← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 80

Sashe 52

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Hajiya Aisha tana dreving ta kalli Maryam dake kusa da ita tace"kinga wannan kananun kayan da na sai mai ki in kinje gidan mijinki su zaki riqa amfani dasu, kar ki tsaya kunya kinji ko tunda kinga kina da kishiya
Kiyi kokari ki kama mijinki a hannu tunda dai Allah ya qaddara wannan yaron Mijikin ne sai ki godewa Allah, yanzu sauran yaki yana gareki
[10/06/2019 8:00 PM] Binta Umar Abbale: Hajiya Aisha ta dage tana koyar da Maryam dabarun zama da miji da yadda a ke kula dashi tace "su mazan wannan zamani da kike ganinsu sai da rarrashi da siyasa, sabida haka sai in zage damtse gurin ganin kin kama mijinki a hannu"
Maryam kuwa sunkuyar da kanta tayi tana jin kunya Hajiya Aisha jin irin abinda take fada ita kam kunya take ji tana ganin bazata iya amfani da wadan nan kananun kayan ba
Sai daf da magariba suka shiga gida,
Ya Rabi taji dadin abinda kawarta kuma aminiyarta tayi mata ganin yadda Diyarta Maryam take walwali ga wani mugun kamshi tana zabgawa duk inda ta gifta
Bayan sallah magariba Ya Rabi tace ai ya kamata su shiga bangaran Momy domin su gaisheta kuma suyi mata godiya da fatan alkairi
Duk su ukun suka shiga gurin Momy ta karbe su cikin mutumci gami da kyautatawa
Ya Rabi tace" Hajiya sai mukaji wannan abin alkairi kuma"
Momy tayi dariya tace"ai haka Allah ya tsara dukkanin abinda Allah ya tsara babu mahalukin da ya isa ya hana, Allah yayi Maryam matar Nasir ce"
"Wannan abu haka yake hajiya, Ubangiji Allah ya sanya alkairi ya basu zaman lafiya Allah ya bashi ikon kyautata adalci a tsakaninsu"
"Ameen ya rabbi nagode sosai"
Momy tafada tana kallonsu cike da murmushi
Ta cigaba da cewa gobe insha Allahu zasu tare a gidanshi dake tarauni kar ku wahalar da kanku komai an tanada a gidan, Maryam kadai muke bukata,insha Allah kayan lefanta ma zataje ta tadda a can"
"Hajiya Allah ya saka da alkairi ubangiji Allah ya kara arzuqi da wata mukan babu Cabinda zamuce daku wallahi"
Aunty tafada tana sunkuyar da kanta
Momy tace "nasan dai Dota bata da matsala yarinyar tana da nutsuwa amma dai sai a kara ja mata kunne sabida ba ita kadai zasu zauna ba a kwai "yar uwarta duk abinda zata gani ta kauda kanta wataran sai labari
"Insha Allahu za'a yi mata fada Hajiya duk da cewar Maryam bata da kwarfinaya da yawa, amma yau da gobe ta wuce wasa
Hajiya Aisha tafada cikin nutsuwa da dattako
Hira suka cigaba da yi cikin fahimta gami da wayewa dake Hajiya Aisha wayayyiyar Mace ce kuma "yar boko shine dalilin da yasa Momy ta ji hankalinta ya kwanta da ita
[11/06, 13:58] +234 808 996 5176: [10/06/2019 10:17 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*115*
Nan sukayi sallahr isha'i Momy ta sanya mai aikinta Uwani ta hada musu abinci dole babu yadda suka iya suka zauna suna ci suna mamakin karamcin Momy
Karfe takwas na daran rabar Lahadi Maryam ce durkushe gaban mahaifinta tana kuka sosai shi kuma yana mata fada kan ta kula da auranta kuma tayiwa mijinta biyyaya da dukkanin abunda ya umarce ta.

Aunty ma tayi mata addu'a sosai sannan tayi mata nasiha irin tama ta mata yi nayi bari na bari
Yaya Rabi daman ita kullum Cokin yiwa Maryam din nasiha
Dake babu jama'a sosai sabida basu wuce su biyar ba sai Momy tacewa drevar ya dauki babbar mota kawai ta isa
Haka Ya Rabi ta sanya Maryam cikin mota tana gursheken kuka kamar ranta zai fita wai yau ita ce ta auri Wanda bataso Wanda yayi mata muguwar tsana a rayuwarshi
[11/06/2019 7:09 AM] Binta Umar Abbale: Momy ta rungume ta a jikinta tace "kiyi hakuri Dota ki zauna da mijinki lafiya da "yar uwarki nice mahaifiyar Nasir nafi kowa sanin halinshi duk wani abu da kike tunani zai faru babu shi sai alkairi, ni da kaina zan damka masa amanarki shine ki kwantar da hankalinki in kika iya zama da Nasir zaki ji dadinshi sabida yana da saukin kai duk ranar da kika ga ya tashi yana muskilanci to mybe da akwai abinda yake damunshi ke zaki dinga bibibyarshi tunda shi zurfin ciki gareshi, dan Allah Maryam ga amanar Nasir nan Na damkata a hannunki kamar yadda ba bashi taki amanar ki lura da cinsha da shansa domin Sam baya son cin abinci sai na tsaya a kanshi sannan"
Wani irin tausayin Momy ne ya kama Maryam babu abinda Momy zata nema ta Gaza yi mata shi a rayuwarta sabida haka tayi alkawarin ko da Nasiru zai yankata gunduwa gunduwa za ta tsaya ta rike amanar da ta karba
Wani irin gida ne mai bala'in kyau da tsari plate ne mai dauke da part uku sai katowar haraba gurin ajiye motaci ma na mussaman ne can gefe lambu ne an kewaye shi da wasu karafuna sun sha ado gurin gress kafet ne a ko ina na gurin yanayin gidan kamar irin gina ginen kasashan waje ko ina tsaf tsaf Ma'aikatan gidan sai kaiwa suke suna kawowa ko wanne da aikinshi
Nura tayi parking din mota Momy ta fito hannuta rike da Maryam Ya Rabi da sauran jama'a suka fito suna bin gidan da kallo cike da kauyanci sabida kalar faint gidan ma abin kallo ne Momy ta fito da waya tana neman Nasir ta kira ya kai sau uku ba'a daga ba, gashi tana ring sai ta kashe wayar tana tuna in wane part din ne na Maryam tana tsaka da tunani motoci suka fara shigowa gidan dauke da amarya Mubina da ta wagarta, motoci sun kai goma
Kan kace kwabo gurin ya cika da hayaniya dangin Mubina suka dinga fitowa daga mota kamar bazasu kare ba.
Chapter 52 · 0% Book details