← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 80

Sashe 71

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru tayi masa sai da ya kara maimaitawa sannan ta d'aga kai,alamar ta yarda, tace"amma da sharad'i
Cikin zuciyarsa yaji mamakin abunda tace, ko wane irin sharad'i ne oho,
"Fad'i sharad'in inji"
yada yana wasa da gashin kanta
"Kabar min baby na inason shi, don Allah, tafada tana marairace wa, Lura da yayi dole, dole sai ya had'a da wayo da dabara gurin ta yasa yace" shikkenan Sharadin?
[26/07, 01:51] +234 808 996 5176: [7/16, 8:13 PM] BintuBatula,BintUAbble
: *YARO DA KUDI*
*152*
D'aga kai tayi tana wani marairaice fuska, a gigice a kamo fuskarta ta yace"shikkenan na bar miki abunki, amma in kin haihu ke zaki raini abunki kuma dole za mu tsarin iyali"
Cikin k'uriciya Maryam tace "na yadda nidai in dai zaka bar min babyna rainon shi bazai min wahala ba"
"Shikkenan magana ta wuce ai"
yafad'a yana laluben ta, jikinshi ta kwanta,sosai shi kuma yayi rigingine kan Sofa ya d'orata a saman sa, a takaice anan suka fara soyyayarsu kafin abu ya d'auki zafi, ya dauke ta suka nufi bed din, Maryam ta sakar masa jiki sosai, kuma tayi masa kalolin soyyaya masu wuyar manta, ya gamsu iya gamsuwa itama taji d'adi da bata taba ji ba domin yau dalilin sakin jikin da tayi yasa, bataji zafi ba, bacci sukayi rungume da juna,
Kusan tare suka tashi daga bacci, ya mik'e ya shiga toliet ya fara wanka, cikin nishad'i so yake ya dawo daga massalaci ya k'ara wani sex din dan jinsa yake zam!zam, Maryam ba irin matan da za'agaji dasu bane,
Yana futowa suka had'a ido tayi saurin rufe fuskarta da bedshit din tana jin kunya,
Bedshirt din yaja da hannushi fuskarshi babu yabo babu fallasa yace"ki tashi ki gasa jikinki kiyi wanka kiyi sallah, kafin in dawo, domin zan k'ara wani"
Bud'e fuskar ta tayi kad'an tana satar kallonsa tace"Uhum"Uhum ni kam nagaji ancle gaskiya"
"Ni ban gaji ba Princess ki shirya ina dawowa zan d'ora inda na tsaya, kina son baby ni kuma ina son soyyaya, sabuda haka a kan sharad'i kike duk lokacin dana b'ukace ki ki amunce kawai babynki zai fi samun lafiya"
ya karasa maganar yana kokarin futa.

Sakato Maryam tayi har ya futa, a fili tace"anya zan iya da fitinar ancle kuwa, jiya ba, sau kusan uku yana rilizing a kanta da yayi zai sake zage damtse yana aiki sai kace wani ayo anya zata iya kuwa!?

Jikinta a mace ta mike ta shiga toliet tayi ruwan zafi kamar yadda yace mata, tayi wanka ta futo tayi sallah, bayan ta idar ta yi addu'oin ta yadda ya samu, zama tayi shiru ga yunwa tana sasakar ta, ga fargar bar ancle d'in, shida da rabi ta jiyo motsin sa, yana k'okarin bud'e dakin, gabanta ya fad'i, ido suka had'a tayi saurin sunkuyar kanta k'asa, yana sanye da wani k'aramin wando wanda ya ,kama jikinshi, iya gwiwa ne, jikinshi duk aljiwai, babu riga a jikinshi kirjinshi wani irin gashi ne a kwance powar dinshi duk a murd'e, cikin zuciyar ta tace"wannan in baiyi k'arfi ba me zaiyi haka yake zagewa a kanta, babu abunda ya dameshi
Kwalla ta fara tarawa a idonta dan yaji tausayin ta, kwanciya tayi kan dadduma tana kudundune jikin ta, zama yayi saman gado yana kunna wayarsa, yana kallonta, k'afarta yaja yace"bacci zaki koma kin manta abunda nace miki ko"
Mikewa zaune tayi tana ya mutse fuska tace"ancle jiri ne yake damuna ga yunwa"
Tabe baki yayi yana kallonta,yace"yanzu me kikeso ai miki"?

Abunci zanci in kwanta in huta"
tafad'a bakin ta na rawa,
"Ni kuma fa"?yafada yana kallonta
"Ancle kayi hakuri don Allah wallahi yanzu na gaji, gashi gurin yana mim zugi"
Shiru yayi tsawan minti biyu ya mike ya futa daga d'akin, murna ta ke tayi tunanin ko ya hak'ura ne, sai gashi ya dawo,hannushi rik'e da wani k'aton faranti cike da kayan tea
da wasu manya-manya biscut masu tsada
Ajiyawa yayi gabanta yace"ki had'a tae ki sha, tukkuna, kome ye sai ya biyo baya.
tae din ta had'a ta fara sha kad'an-kad'an, tana satar kallonsa, magana ce a bakinta, tanajik nauyi, shi kuma hankalinsa yana kan wayarsa,
Da kyar! tace"ancle Momyfa me zaka ce mata"?

Hararata yayi yace"kwartanci nayi kome, daga nan ma gida zan wuce dake babu wani gurin Momy da zan mayar dake, nima ina b'ukatar ki"
Yafad'a yana daddana waya babu abunda ya dameshi.

Shiru tayi kawai tana danne kuka dake son ya kufce mata, amma ina sai da hawayen ya zubo,sheshsheka yaji yayi saurin dago kanshi, yace Cikin fargaba ya sako daga bed din ya zauna kusa dai ta, kafad'ar ta ya kama yace "Baby Sorry stop crying"
Cikin damuwa yad'i maganar.
[26/07, 01:51] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*153*
K'inyin shiru tayi, jikinshi ya fara kyarma sam baya son kukanta,yanzu ci masa rai yake, yace"Princess wannan kukan naki,bana son shi ki fad'amin dalili kinji, kiyi shiru please"
Yafad'a ya kaskantar da kai.
kamar bashi ba
Ita kanta Maryam din tayi mamakin shi, cikin shagwaba tace"ancle muje gidan Momy bana son komawa gidanka,wallahi tsoran kwana ni kad'ai nake"
Shima marairaice wa yayi yace"takwana gidan sauk'i Mylove ni sai in dinga tayaki kwana ko"?

"Uhum!

Uhum! ita kuma Mubina fa"?

Tafada cikin shagwaba,
Shaf ya manta da wata mubina shi, yace" babu ruwanki da wannan, ke dai kawai ki amunce min please kar ki k'ara kuka kinji"?

D'aga kai tayi kamar wata yarinya k'arama, shagwabar ta tana dilmiyar dashi, yace"bari ij had'a miki tae ko"?

D'aga kai tayi a karo na biyu, kawai tana binshi da kallo, cikin mamaki wato shi dai in zaiyi sex ko wane irin ladabi da kwantar da kai ya iya abunda Maryam bata sani ba, shine ita kad'ai yakewa wannan, sabuda shi kad'ai yasan irin gamsuwar da yake da ita.

Duk ya zubar da madara a k'asa gurin had'awa ga wani uban sugar da ya zabga mata, k'arba tayi ta kurb'i kad'an sugar cau! a bakinta ya mutse fuska tayi, zuciyar ta ta fata tashi, sai kawai ta aje cup din kasan kafet ta kwanta k'asa,
Cikin mamaki ya bita da kallo ganin yadda ta lanjare, a kasa, yana d'aya daga cikin abunda yasa ya tsani cikin jikinta,sabuda yasan shine ya jawo mata,wannan kasalar, dole ne ma yasan yadda zaiyi dashi,
Kwanciya yayi kusa da ita ya mannata bayanta a kirjinta sai shinshina ta yake, yace" wannan yana d'aya daga cikin abunda yasa bana kaunar cikin jikinki, sabuda zai shiga rayuwata, nima ina b'ukatar a kula dani, jin abunda yace"yasa tayi saurin juyo wa tana fuskantar shi, ta bude baki kenan zatayi magana ya had'e bakinta da nasa, ya shiga sarrafata cikin kwarewa babu yadda ta iya haka ta hakura sabuda tana bukatar ya bar mata cikinta, nan kan kafet yayi ta wasanninsa da ita, sannan ya dauke ta suka koma bed, nan na futo na barsu nima.

Sai kusan sha biyu saura na rana, sannan Nasiru ya sararawa Maryam, tana kwance laka-laka kan bed cikinta sai kullewa yakeyi wani irin amai! mai k'arni yana yunkuro mata, bakintq duk ya cika da miyau, kafin tayi yunkurin mikewa amai ya kece mata nan tai tata kwarashi kan bed, mai wahalar gaske, lokacin Nasir yana toilte yana wanka, yana futowa idanshi ya sauka kanta,tq dafe k'irji tana kakari, ya mutse fuska yayi, yai saurin dauke kanshi, yana jin tashin zuciya, jin k'arnin amai ya cika d'akin.

Da towol din a jikinshi ya futa daga dakin da sauri ko sauraron ta bai ba, tana yunkurin amai,kamar zata amayar da "yayan cikinta.
[26/07, 01:51] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*154*
Da kyar! ta samu amai ya tsaya, ta mike a hankali, jikinta nan nad'e da wani k'aramin towol iya cinya, bedshirt din ta cire daga kan bed d'in ta nufi toilet dashi, tana mamakin rashin imani da tausayi irin na Nasir, cikin abun wanki ta sakashi ta hada ruwa tayi wanka, bayan ta gama, sai ta wanke bedshit din dake a kwai gurin shanya a ciki ta shanya, ta futo, kayanta da ta cire du ta mayar, ta zauna kasan kafet ta had'a ruwan tae babu suga sai lipton shi take sha'awa sabuda yadda take jin cikinta kamar an mata yasa, kurb'a takeyi k'adan-k'adan ya shigo dakin cikin Sallama, daga shi sai treeQutar sai wata d'amammiyar vest kana ganin shi kasan yana cikin farin ciki sai annuri ne yake sauka a fuskar shi, bakin kofa ya tsaya yana karewa dakin kallo, ganin ta dauke bedshit din ta sanya wani, yasa ya shigo d'akin yana wata irin tafiya irin tasu. sunkuyar da kai tayi, kawao tak'i kallonsa, kwanciya yayi kan bed din yana kara gyara eir pix din dake kunnenshi, babu abunda ya dame shi, Maryam bata taba sanin namiji mayaudari bane sai yau lallai wato bukatar sa ta biya shikkenan har ya manta da ita.
sai da tagama shan tea dinta sannan ta dago kai tana kallonshi a nutse ta kira sunanshi, kasancewar da eirpic a kunnahi bai jiba, sai da ta buga gadon da hannunta sannan ya ankara cire eir pix din yayi yace"Ya akai"?

Shan kunu tayi tace"ka maidani gida"?

"Wane gidan"?

Yafada cikin sigar rashin mutumci
" Gidan Momy"
tafada muryarta tana rawa.

"Momy ce take auranki ko ni"?
yafada fuskarshi babu walwala,
" Kaine, kake aure na, amma ai ba haka kukayi da Momy ba"
"Ok to babu ruwanki da yadda mukayi da Momy, ni babu wani mayar dake da zanyi, kina nan ma, ita Mubina ta zauna can, in anjima in nafuta zansa Giss ya kawo miki kayanki"
yafad'a yana maida eir pix dinshi kunne,
Kuka tasa sosai tace"ai ba haka mukayi ba, ni wallahi bazan zauna dakai ba gwara gidan Momy ko gidan Mubina, ni bazan zauna kusa da kai ba ina ciwo baka damu dani ba, in ma mutuwa zanyi in mutu babu abunda ya dame ka"
Dariya yasa yace" Kinjiki da wata magana,nifa bazaki sanya ni a maganar cikinki ba, haka kawai ina hutawa ta, tunda dai ke kinji kin gani zaki iya kiyi, amma kar ki saka ran dan kina amaye-amayen ki zan taimakamiki babu ruwana yarinya"
yafad'a yana karkad'a kafa da alama music din da yake ji yana ratsa shi.
Chapter 71 · 0% Book details