa da kai da abinda ka haifa ,ina so ko bayan babu raina ,ka daura auran Abdul da Maryam,domin ina sha'awar hada zuri'a da ta Ya'u, da naso Nasir ne ya samu wannan garabasa domin auran kamilar mace irin Yarinyar dace,dukkaninku baza Ku fahimchi haka ba sai nan gaba, Nasir ya fadamin qeqe da qeqe ban isa dashi ba ,kuma bazai bi umarnina ba, sabida haka da wannan bakin cikin zanmu a rayuwata ,Nasir nagode nagode, nagode, tari ya rurnikeshi,!!

Hankalin Nasir yayi mugun tashi, kaddai ,dady ya sauki maganar su ta dazu da zafi haka,har ta janyo masa tashin ciwonsa,shifa yafadi hakane kawai dan ya bata masa rai, amma kwata-kwata-ba gaskiyar abinda yake zuciyarshi ba kenan,
Kafin ya dawo daga tunanin nashi,yaji Momy ta rusa ihu,yayi da Mahaifin Mubina,yake Fadin *innalillahi wa'inna ilayi raji'un*
Dady ya amsa kiran Ubangiji
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [16/05/2019 9:26 AM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*
*74*
Nasir ya fasa wani ihu yayi kan dadynsa ya ruqunqume shi,kuka ya kece masa ,cikin dimuwa da fitar hayyaci ,yake fadin *innalillahi wa'ina ilayi raji'un*
Dady kar ka mutu, bakace ka yafe min ba, dady ka tashi in fada maka abinda yake zuciyata duk kanin abinda nafada maka abaya ,karya nakeyi wallahi,dady ina mutukar kaunarta ,har a cikin zuciyata,dady in kayi min haka ina zan sanya rayuwata pls dady karka yimin haka rayuwata nima tazo karshe ban da amfani a duniyar nan,kafadamin mai kake bukata nayi maka shi yanzu!!!

Nasir kuka yake sosai da sosai ,duk ya gigice yafita hayyacinsa, in banda gumi babu abinda yake zuba a jikinsa,yabi ya rungume gawar dady ya hana kowa ya kusance shi,da kyar!

Malam Ya'u ya karaso gurin gami da dafa kafadar Nasir din cikin dauriya da jajircewa ya ce"kayi hakuri Nasiru Allah Ubangiji ya amshi Alh cikin aminci da yaddarsa, ya mutu yana kalamar shahada,yanzu babu abinda yafi bukata da kai sai addu'a kaji"
Nasir ihu!

Yakeyi yana sambatu da'alama kwakwalwarsa a lokacin ta daina aiki,domin kwata kwata bai ji abinda Ya'u yake fada ba.

Maryam ko yanke jiki tayi tafadi, ta suma!!!

Kafin kace kwabo gidan ya hautsine da hayaniya, tuni Nura ya fita ya sanar da Sucurty da ke waje abinda ke faruwa a cikin gida,
Aunty ko tana bangaransu duk wannan abin da yake faruwa bata sani ba tana kchin tana hidimar Dora abincin rana,taga Malam ya shigo mata da yarinya ranga ranga,
Salati ta tafka tana tambayarsa abinda ya faru ,sabida dama tasan da batan da Maryam din tayi na awanni biyar da suka wuce,Malam Ya'u yace"babu lafiya Suwaibah ,muna cikin tashin hankali,Allah yayiwa Alh rasuwa
Gigicewa aunty tayi domin duk a zatonta mahaifinta yake nufi ,sabida tasan shima ba shi da koshin lafiya.

Kuka ta fashe dashi tace "shikkenan baba wahala ta kare"
Ganin bata fahimci abinda yake nufi ba,yasa ya tsaya yayi mata bayanin komai,aunty ta rika salati tana sanar da ubangiji,da gudu tayi dakin ta zaro hijab tana ,nanata innalilahi a fili,take tambayar mai ya sameshi,shiru Malam yayi mata shi dai yana ta tasbihi cikin zuciyarsa, tare suka shiga farlou, har yanzu Nasir na rungume da gawar Mahaifinshi ,yanzu.

Ya dai na zubar da hawayen sai kukan zuci yakeyi kwata kwata ya hana kowa kusantar gawar ,har Momy dinsa, dake kusa dashi ,ita kuma a lokacin Allah ya sanya mata juriya,kwata kwata idanunta sun bushe ,babu hawaye ko days,amma kana kallonta kasan tana cikin dimuwa!

Da tashin hankali
[16/05/2019 9:43 AM] Binta U Abble: Tace"My Son shiyasa kullum nake fada maka ka kiyaye bacin ransa ,sabida kasan yana da lalura,kaki ji ,ko ka gani yanzu yazo ya tafi ya barmu mai zakace min ,my son ,mai zakace min!!

Momy tafada muryar ta tana karkarwa,
Aunty tazo ta dafa kafadar Momy tana zubda hawaye tace"Hajiya Kiyi hakuri kinji,dama Allah ya kaddara lokacin Alh yayi yanzu bawa bai ta kashe wani ba face sai lokacin sa yayi, kiyi hakuri ,kiyi mishi addu'a Allah ya jikanshi Hajiya Allah ya sanya mana hakurin jure rashinsa da mukayi.

Sai lokacin hawaye ya kecewa Momy ,tafadi a gurin ragwajb ,tana kuka, cikin tashin hankali da damuwa take fad in"innalillahi wa inna ilaihi raji'un
Aunty tazo ta dafa kafadar Nasir tace"dan gidan aunty kayi hakuri kaji ko ka fawwalawa Allah kowa na hakane,don Allah ka saki kyale Alh ayi masa suttura ,duk wannan abinda kakeyi bazai sa dawo mana dashi ba"
Nasir ya zubawa aunty ido yana kallonta ,bakinsa dai motsi yakeyi ,da kyar ya samu ya finciko maganar ,yace"aunty dady ya mutu,!!

Wancan yarinyar ,ce tayi sanadi ni babu ruwana,sabida lafiya kalau na tafi na barshi da'ita,sabida haka ,duk yadda zanyi sai nayi gurin ganin na wulakantata ,tunda tayi sanadin kashe min mahaifi.

Aunty Sam!!

Bata fahimchi maganarsa ba ,ta lura kwata kwata baya cikin hankalinshi,tace"eh nima Na amince Auncle ka dauki mataki kan wanda ya zalunce ka,amma yanzu abinda nakeso dakai ka saki Alh ayi mishi suttura kaji ko"
Nasir yayi zakwado!!

Yana bin dady dake rungume a jikinshi da kallo vakinshi sai motsi yakeyi,yanzu wai da gaske ne dady shi ya mutu !!

Ina karya ne!

Abinda ya fada kenan da karfi!!

Sai ya fara Jan numfahi!!

Da karfi ,kan kace kwabo ya afka kan dady din nasa ya suma!!!

Guri ya hargitse da salati,Ya'u yazo ya janye Nasir ,daga kan dady,yayinda "yan Uwan dady din suka samu damar janye dan uwansu,domin sutur tashi,
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [16/05/2019 8:45 PM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*
*75*
Momy ta kidime tayi kan Nasir din tana kuka sosai ,tamkar wacce tasamu tabin hankali take cewa "My son kai ma zaka tafi ka bar ni ne, ta kamashi sai jijjigashi takeyi tana kuka da sauri Malam Ya'u yazo da ruwa mai sanyi cikin gora ya bude ya watsa wa Nasir din ,cikin zuciyarsa yana ta nanata Kalmar innalilahi
Nasir ya mike a zabure!! yana dube dube babu dadynshi a gurin ya mike da sauri ,jiri! ya debeshi ya yar kan kujere ,sai ya dafe kanshi da hannunshi guda,ya na furta,kalame "Ya Allah!!

Momy da aunty sai tausarsa sukeyi,kar ma dai aunty taji labari,shidai idanunshi suna rufe,kwata-kwata hankalinshi da tunanunshi baya kansu,zuciyarsa take fada masa kayi rashin mahaifinka har abada Nasir,sai ya karyar da wuyanshi jikin kujera ,hawaye yana zirarowa daga idanunshi da suke rufe,
Kankace kwabo mutuwar Alh Huseen ta karade birni da kewaye sabida dukkanin wanda ya kwana ya tashi a garin kano da kewaye babu Wanda bai sanshi ba idan ma baka taba ganinshi ido da ido ba to za ka ganshi a jarida ko gidajan TV ko tashoshin yada labarai,sabida yadda yayi suna gurin taimakon marayu da nakassasu gami da taimakon talakawa ,Sam dukiyarshi bata rufe masa ido ba sabida haka ,kofar gidan damqam!
Chapter 29 · 0% Book details