← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 80

Sashe 13

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taci gaba da cewa ,Dama Dama Wannan Abokin nashi ne,sai tayi shiru takasa karasawa,
Ina jinki ya kikayi Shiru Momyn tafada"
Shine Yake kulani Momy nikuma bana so tafada kanta a kasa,
Momyn tace"To ae kina da gaskiya Mutuncin "ya mace tsare kanta babu ruwanki dashi ko ya kulaki ,gaisuwa kawai na lamunce kiyi dashi kinji ko kuma zanyiwa Nasir magana tunda ba kyaso tayi masa magana duk inda ya ganki Kar yakara shiga lamarinki"
Gabanta yafadi jin Abinda Momyn take fada,
Da sauri ta dago kai tace"A,a Momy ba sai kin yiwa Ancle maganar ba Dan Allah"
Harararta Momyn tayi kadan tace"ae dole in yi mishi magana yajawa Abokinshi kunne domin a kanki zan iya batawa dashi"
Sunkuyar da kai tayi tana Murmushi kadan tace"Dan Allah Momy mubar maganar bana so ki batawa Uncle rai"
Dariya Momyn tayi gami da Mikewa daga kan daddumar da sukayi sallah A kanta tace" in dai a kanki ne ran Nasir zai baci kuwa ,
Mikewa tayi ita ma tabi bayan Momyn suka sauka kasa ,a tare Maryam din na kokarin fita da niyar tafiya bangaransu Momyn ta dakatar da ita,tace Lallai sai ta tsaya sunci Abinci tare ,ba yadda ta iya haka ta bi bayan Momyn can dainnig in da kayan Abinci ke jere iri iri na haduwa na Alfarma,
Momyn ta hada Mata komai tsaf ,Cikin nutsuwa Maryam tafara cin Abincin suna hira da Momyn kadan kadan ,sai da Momy ta tabbatar da Maryam ta koshi sannan ta kyaleta ta tafi bangaransu.

Lokacin da tashiga shashin nasu Ana sallahr isha'i Aunty da su Nafi'u duk sallah suke ,sabida haka Alwala ta daura ita ma tabi sawun su.

Aunty na idarwa tafara hidimar Zubawa yara Abinci ,ta kalli Maryam dake zaune kan dadduma bayan ta idar da sallah tana Addu'a ,"kefa a zuba miki ?

Nasan dai kinci gurin Momynki ko?

Daga kai Maryam tayi A nutse tace wallahi kuwa Aunty a koshe nake Amma da safe naci dumame dama yafi dadi"
Tabe baki Aunty tace Allah ya kaimu . mai kika tsaya yi a ne a can?
,,,,,,,*
[23/03, 00:15] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*YARO DA KUDI*
writing By*
~*Binta Umar*~
~*Maman Abdul Wahabu*~
*MRS AHAMAD GWADABE*
_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176
_INA MIKA SAKON TA'AZIYATA GA "YAN UWA DA IYALAN ALHJI RUFA'I GWADABE ,MUNA ADDU'AR ALLAH YAJI KANSHI YA GAFARTA MASA ALLAH YA YAFE MASA ALLAH YA KYAUTA TAMU BAYAN TASU
Aunty Momy ce ta Sani gyaran dakin Ancle Maryam tafada cikin Nutsuwa.

Ayya to ae kin kyauta Aunty tafada.

Ancle din ma ya kwana biyu bai shigo min ba Aunty tafada tundai ranar da yadawo"
Ita dai Maryam bata ce komai ba domin Aunty bata son Laifin sa ko kadan.
****************
Karfe takwas saura na safiyar Litinin Maryam tsaf cikin Unporm dinta na Makaranta, Tana zaune gefen Babanta suna karyawa a gurguje ,ta kalli su Naf'iu tace "kuyi sauri Wallahi idan ba hakaba in tafiyata"
Ya Maryam ni dai naga Mutafi kawai Mubarshi tunda kullum sai yasa munmakara,
Duka Nafi'u ya kaiwa Miftahu jin Abinda yake cewa yace "bana hana yimin Rashin kunya ba"
Maryam tayi sauri ta riqe hannunsa tace "ai ba karya yayi maka ba ka dakeshi sai na rama masa"
Dariya Babansu yake musu yace"kai Miftahu kafiye tsokana kai kuma Nafiu sangirma kamar gyambo"
Aunty tace "Haka sukeyi si tayin koka ye kokayen shashanci"
Mikewa Maryam tayi tana gyara books din hannuta gamida da gyara jakarta tace"ai sai Ku tashi Mutafi ko"
Duk suka miqe a tare suna yiwa iyayen nasu Sallama.

Mi kewa Malam Ya'u yayi shima ya biyo bayansu Dan haka yake musu haka yake rakasu har kusa da makarantar sannan ya dawo gida dake makarantar babu nisa da gidan Alhji Huseen din.

Suna fitowa harabar gidan sosai Nasir ya fito daga part dinshi jikinshi sanye da kayan motsa jiki jikinshi a Murmurde ,sakin Fuska yayi lokacin da Idonshi yayi tozali dasu Nafi'u Yace "Morning My boys gami da dumqule hannusa kamar yadda yake musu ,Da sauri Nafi'u ya karaso yana dariya ya daki hannun Sosai yace"Morning Ancle katashi Lafiya"
Kalau Aboki na Nasir din yafada yana Jawo hannun Miftahu suna gaisawa,
Farin ciki ne ya Lullube Malam Ya'u yana tsaye Fuskarshi tamkar gonar auduga Dan dadi.

Nasir ya Mika masa hannu kamar ko da yaushe yace "Arrama Barka da Asubah"
"Barka kadai Nasiru katashi Lafiya"
"Lafiya Alhmdilahi"
Yace "kuzo in aje Ku a Skull din ko"
Yayi can inda motarshi take a je.

Ayya ai da ka barsu ma Nan makarantar tasu take bakin hanya"Malam Ya'u yafada
Ai fita zanyi Arrama Kawai su shigo na sauke su Nasir din yafada,
Ko gama rufe baki bai yi ba Miftahu yayi gaba dama yana kwadayin shiga Motar Ancle din.

Cikin sanyi Murya Maryam tace"Ancle ina kwana"?

Yanajin ta ya share ta,bata daddara ba ta kara maimaitawa,
Shiru yayi a karo na biyu yana kokarin bude mota Malam Ya'u yace' Maryam na gaishe da kai Nasir"
"Ok ya joyo Ya Dan kalli inda take yace" Lafiya Maryam yaya kike?

Dadi taji ganin yadda Ancle din ya Amsa gaisuwarta.

Tace"lafiya lau Ancle ,banza yayi da ita ya tada motar bayansu Nafiu sun shiga ko sauraron ta bai yi ba yafara kokarin tafiya.

Tace "Ancle ban shiga ba fa"
Wata harara yayi mata yaja tsaki kadan Dan ganin Malam Ya'u na gurin ya daka ta tashiga tukkuna sannan yaja motar
Malam Ya'u ya karasa bakin get din yana kokarin bude masa kofa,
Ya fice daga gidan.

Yana fita ya tsayar da Motar ya waigo yana kallonta A wulakance ,yace ke saukar min A mota"
*BINTA UMAR ABBALE*
_MARUBUCIYAR_
_*NANA KHADIJA*_
_*YARO DA KUDI*_
_*GIMBIYA BALARABA*_
[26/03, 01:44] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

YARO DA KUDI*
writteng by*
*Binta Umar*
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~
~*MRS AHAMAD GWADABE*~
_WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU_
08089965176
Diri diri cewa Maryam tayi jin Abinda yake cewa sai tasa masa ido tana kallo cikin tsoro!

Ya buga mata wata muguwar tsawa "get out nace kin tsaya kin sanya min ido shegiya Mayya mai kama da Aljanu kici kanki kurwa kurr!

Yafada A harzuqe!

Da sauri Maryam tabude murfin motar tafice tana jin wani mugun bakinci idan anyi duniya Dan Manzon Allah baza ta qara kula Uncle ba ko me za'ayi kuwa sai dai Aunty ta daketa a kan taqi kulashi.

Tana sauka ko sakon daya bai qara ba yafigi motarsa hade da bula mata kura!

Jikin Unporm,
Wani hawayen bakin ciki ne yafara fita daga idonta tanayi tana karkade jikinta kana takama hanyar tafiya kamar yadda suka saba tunda dama skull din bawani nisa da gida.

Kan ta karasa skull tayi kokarin daina fitar hawayen Amma kana ganinta kasan tayi kuka sabida yadda idonta yayi ja!

Sukuku su nafi'u sukayi ganin Abinda Ancle yayiwa Yayarsu ,Miftahu yace "Uncle Yaya Maryam tayi maka Laifi ne?

Yana kokarin kunna kida kamar yadda yasaba yace"No" Babu Laifin da tayi min Abokina Kawai bana Ra'ayinta ne Na tsaneta!

Miftahi"yace Uncle mai tayi maka katsane ta mu kuma ba ka tsane mu ba?

Dariya yasa kadan yana mamakin tambayar kwakwa irin ta yaron yabashi hannu suka tafa yana dariya yace" Ai ba lallai sai mutum yayi ma laifi ba zakiji baka sonshi boy Yayarku tsoro take bani idan nakale ta tamkar Aljana"
Dariya Nafi'u ya qyalqyale dashi gami da dukan kafadar Nasir din sai kace wani sa'ansa yace"Lallai Aboki Yaya Maryam din ce Aljana duk kyawunta kaji kuwa yadda a skull a ke maganar kyanta A kwai Ancle Bash dinmu kullum sai yayi mata Magana bata kulashi bakaji yadda Abokai na suke cewa wai duk tafi mu kyau.

Wai suna kama da wannan "yar india Ashwariya" idansu iri daya Dan Na Yaya Maryam din har yaso yafi na Aswariyyan blue,
Tabe baki Nasir yayi yana girgida kai Alamar yana jin dadin Music din dake fita kasa kasa cikin motar tasa yace"gaskiya waddan nan Friends din naka sun cuci Aswariyya da suka hadata da wan can tab!!

Da nasansu sai na Zane su da bulala domin sun batawa star ta kyawunta"
Yafada yayin da yakeyi parking.

Daidai get din Makarantar.

Dariya Nafi'u yayi yana bude mota yace"to Uncle ko in kira makasu ne"
"Aa No" barsu kawai Zamu hadu ne wataran Amma kafada musu duk sanda muka gadu sai Na Zane su da kyau yafada Cikin sakin Fuska da barkwanci
Dariya yaran sukeyi suna kokarin daukar Lounch book din su Ancle din ya fito da wasu tarin Sweet masu bala'in tsada da dadi Dama ba ya rabo dasu cikin motar kasancewarsa ma'abocin son kayan zaqi ya basu yace"gashi nan kuje kura ba ko"
Cikin nutsuwa suka karba kana suka daga masa hannu suka nufi cikin makarantar,
Yana kokarin juya mota Maryam ta karaso jikinta a sanyaye ko kallon in da Motar take ba tai ba kai tsaye cikin Makarantar ta nufa,
Shi ma ya ganta yayi saurin dauke kai daga kanta gabansa na faduwa kadan bala'in jin haushin yarinyar yakeyi bai San meye dalili ba ,ko kadan bai tausaya mata ba tafiyar dasu kai suka barta.

Yaja Motarsa ya bar gurin Cikin Nishadi da'Alama yanajin dadin duniyar"
Tana Shiga cikin Makarantar Uncle bash ya tare kamar ko da yaushe,sai ta saki Fuska tace"Uncle ina kwana?

"Lafiya kalau habibty Yau kin Makara da yawa fa Yafada idonshi tsaye kanta ji yake tamkar ya lashe ta ya huta!
Chapter 13 · 0% Book details