← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 80

Sashe 24

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasir ya fito daga bed din hannunshi nan nade da blet , sai huci yake yi dole sai ya hukunta Maryam,sabida ita "yar iska ce shine zata kulleshi cikin daki ,tamkar gidan ubanta,
Ya bi farlo da kallo babu ita babu dalilinta, da sauri ya shiga kchin yana tunanin ko anan ta boya, nan ma bata nan ya fito yana rarraba ido,yashiga master bedroom din shi ya duba nan ma batanan,a gigice yafito yana daga labulayen farlo wai ko ta makale a ciki, wata zuciayr tace masa kila ta fita lokacin da Joy ya bude kofar,da sauri ya saki blet din ya fadi kasa, jikinshi na rawa ya fita daga farlon yana kwalawa Joy kira, a ran sa yace yarinyar nan tafita ahaka ai ta cuce ni, wallahi,shegiya "yar iska kawai,
Ya riqa yiwa Joy masifa mai yasa lokacin da ya bude kofar bai kulle ba, Joy sai bashi hakuri yake,ko saurarasa bai yi ba, ya nufi daya daga cikin manyan motocin sa dake aje a farfajiyar gurin ya shiga a fusace,Joy ya biyo shi a baya yana bashi hakuri,ya daka masa tsawa gami da cewa ya koma baya bukatar rakiyar shi,
Ya fafari motar ya fice daga gurin a fusace, ya daki kan motar yana huci a fili yace"Maryam I will kill you, Maryam in na ganki sai na kusa kashe ki, ji yake tamkar ya fashe da kuka Dan bakincikin abinda tayi masa
[19/05/2019 12:39 PM] Nana Aisha: *YARO DA KUDI*
*58*
Maryam ko na ciki gidan tana jin duk wani motsin shi,sai da ta tabbatar ya fita sannan ta fito da sauri,Allah yasa ya bar dakin a bude tayi sauri ta shiga ta saka kayan ta cikin sauri-sauri take yi tanayi tana kallon kofa ,dama safarta na kafarta ta lalubi niqaf din ta ta daura , sai da jakar ta na motarsa haka tafito da sauri tana wai wayen dakin.

Karo suka kusa yi da Joy ya dawo da niyar rufe kofar, ita kuma zata fito,
Tsawa ta daka mata cikin turanci yace"wuce ki koma ciki"
Ita ma cikin turancin tace"ai mungama da shi,Ogan ku ya sallame ni,tafadi maganar kamar gaske.

Joy sai ya yadda da maganar ta sabida dama oga in ya dauko yarinya.

Da safe ,bata kwana masa a gida sai dai in da daddare ya shi go da ita
Ba ta hanya yayi ta wuce gabanta yana faduwa ta fice daga gidan.

Babu kowa a layin shiru babu motsin mutum sai gilmawar mota,jefi-jefi ,Maryam sai rarraba ido take tana addu'a Allah ya kawo mata dauki.

Wata mota tazo ta wuce ta gabanta fuuuu! sai daga hannun take.

Sannu a hankali motar tadawo da baya har tazo in da take,Marym bata tsaya ganin Wanda yake cikin motar ba kawai ta bude ta afaka,ciki jikin ta na karkarwa,
Anwar ya sauke a jiyar zuciya yana cizan lebanshi nakasa a fili yace"tsuntsu daga sama gashashshe ,ba sai na sha wahala ba,tunani yake yi mai yakawo ta gidan Nasir,gidan da bakowa ne yasan dashi ba, Lallai a kwai wani abu boyayye ,wata zuciyar tace masa mybe ita ce yarinyar da Abbas ya fada maka,dazu,in hakane Nasir ya gama dashi, wallahi, dama yafada masa ba ya cin saura,to wannan ba zai hanashi biyan bukatarsa a kan yarinyar ba.

Ta mirrow din motar ya kura mata ido yana jin wani fleenig na yarinyar
Da kyar yace"baby kin gane ni kuwa,dago kai ki kalle ni ,masoyinki Wanda ya jima cikin kwadayinki,da sha'awarki tare da sha'awar komai naki
A gigice Maryam ta dago kai jin kamar maganar abokin uncle Wanda ya taba ritsa ta kwanaki a dakinshi.

Ido hudu sukayi ,Maryam tafasa wata kara,tafara kokarin bude kofar cikin zafin nama,
[19/05/2019 12:39 PM] Nana Aisha: *YARO DA KUDI*
*59*
Abinda Maryam bata sani ba kuwa motar mai sucurity ,tayi -tayi ta bude takasa, Shiko Anwar yana kallonta yana dariya, yace"ina zaki babyna ai yau Allah ne ya amsamin addu'ata a kanki"
Maryam ta fashe da kuka tace "Wai mai nayi muku kai da abokinka kuka tsaneni in sha Allah ,nafi qarfinku Allah bazai baku iko a kai na ba"
Dariya Anwar yayi yana dukan kan mota yace"ke din ce baby duk namijin da yayi ar ba dake sai yaji yana sha'awar ki ,sabida kina da wasu abubuwan da ba kowace mace take dashi ba.

"Allah ya fiku domin dashi na dogara ban taba zina ba kuma ban yi ba ,sai dai Ku kashe ni Allah ya isa tsakanina daku ,"yan iska kawai"
Cikin kuka take fadin maganar kwata-kwata a lokacin babu tsoro ko guda a tare da ita,
Anwar ya tsai da mota ran shi a bace ya waiwayo yace "ni kike zagi dan ubanki ,shegiya "yar mai gadi,kamar ni ki sani a gaba kina zagi yau sai na nuna miki yaya bariki take,
Kawai sai ya kwantar da kujerun motar ,ya afka kan ta, ya fizge hijab din har yana makure mata wuya ,ya kama Brest din ta ya riqa murazawa ya danne ta Tanata motso motso ,dukanshi take tana kuka,shikuma ya fita daga hayyacinsa sai kokarin zare wandon sa yakeyi,
Motar Nasir yace tazo ta wuce,yana ciki yana cikin bacin rai,babu inda bai duba ba bai gan ta ba ,har skull din su sai da yasa aka duba masa ,a kace yau bata zo ba,
Motar Anwar ya gani ya dawo da baya, yayi parking ya fito cikin zafin nama ,ya karasa gurin motar
Numfashi ya riqa ji da nishi!

Nishi!

Yana tashi cikin motar ga kukan mace nan a ciki, babu abinda yake gani kasancewar motar mai duhun gilasai ce,sai ya daki motar da kafarshi gabanshi yana faduwa ,sabida yadda zuciyarshi take fada masa Maryam ce a ciki motar
Maryam kuka take ,tana kiran ancle din sabida ita tana ganinshi shine baya ganinsu,yayinda Anwar ya gigice ya fita daga hayyacinsa ,sabida yadda yayi nasarar cirewa Maryam rigarta har briziyya ga kirjinta nan duk a waje ,ta na rufewa da hannuwanta tana kuka shikuma Anwar yana cire hannuta yana ihu!

Nasir hankalinshi ya tashi sabida ya gama yaddawar kanshi cewar Maryam ce a cikin motar,
Zagin Anwar yake cikin turanci yana dukan motar da kafarshi da hannunshi, jikinshi sai tsuma yakeyi ya tafi da gudu ya dawo ya kaiwa glass din mota doka da kafarshi mai sanye da takalmi boot mai Mugun tsada da kwari,
A i kuwa glass din ya fashe , ya zira hannunshi cikin motar yana kokarin budewa, tafin hannunshi duk ya yayyanke, amma Sam bai damu ba,
Lura da yayi Anwar ya sanyawa motar suciruty yasa ya zira hannu ya damko wuyan Anwar din ,yana dukan kan shi,hade da zaginshi cikin turanchi
Anwar ya dawo hayyacin shi har yanzu yana kwance kan Maryam ya dago ta ya rugume a jikinshi idon shi kamar gauta,ya ke kallon Nasir"da kyar tace" haba mana! yawa kake Alhji ya ina hutawa zakazo kana min haka ,har da fasamin glass din mota"
Nasir kamar zuciyarsa ta fashe haka yake ji ganin Maryam rungume jikin Anwar babu riga,ga nonuwan ta a waje ,daga ganinsu Anwar ya taba ganin yadda sukayi jajazir abinka da farar fata
[05/06, 18:47] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*60*
Nasir yace "ka bude motar nan dan ubanka shege maye ,kawai wallahi tallahi kasake kayiwa yarinyar nan wani abu sai na kashe ka Anwar!!

"Iwiil kill you San nakashe ka,!!!

Cikin ihu da hayaniya yake maganar sai dukan motar yake yana kokarin budewa hannuwanshi duk sun faffashe sakamakon glass din motar da ya fashe,.

Anwar ya bude ya saki Maryam gami da bude mota sabida ,yadda yaji Nasir yana zaginshi gami da cin mutumcinshi,duk akan abinda bai taka kara ya karya ba,yarinyar da da kudi zai iya siyan ta ko nawa ne tunda Allah ya hore masa,yau sai yaga da abinda Nasir yake taqama
Yana fitowa daga motar Nasir ya damke shi ,ya rika gaura masa marika hagu da dama,.yana zaginshi,fadi yake sai naga bayanka Anwar tunda kashiga gona ta,sai na kashe ka
Kan kace kwabo fada ya rikice a tsakaninsu,
Maryam na cikin mota jikinta duk yayi tsami,sai kuka take,ga gefan kafadar ta kwalaba ta yanketa sai jini gurin yake fitarwa,da kyar ta lalibi rigarta ta zira ta saka hijab ta bude motar ta fito, tana jan kafarta domin ita ma glass ya yanketa ,ko kallonsu bata yi ba, wanda har yanzu suke kokawa da junansu, Nasir sai duk Anwar yake duk ya fasa masa baki da hanci,
Motoci jefi jefi ne suke wucewa saboda dama can titin ba ka safai a ke bin shi ba,
Kokarin tsallaka titi take,Nasir ya ankara da ita , yasaki Anwar cikin zafin nama ,ya nufi inda take bai jira komai ba,ya dauke ta cas!

Ya nufi motarshi da ita.

Maryam kuka take tana dukan bayanshi, bai saurare ta ba a jeta cikin motar ya rufe
Ta dunga dukan glass din motar tana ihu gami da kiran sunan shi ko sauraron ta bai yi ba ya karasa in da Anwar yake kwance jina jina cikin jini, da gaske Nasir kokarin kasheshi yake domin ko da ya karasa gurin dukanshi a kirji shi da qafarshi mai sanye da katon takalmi.

Ihu!

Anwar yake yana kokarin kwatar kanshi ya kasa !

Motar dady ce tazo ta huce fuuuuu!!

Dady yayi daurin da katar da Nura drever yace"kamar motan Nasir ce waccan ko Nura"
Nura yace"kwarai kuwa Alh.motarshi ce ,ai Nasir din ne ma suke fada Alh da'alama babu lafiya"
"Subahanallahi"
Ko ma baya"
Dady yafada cikin tashin hankali,
[05/06, 18:51] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*61*
Nura yayi parking din motar can tsallaken titin da sauri dady ya bude ya fito sabida hankalinshi ya tashi ganin abinda yake faruwa,
Sam Nasir bai ga zuwan shi gurin ba, yana can yana dukan Anwar sai kace wani mahaukaci, dady ya daga hannunsa ya tsinka masa mari ,cikin tsananin fushi da bacin rai!

Yace"kisan kan zakayi Nasir iyi mai Anwar yayi maka kake masa irin wannan dukan.?
Chapter 24 · 0% Book details