← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 80

Sashe 65

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yadda ta same ta cikin mawuyacin hali shi yayi mugun daga hankalinta, da kyar ta samu ta shirya ta ta kamata a daddafe suka fito harabar gidan, suka nufi inda motar take, Momy tace"dole muje can guri na in sa miki ruwa,da gani babu ruwa a jikinki,ga rashin karfi da kuzari"
Maryam babu bakin magana,sai nishi takeyi,
Momy ko addu'a take cikin zuciyarta Allah yasa abunda take hasashe ga Maryam din ya tabbata.
[25/07, 23:56] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*136*
Momy ta kwantar da ita cikin kujera ta nufi bedroom dinta ta dauko kayan aiki, a nutse ta sanya mata ruwa, ta rage mata karfin AC dake farlon, ta mayar da kayan aikin ta dawo farlon ta zauna kusa da Maryam din, wacce bacci yafara fuxgarta,
"Ina Myson din, na kira wayarshi tun jiya daddare misalin sha daya na daran jiya naji a kashe,kuma yau ma na kirashi da safe stiil wayar a is swich of, nan na tabbatar babu lafiya"
"Momy nifa ban san inda yake ba mybe ya futa da wuri ko wayoyin nasa suna gurin yaranshi"
"Anya kuwa"
Momy tafada cikin mamaki!

"Bari in kara kiranshi mugani"
Maryam shiru tayi mata kawai domin ta kanta takeyi, bacci ne ya dauke ta
Yana can getshouse dinshi kwance kan bed daga shi sai gajeran wando sai zukar sugari yake, tun jiya yakeyin abu daya sugari ya sha babu a dadi,ko da yaje muwala hotal din kasa shan Wsky yayi yana kallo a na sha, daga yayi yunkurin dauka ya sha sai zuciyarsa takwabeshi,nasihar Dadynshi ta fado masa sabuda haka ko awa guda bai yi ba, ya baro gurin ya yada zango a gidanshi na hutawa,tunda ya kashe wayarshi, bai kunnata ba sai da safe misalin, tara shaura kwata,
Yana kunnawa kiran Momynshi ya shigo,
Maganarshi a sarke tace"Momah"!

Yadda ya kira sunan nata abun ya taba mata zuciya, lokaci kan kani ta fahimci yana cikin wani hali,babu da abunda tafara tambayarsa dashi sai "kaci abunci"?

" Momy wane abinci kuma da sanyi safiyar nan"
yafada yana kashe guntuwar tabar da yake sha a wani karamin plete wanda a ka tanade domin hakan.

"Ok ina so in ce kayi breakfarst ne,naji muryar ka wata iri"
"Yanzu zanyi Momy"
yafada yana kokarin gyara muryarsa dan kar ta gane"
"Ok hada ni da Maryam mu gaisa domin mun kwana biyu bamu hadu ba"
Gabanshi yafadi, amma dake namijin duniya ne, sai yace"Momy kin ganta nan tana bacci sai dai in ta tashi sai ta kiraki"
Murmushi Momy tayi, tace"Myson yaushe ka koyi karya abunda ba halinka ba"
Dariya yasa yace"Momy a ina na miki karya"
"Gashi kuwa kayi, ta tabbata kenan ba'a gida ka kwana ba domin tun misalin karfe shida da arba'in da biya nake gidan ka,dalili Maryam ta kirani a waya bata da lafiya, karkaso kaga a halin da na risketa,Myso kanaso ka kashe musu yarinya ko"
Momy ta karashe maganar ranta a mugun bace!
[26/07, 01:47] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*137*
Mikewa yayi da sauri wayar na neman subuce wa daga hannunshi, yace"Momy ita ce tace miki bankawana a gida ba"?

"A'a babu ruwanta, nice nafada, sabuda ban ga motar da kake futa da ita ba, kuma in a gida ka kwana me yasa baka san bata da lafiya ba, yarinya saura kadan ruwan jikinta ya kare, wannan wane irin rashin imani ne"
"Momy bata fada min ba, kuma yau da wuri na fita tun asubah sabuda tarbar wasu bakinmu, amma yanzu naga komai yanzu zanzo,amma dai jikin nata da sauki ko"?

" Humm, Alhmdulilahi jikin gata nan na sanya mata ruwa, tana bacci, sai ka shigo"
ta karashe maganar tana kokarin kashe wayar
Mikewa yayi da sauri ya nufi toliet yayi wanka ya fito a gurguje ya kimtsa cikin wani mugun yadi mai uban tsada filtex ne milk colour yayi masa kyau sosai, ya taje sumarshi, yau har hula ya sa, zanna bukar, ya sanya farar kafarshi takalmi na zallar fata, kamfanin Gucci mai gidan dan yatsa,kafar tayi kyau cikin takalmin dake baki ne, sosai yayi kyau, ya fito wani babban mutum, wayoyinshi ya diba, ya futa, daga dakin
Giss ya na hango fitowarsa ya mike da sauri ya karasa suka jera tare,Ya bude masa kofa ya shiga shima ya shiga ya zauna, Tony ya ja motar suka fuce daga gidan.

Minti ashirin ne ya kaisu gidan, Tony yayi parking din motar, kafin Giss din ya futo ya bude masa tuni shi ya bude, motar ya futo,
Baban gida ne,da Malam Ya'u tsaye bakin get suna magana, Malam Ya'u kasuwa zai tafi ya tsaya suna gaisawa da Baban gida da yake Baban gida yakan fito ya zauna gurin sabon megadin su dan yi hira,
Yana daga inda yake tsaye ya daga musu hannu, gami dace"barkanku da asubah"
"Barka kadai Nasiru"
Malam Ya'u yafada yana mamakin irin gaisuwar da yayi musu kamar bai taba ganinsu ba,
Baban gida yace"
na lura har yanzu yaron nan haryanzu yana mana kallon kaskanci"
Murmushi Arrama yayi yace"Nasiru kenan, akwai lokaci, ina ganin har yanzu da akwai kuruciya a tare dashi, duk zai dai na"
"Allah ya kyauta"Nan sukayi sallam Arrama ya futa, daga gidan, da nufin zuwa kasuwa
Bacci take sosai kan doguwar kujerar dake farlon, Momy tana sama, Kyauta mai aiki ce kawai take shige da fuce a farlon tana aikace-aikacen ta, ya shigo farlon cikin sallama,
Kai tsaye idan sa ya sauke kan Maryam din tana kwance, har yaje ya zauna bai dauke idonshi daga kanta ba,
Da sauri Kyauta ta karaso gurin tana washe baki tace" Sannu sa zuwa Uban gida na,ai nace Yanzu Hajiyar ta hau sama,tana zaune tana jiran zuwanka ina jin wanka zatayi"
"Owk"
Abunda yace kenan, yana dauke kai, sabuda ya tsani shegan surutun irin na matar yanzu zata fara masa kankan ba, da fadi ba a tambaye ka ba
"Muntashi lafiya, Uban gida na"
Kallonta yayi fuska a ya mutsu yace"kalau kefa"?

Washe baki tayi tace"nima lafiya kalou, bari in kawo maka abinci"
"Kar ki kawo min komai, a kushe nake"
Yafada idanunshi kan Maryam dake faman mutsu-mutsu tanaso ta fuzge robar karin ruwan bata sani ba
Da sauri ya mike ya karasa kusa da ita ya ra6a ya zauna jikinta sosai yana gyara mata, hannu, Kamshin turaren sa ne yasa ta bude ido da sauri, idanunsu suka sarke da juna, da sauru! yayi kasa da nasa idon sabuda yadda yaga idanun nata sun kara wani irin blue gasu sun kara girma,sosai yausha rabon da su hada ido kamar yau,duk abunsa ba yadda ya kalle idonta domin take alkadirinsa a kanta yake karyewa,ko Sex yake da ita baya ta6a kallon idonta, bakinta kawai yakewa kiss.

Maryam ko wani irin a mai ne ya dinga yunkuro mata sakamakon kamshin turaren jikinshi, gefe guda koma zuciyarta ta wata irin faduwa sabuda wani irin son Nasir din ya yi mata dirar mikiya abun ya kara nunkuwa a kan na da,mussaman yanzu da ta ganshi cikin manyan kaya wanda suka fito masa da tsantsan kyawunsa gami da haibarsa da kwarjini, a zuciyarta addu'a take masa domin Allah ya shirye shi.
[26/07, 01:47] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*138*
Ganin Momy tana sauko wa daga sama yasa shi saurin rungoma Maryam din jikinshi yana wani yi mata magana kasa-kasa Hannushi a sumar ta yana shafawa cikin sigar rarrashi,
Momy ta sauko a nutse ta zauna kan kujera tana kallonsu rungume da juna, tace"Myson ka shigo a she"?
Chapter 65 · 0% Book details