← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 80

Sashe 17

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaci gaba da cewa "meye ma Alaqarka dasu dady"
Dan Allah ka kyalesu ,dole za ai ta tambayar yaran waye a gurin tunda dai an San ba naka bane"
Dady yace"babu ruwanka ,kawai ka tashi ka je kai min Abinda Na saka"
Momy tace"bara Na kira Aunty sai ta turo su kawai ba sai yaje ba"
Domin Momy bata son bacin ran Nasir ko kadan
Dady yace"shi nake so yaje ya tawo da su ai kannensa ne"
Sai mom din tayi shiru ganin dady yafara hasala domin tana mugun gudun bacin ran mijin NATA
Mikewa yayi ,yana kallon Dadyn nasa yace"Afuwa my dady Na tafi"
Sai Mom ta saki fuska tana dariya"
Dady ko kara shan kunu yayi har sai da Nasir din ya fice daga farlour
Ya kalli Momyn yace"narasa Abinda yarinyar nan Maryam tayi masa Na fuskanci basa shiri"
"Wallahi kuwa Ashe kai ma ka fuskanta, gashi yarinyar nada hankali da nutsuwa"
"Kwarai kuwa Dady yafada yana saqa wani Abu cikin zuciyarsa ,a game da lamari,Amma ya barwa zuciyarsa,
Duk suna zaune ,guri guda bayan sun gama karya wa tsaf dasu Mussaman Nafi'u da Miftahu ,suna cikin do gayan kaya Na wata lafiyaryiyar shadda,har da hula,dama tun Asubah Alh Hussein ya fadawa Ya'u cewar a shirya yara zai je dasu wani guri
Shiyasa yana shigowa yafawa Aunty Dan haka tana sauke Abin kari ta mayar da ruwan Wanka.

Ta shiryasu tsaf
Maryam ce kawai take Wanka yanzu,
Nasir ya shiga da sallama,
Duk suka Amsa,ya Dan tsaya daga waje yana karewa farloun nasu kallo,Arrama Yau yace"Nasiru ya katsaya nan ,kashigo mana"
Aunty tace"rabu dashi ,ai yasan shi mai Laifi ne a gurina"
Bai yi Niyar shiga ba Amma jin furucin Aunty yasa kawai ya daga Labule fuskarsa a sake ya shiga ,
Wanda yayi dai dai da fitowar Maryam daga dakinsu Jikinta sanye da riga doguwa mai zubin "Yar kanti rigar tafitar mata da duk wani hallitar ta hannuta riqe da gyale tana kokarin nan nade kanta dashi ,batan ta nannade gashinta,yarinyar tayi kyau ba Dan ka Dan ba,
Nasir ya riqa jin gabanshi yana faduwa lokacin da sukayi ido hudu da ita,sai ya nemi yawo yarasa a bakinshi ,da kyar ya Aro dauriya da jarunmta a saka a zuciyarsa ,yakarasa ya zauna kujera,
Yace"Aunty A she laifi nayi ,Afuwa Na tuba "
Yafada yana sakin dariya,
Yace kai Na bisa wuyana Aunty"
"Wallahi Nayi fushi da kai Nasir,yau sharabon ka daka shi go min,ai INA jin tun ranar da kadawo ko"
Yace"Aunty Na manta"
Wallahi pls Aunty ,kai miftahu zo ka tayani bata hakuri"
Miftahu ya taso yana dariya,yace Aunty kiyi hakuri kinji Uncle yana da Kirki
Sai tafashe da dariya ,Malam Ya'u ma ya saka dariya yana mamakin zaro zance irin Na miftahu
*BINTA UMAR ABBALE*
_MARUBUCIYAR_
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
_in kana bukatar cigabanshi ga number nan_
08089965176
[09/04, 15:10] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

YARO DA KUDI*
Writting by*
_*BINTA UMAR*_
*MAMAN ABDUL WAHABU*
_BISSIMILLAHI_
Aunty tace"ai nayi hakuri tuntuni Miftahu,Uncle din naku ne wani'sain bai da kirki"
Nasir ya gyara zama fuskarsa a sake yace"ki dai yi hakuri Aunty ni din ne sai a hankali wallahi tun da nadawo bana zama kwananan ma za'a bude sabon Asibiti Na"
Aunt tace"kai masha Allahu Dan gidana Allah yasa s fara Aiki a sa'a Allah ya tsare da tsarewarsa"
Malam Ya'u ma cikin Farin ciki yace "Na tayaka murna Nasiru,Allah ya tsare ka daga sharrin mai sharri"
"Ameen Ameen ,Nasir din yafada yana Dan satar kallon Maryam dake tsaye gefan Aunty.

Malam Ya'u yace"kaga yanzu sai ka fito da matar Aure ko domin shine cikar mutum"
"In sha Allahu ,Arrama munanan muna dubawa a dai tayamu da Addu'a"
"Addu'a kullum cikin yi muku ita muke Nasiru ,zamu kara a kan wacce muke yi"
"To Alhmdullhi ,Allah yasaka da Alkairi Arrama Allah ya ja kwana"
"Ameen Ameen"Arrama Ya'u yafada yana jin dadin yadda Nasir din yake daukar maganarshi babu raini ko daya"yace"ina abokin ka Anwaru?

Dariya Nasir yasa yace"tunjiya rabo Na dashi Amma yanzu zan yi kiranshi a waya"
"To to Masha Allah ,ka mikamin gaisuwata"
"Insha Allah zaiji"
Nasir din yafada yana kokarin tashi tsaye.

Aunty ta bugawa Maryam harara tace"tsayuwar me kike nan gurin kina ganin mutane kin gagara gaishe su.

Maryam ta gyara tsayuwa tana kallon Uncle din tace"Aunty nazo zan gaidashi naga kuna hira shine Na dakata tukkuna"
Tsaki Aunty taja ,tana hararata
Maryam ta gyara Murya idonta kansa tace " Ancle Ina kwana"?

Saurin dauke kanshi yayi daga kanta ,yana tafiya yace"lafiya Maryam ya kk?

Kamar gaske yayi furucin.

Maryam tace "lafiya lau Uncle"
Yace"dady yace Ku fito zamuje Anguwa"
Tace"to Uncle"
Ya kalli Aunty yace"sai mun dawo Aunt
Mikewa tayi ta biyo bayanshi tana musu addu'oi iri iri tace"yanzu zasu tawo ai Maryam ce tafiye shirishirta"
Ya saki fuska kamar babu wani kulli cikin zuciyarsa yace"ki kyaleta Aunt kowa da irinshi ,Amma dai kar sukara minti goma basu fito ba"
Aunty tace"in sha Allah"
Yayi mata sallama ya fice daga bangaran nasu.

Dady Na tsaye a harabar gurin hannunshi ruqe da key din mota yau ba ya sha'awar a tukashi shi dakanshi zai yi drevin .

Nasir yakara so gurin zai karbi key din ,dady yace Ina su ke,"?

"Gasunan fitowa dady"
"Masha Allah"
"Dady kawo key din mana"
"Aa yau sha'awar dreving nake je ka huta kawai"
Dariya Nasir yasa yana mamakin rigimar dad din shi
Kawai sai ya wuce ya Nufi Motar Dady ya bude yayi zamanshi ,
Yana wani mugun jin haushin yarinyar ganin yadda take bata musu lokaci dady yayi shiru sabida baya son laifinta ko Dan,Wanda in da shi yayi haka da tuni dady ya balbaleshi da fada.

Can ya hangi tawowarsu ita dasu Nafi'u ,yayi saurin dauke kansa,yana jin wani yamm!

A jikinshi,nan da nan jarabarsa ta motsa domin shigar da yarinyar tayi ta tafi dashi,yau babu hijab ga qirjinta a waje yana gani ta cikin Riga,kamar su tsone mai I do a tsaye!!

Ya riqa takurewa jikin mota yana sauke Numfashi ,gaskiya yarinyar nan ta cuceshi,
Suka karaso motar tare da Dady yana ta jansu da wasa,ya bude musu ,bayan motar suka shiga,
Shima ya shiga ,ya kalli Nasir Wanda ke zaune ido nshi a lumshe.

Yace"kai layarka kuwa"?

Ido guda ya bude domin bayason dady ya fahimci halin da yake ciki ,yace "lafiya dady kai na ne yake Dan ciwo kadan"
Dady ya tada mota ,yace"zaka fara tsirface tsirfacen naka ko,?

Daga haka sai dai in nemeka in rasa gurin taro ka fakaice da ciwon kai!!

Wai Kai meyasa baka son mutanene?

Murmushi yayi Na gefan baki yana cije lebe,shi kadai yasan halin da yake ciki Dan idan jarabarshi ta tashi bata sarrafuwa ta dadi.

In bai kwar ba,yanzu tunaninshi ma yadda zai je ya zauna tsawon Awanni gurin taron batare da ya rage Abinda yake tsinkolunshi a mararshi ba,
Yace "Sorry My dad ,Da gaske nake fa yanzu nan nafara jin jiri kasan bana son zafi ko hayaniya"
Dad yace"sai ka nemi guri guda ka zauna ,Amma yau komai Abinka sai ka zauna an tashi a taron nan dakai"
Kwanciya ya gyara cikin motar still idonshi Na rufe yace"To dady duk Abinda kace haka za'ayi"
Maryam tayi tsuru a baya ita da qannenta tana jin maganganun da da Uba ,gefe tana mamakin Ashe Uncle yasan darajar iyayenshi,ganin duk Abinda dad dinshi yace baya musa masa,
*BINTA UMAR ABBALE*
_MARUBUCIYAR_
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
_in kana bukatarshi ga number nan_
08089965176
[10/04, 15:13] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

YARO DA KUDI*
writting by*
_*BINTA UMAR*_
*MAMAN ABDUL WAHABU*
_BISSIMILLAHI_
Ma keken guri ne cike da Mutane maza da mata yara da manya ko wannensu zaune cikin kujera cikin manyan rumfuna
Gefe kuma motoci ne manya manya kowa ya aje tashi hatta "yan matan dake gurin kowacce da tata motar,kana ganinsu kasan "yan matane masu Amsa sunansu gurin ilimi da Arziqi gami da wayewarka ,gasunan dai kowa da irin shigarshi ta rashin kamun kai ,kowacce tana hurawa "Yar uwarta hanci tamkar ba a gurin taron Sada zumunchi suke ba.

Motar Dady ta shiga gurin
A nutse yayi parking yafito yana gaigaisawa da jama'a cikin barkwanci kamar yadda yasaba
Nasir yafito daga mota yana wani ya mutse fuska,gami da bin gurin da kallo a dage!!

Hanifa dake zaune can nesa ta hangi fitowarsa ,gabanta yafadi ,domin tazata bazai zo gurin taron nasu ba sabida taga ba kasa fai yake zuwa bah.

Sauri tayi ta mike tana gyara rigar jikinta ,wacce tafito mata da duk wani sassa Na jikinta, da wani mitsayacin takalmi mai tsayi ,ta nufi inda Nasir din ke tsaye jingine jikin mota,fuskarshi babu yabo babu fallasa,yana kallon dadynshi yana gaisawa da jama'a cikin farin ciki
Ta karasa gurin cikin wata irin tafiya ta daukar hankali duk wani sassan jikinta yana motsawa mussaman qirjinta,
Tun daga nesa ya hangi ta wowarta gurin yayi saurin dauke kansa yana ya mutse fuska,cikin ransa yace yarinyar nan zatazo ta takurani yanzu
Ashe Mubina ta ga lokacin da Hanifa ta mike domin tarar Nasir din,ranta ya baci in da A kwai wacce ta tsana bai wuce Hanifa ba duk da tana a matsayin "Yar uwarta ,sabida tana son Abinda take mugun so,
Sai kawai ita ma ta mike tsaye cikin yanayin shigarta ,ta durfafi inda suke tsaye,
Hanifa ta karasa gurin fuskarta a sake ta ke gaida Dady har da tsugunawa ,Dady Ya Amsa cikin farin ciki yace"ina Babanki yake"
"Gashi can zaune ai kai kadai a ke jira dady a fara gabatarwa"
Dady yace"masha Allah"
Ta karasa kusa da Nasir cikin iyayi da kwarkwasa tace"Ya Nasir dama talaka Na ganinku ,Yaushe kadawo daga ,America ne?

Fuskarshi ya Dan saki kadan yana bin ta da wani kallo irin nasu Na"yan duniya ,yace "Me zaki min kike nema Na ,?
Chapter 17 · 0% Book details