← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 80

Sashe 41

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dariya kamar ta kashe Nasir a cikin mota ,yana sane yake ta faman danna Hon babu ji babu gani
Maryam ta juyo a fusace tana danna masa harara taja tsaki ta cigaba da abinda takeyi,shiko yana ganin abinda tayi sai ya kara danna hon da karfin gaske
Ya bude motar ya fito a fusace, ya nufi gurin , yana zuwa kawai ya buge hannunta daga jikin get din yace"dallah matsa mana a guri kinsan baza ki'iya budewa kika batawa mutane lokaci idoit"
Maryam jikinta a sanyaye ta dinga kallonshi tana galla masa harara sai haki takeyi tsabar gajiyar da tayi ga hannuwanta sunyi ja sabida yadda take tura kofar abinka da farar fata ,tafin hannun yayi jajazir, a fusace ta wuceshi taje ta zauna kusa da Baban gida ,duk da haka bata fasa hararsa ba
Ja da yayiwa get din duk irin raurinsa da nauyinshi kuwa ,ya bude nan take, sai a lokacin Malam Ya'u ya karaso gurin, Nasir wuce yaje ya shiga motarshi ya fita daga gidan ranshi a bace yace"ai ko ka bar aiki ko baka bari ba dole in samu wani Wanda zai dinga kula da aikinshi"
[06/06, 01:47] +234 808 996 5176: [28/05/2019 10:06 AM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*94*
Baban gida ya rika yiwa Maryam dariya bayan Nasir din ya fita,yace"kin cika raguwa da kika kasa bude kofar can, nasan inda Nafi'u nasa ko Miftahu da tuni sun bude, ke kin tsaya shirme dube ki sai nishi kikeyi kamar wacce tayi aikin karfi"
Itama dariya tasa tace"wallahi kuwa na dauka zan iya budewa ashe akin babba ne ,dubi hannun fa"tafada tana nuna masa tafin hannunta, dariya kawai yake mata har Malam Ya'u yazo ya zauna a gurin,
Yace "dazu naje na samu Hajiya nafada mata halin da ake ciki"
Baban gida yace"ai haka yafi gwara tasan komai da wuri"
Hakadai suka zauna suna tattauna maganar,
Maryam ta mike ta shiga gida tanajin wani farin ciki a zuciyarta ganin zata dai na rayuwa a karkashin wani Wanda bai San darajar Dan Adam ba.
*****
Bangaran su Abdul latif kuwa lokacin da mahaifiyarsa taji abinda yake faruwa daga bakin Alh Hassan wato mahaifin abdul cewar Dan uwanshi bar wassiyar ko bayan babu ranshi a daura auran Abdul da Maryam, sai tayi tsalle ta dire tace"wallahi bata yadda ba danta bazai auri , wa"yanda ba'a san asalinsu ba ba'san daga inda suka fito ba sabuda haka indai ita ce ta haifi Abdul to bata amince ba"
Alh Hassan yace"dama bama bukatar ki amince ,dole zan cikawa dan uwana burinshi kafin ya mutu"
Rikici a ke sosai akan maganar inda Hajiya Zulai taja tunga tace bata amince ba,shi kuma yace babu abinda zai fasa
Abdul ma yaji duk halin da ake ciki ,to duk da haka yana nan a kan bakanshi sai tausar zuciyar Mahaifiyar tasa yake
Hajiya Zulai kuwa sai zugata akeyi cewar yarinyar "yar iska ce ,sabida kwanaki ma an nemeta anrasa
[28/05/2019 12:11 PM]
Binta Umar Abbale: Sabida haka ta tada hankalinta a kan maganar, tace ita bada yawunta za'ayi wannan aure ba.

Misalin sha daya da rabi na dare Nasir ya shigo gida ,Malam Ya'u na zaune a bakin get har yanzu bai shiga gida ba sabida Nasir bai shigo ba har yanzu radio ce a hannusa yana sauraron tashar Ballo Dandago wato radio Kano kenan
Da sauri ya aje radio ya mike ya je ya budewa Nasir get, ya shigo da motar.

Yayi parking ya fito , kai tsaye bakin get din ya nufa Inda Malam Ya'u yake yana kokarin mayar da kofar ya rufe.

Muryarshi Sama-sama yace"Arrama ina son magana da kai"
Malam ya juyo da sauri Dan bai tsammaci zuwanshi gurin ba
Yace"to to ai babu matsala Nasiru ina sauraronka
Nasir ya gyara tsayuwa sosai yana kallonsa yace"dazu Momy take fadamin maganar da kukayi da ita, cewar zaka bar aiki a gidan nan ko"?

Cikin mamaki Malam ya dago kai yana kallon Nasir din yana Mamakin yadda ya tsareshi da tambaya sai kace wani ubanshi,lallai Yaron yana ji da izza, amma sabida dattako irin na Ya'u sai yace"kwarai kuwa Nasiru inaso in fara kasuwanci ne"
"Owk yanzu tsawon shekaru nawa kayi a gidan nan kana aiki ,inaso in biyaka hakki kane kamar yadda shari'a tace"
Nasir yafadi maganar kai tsaye kuma da'alama haka abin yake har cikin zuciyarsa
Cikin dumbun mamaki gami da al'ajabi Malam yake kallon Nasir din, ya nuffasa gami da cewa"kayi gaskiya Nasiru ni tun lokacin da marigayi ya dauke ni aiki a gidan nan ba muyi dashi zai biyani domin ba nai masa gadi Dan ya biyani komai sabida haka babu wannan maganar a tsakanina dashi har ya koma ga Allah"
Nasir ya sauke a jiyar zuciya, yace" ai nasan da haka, yanzu dai nine maigidan, kamar yadda zan je in dauko wani get man din in biya shi hakkinshi ya zama dole in baka hakkin ka"
Arrama yace"bana bukatar komai Nasiru nagode sosai da kulawa"
Nasir ya bude Jakar dake hannusa ya fito da kudi kimanin dubu dari biyar yace"ga wannan ka rike ka hada dasu gurin yin bussines din naka , Allah ya taimaka"
Cikin mamaki Malam ya karbi kudin shi kuma Nasir ya juya ya shige part dinsa
Da safe Malam ya fito da kudi yana nunawa aunty ,itama tayi mamaki sosai, sai tace kawai ya hada dasu tunda dai shi bashi ya nema ba
Haka rayuwa take Malam Ya'u ya fara kasuwanci cikin sa'a sosai yake samun rufin asiri, yanzu ya daina zaman get kwata-kwata da gari ya waye zai fita kasuwancinsa ,hakanan yanzu shine yake dawainiya da yaranshi gurin biyan kudin makaranta,dama su Nafi'u ne ,Maryam tuntuni ta kammala karatun ta, kafin mutuwar dady ya tsaya mata sai da tayi karatu sosai kuma takkadunta sunyi kyau sosai shiyasa take so ta samu aiki ko a karamin asibiti ne domin ta tsaya da kafafunta ita kam babu abinda zata ce da Alh Hussen kullum sai dai tayi mishi addu'a samun Rahama gurin uban giji
Abdul yana Legos ya fara aiki yanzu sai dai su yi waya su sha soyyayrsu ,yace "in yadawo za'a hado komai a kawo sai dai kawai a sanya ranar daurin aure.

Nasir kwata -kwata ta manta yau sharabon da su hadu ,sosai tayi bala'in kewarsa tun lokacin da suka hadu a bakin get bata kara ganinshi ba.

Ban garansa kuwa abubuwa ne suka sha masa kai sosai domin yanzu harkoki sun bude masa ba ya zama a gida sosai ko asibitinsa bai fiye zama ba in dai ba dole ba ,sabida yadda kasuwancinsu ya bunkasa daga sunyi odar za ka nemeta karasa ta kare sabida kyawun Motocin da suke shigo dasu da nagartarsu , kudi sosai suka yi suna shi da Abbas Nasir&Abbas Motars sunan kamfanin nasu, Nasir yayi kudi na ban mamaki lokaci guda sunansu ya zagaye kasashe ,a yanzu ma shirye shiryen da yakeyi zai tafi America domin a can ma suna so su bude sabon company shi da wasu turawa.

Momy tayi tayi mishi addu'a , shiyasa yanzu kafin kaganshi sai kayi da gaske, sabida yawan zirga -zirgar da yakeyi.
[06/06, 01:47] +234 808 996 5176: [29/05/2019 1:56 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*95*
Misalin bakwai na dare Nasir ya shigo gidan cikin wata sabuwar motarshi mai masifar kyau da tsada ,yana kwance a bayan mota drevar shi Tony yana jan shi ,gefanshi kuma daya daga cikin budy gard dinshi ne, a zaune , Tony yayi parking din motar a inda a ka tanada, Nasir ya fito daga Motar hannushi rike da wayoyinshi, yayi wani haske sosai sabida yadda hutu ya zauna yana sanye da kananun kaya as'usel kamar ko da yaushe kanshi sanye da wata person cape mai uban tsada, kai tsaye part din Momy ya nufa , Giss ya bi bayanshi rike da jakarshi da wasu takkadunsa ,kana ganin yadda yake tafiya kasan yayi bala'in gajiya, ga wata shegiyar yunwa tana sasakar cikinsa tamkar zata cinye masa "ya"yan ciki, da kyar yayi sallama falon ya zube kan kujera ,kusa da bakin kofa cikin gajiya ya ce "Ya Allah"!

Giss ya tsaya a kanshi yana zare ido, Nasir din ya waigo kawai ya mika mishi hannu batare da yace komai ba.

Da sauri ya mika masa karamar jakar hade da takkadun hannunsa , kawai yayi mishi alama ya tafi, ko da ya fita ma sai ya tsaya nan bakin kofa kawai yana bin harabar gurin da kallo
Momy ta sauko daga sama sabida jin motsi, Sam bata tsammaci shigowarsa ba yanzu, cikin mamaki takaraso inda yake zaune tana kallonshi ,tace"My Son yau da wuri haka"?
Chapter 41 · 0% Book details