← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 80

Sashe 34

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasir ya zakuda kafadarsa gami da gyara wuyan rigarshi babu abinda ya dameshi yace"ke ce kika jawo baby ,dole ne sai na kwanta dake ,ko ni kadai ne namiji gasu nan ki fita wani ya biya miki bukatarki ni bazan yi ba ok"
Yana gama fadin maganar yayi ficewarsa ya barta a tsaye hannunta dafe da kuncinta
Anwar yana kallon fitowarshi yayi mamaki sosai ganin ko minti goma bai yi ba har ya fito kuma da alama ranshi a bace yake
Kawai sai ya mike ya nufi dakin ,baby na zaune gefan bed tana kuka kamar ranta zai fita ,tunda take a bariki babu Namijin da ya
taba dukanta sai Nasir ,sabida yadda take da gata ubanta mugun mai kudi ne mai fada aji sabida haka ita barinkin ta ma da takeyi ba Dan kudi takeyi ba
Anwar ya zauna kusa da ita yana wani lumshe ido ganinta a tube babu kaya dama ya dade yana kwadayinta yarinyar taki yadda dashi bata yadda da kowa sai Nasir sai kace shine autan maza
Hannunsa ya sanya kafadarta yana Dan mammatsa mata jiki yace"baby yaya a kayi ne kyakykyawa a kowa ne hali ,mai yasa kike kuka "?

Cikin kuka tace "Anwar wai yau ni Nass Mara sabida yaga yadda na damu dashi"
Anwar ya ja tsaki yace "an gaya miki ki rabu da wancan Dan iskan kinki kina wahalar da kanki ,tuntuni nasan bayasonki jikinki kawai yakeso ,kizo kawai ,kinsan ni tsakani da Allah nakesonki amma kamar ke babbar yarinya ki tsaya ya mareki"
"Kasan yadda na keson Nasir a rayuwata Dan Allah ka fada min ko wata sabuwar budurwar yayi shiyasa yake min wulakanci"
Anwar yayi murmushi yace"kwarai kuwa sabuwar yarinya yayi kece dai baki Sani ba amma tuntuni dama yake boye miki"
Baby ta share hawaye tana kallon Anwar ranta a mugun bace tace"ai kuwa Nasir ya tabowa kanshi bala'i domin bai isa ya yaudare ni ba wallahi babu wata mace da ta isa ta rabeshi sai ni sabida ni nafi kowace mace sanin waye shi ,wallahi sai na lahanta mata rayuwa ko wacece ita"
Shashshafa mata jiki yakeyi yana lasar baki sai kace tsohon maye yace" nima zanbaki goyan baya mutukar zaki amince dani muyi mu'amala zan taimaka miki gurin ganin kin cika burunki a kan Nasir din"
[22/05/2019 11:31 AM] Binta Umar Abbale: Baby wacce take a bukace tafara jin sakon da Anwar yake ai kamata nan da nan ta juyo gami da kamashi tana kiss din shi ,dama haka yakeso nan take suka dilmiya cikin aikinta Zina ,abinda suke ganin yin hakan waye wace a gurinsu
Nasir ko da kyar ya kai kansa gida , yana kokarin fitowa ya tuna da Baban gida dake can asibitinsa a kwance dole yaje ya duba shi duk da cewar ,a kwai likitoci masu kula da masu jinya amman zuwanshi yana da muhimanci dole ya juya kan mota ya nufi asibitin
Lokacin da ya isa 11:30 Na dare ,haka yayi parking din motarshi ya fito ya nufi ciki
Shiru bakajin komai sai karar Ac a ko'ina ,kai tsaye dakin da ya kwantar da Baban gida ya nufa,ya na kwance yana bacci ,cikin kwanciyar hankali ya duba gefanshi inda wata drowar ke aje magungunanshi ne a aje ,wannan ne ya tabbatar masa da cewa an bashi magani a kan lokaci kamar yadda ya umarta kafin ya tafi
Fitowa yayi daga dakin yana sakin ajiyar zuciya, batare da bata lokaci ba ya leqa sauran dakunan a gurguje nan ma komai normal,
Maryam kuwa tunda taji alamun an shigo gurin ta mike ta fito daga dakin nasu lokacin iyayenta duk sunyi bacci, jikinta sanye da Hijab taje ta tsaya bakin hanya , tana jiran fitowar Nasir din.
[06/06, 01:43] +234 808 996 5176: [23/05/2019 10:26 AM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*84*
Nasir ya fito cikin sauri hankali yayi gaba kwata-kwata bai lura da mutum a tsaye a bakin kofar ba ,sai da yazo daf da kofar suka hada ido da Maryam,gabanshi ya fadi sabida yadda ta dallareshi da idanunta Wanda suke mutukar gigitashi ba tun yau ba,
Sai ya fara addu'a cikin ranshi yace yau kuma kinzo min a zahiri kenan ,da kina zuwan min cikin baccina ki dameni kullum ta'ala yau zaki bude min ido ,to ta Allah bata ki ba,aljana a kwaba,shikadai yake wannan zancan a ransa
Maryam ko da ta lura da yadda ya tsorata da ita ,sai tafara wani salo da idanunta kuma takafeshi dasu kurr!

Abinka da dare ,launin idanun nata yakara yin blue sosai da sosai ga gajiya da tsabar bacci a cikinsu
Nasir ya nemi yawo ya rasa a bakinshi ,da kyar cikin karfin hali ya furta maganar da take bakinshi ,"wai ke wace irin macace ne ,yanzu mai ya hadani dake , zaki tsare min hanya ,uhumm!

Ki fita daga rayuwata in huta kin zame min matsala a rayuwata ,to idan ke aljana ce ina da maganinki hakanan In mayya ce ke nan ma ina da maganinki bai yiwuwa kizo ki dinga damuna cikin bacci na ,yanzu kuma ta kai takawo kina so ki bude min ido ,to baki isa ba wallahi,ya karashe maganar cikin karaji da hayaniya!

Shi duk a zatonsa mafarki yakeyi irin Wanda ya sabayi kullum ta'Allah in ya kwanta
Maryam ta dake tana boye dariyar ta ganin yadda uncle din ya gigice lokaci guda sai Sam batu yake mata,
Ta bude baki da kyar tace" uncle nice fa Maryam dama jinsin bil'adam yana dawowa Jinsin aljanu ,ko duk tsanar da kake min ce ta jawo kake dangantani da aljanu,ok babu komai,dama Aunty tace Lallai sai na baka hakuri wai dazu nayi maka rashin kunya a cewarta to sabida ni ina girmama iyayena kuma ina bin abinda suka ce yasa na ce dole zan tsaya komai dare in kadawo in baka hakuri kamar yadda aunty ta umarce ni ,Allah ya baka hakuri Nasir"
Nasir yayi tsaye yana mamaki yarinyar tabbas itace ba gizo take masa ba sabida haka batare da bata lokaci ba ya makureta jikin garo ya tattaro hijabin da yake wuyanta ya rike a hannunshi sosai ya shaqe mata wuya tana fidda tari sama-sama ,idonshi jajar yace" Dan Ubanki mai kike anan baki tafi gida ba ,ni zaki rainawa hankali ,kice aunty tace ki tsaya kibani hakurin uwarki ko dai kintsaya kinyi yawonki na iskanci dare yayi miki shine kika fake cikin asibitina da safe ,ki tafi ,ni zaki kawowa bariki"
Tana tari sosai yayinda idonta suka kada sukayi jajazir tace "dama duk abinda mutum yakeyi sai ya dauka haka kowa yake uncle ,baka isa ba kayi kadan ,a kanka nayi karuwanci ,ni ba "yar iska bace ehe"!

Mari ya tsinka mata yace"ni kike zagi "yar iska ,yaushe har idonki ya bude da bariki"
Maryam ta fashe da kuka tace"Allah ya isa indai ka kara dangan tani da wannan sunan ancle
[23/05/2019 10:43 AM] Binta Umar Abbale: Yace " an dan gan taki dashi dan ubanki in bakisan bariki ba mai nene kullum sai kinzo kin dame ni dadaddare yau dai zan koya miki hankali"
Janta ya farayi tana turjewa cikin kuka tace"ka kyaleni wai ina zaka Kai ni ne Allah ya isa ban yafe ba"
Bakinta ya buge da bayan hannunsa ya cigaba da janta a kasa ,takalman kafarta duk suka watse a harabar gurin yayin da duk gwiwoyinta suka kurkurje jini har ya fara fita ,kuka takeyi tana kokarin cire hannunsa amma yaki sakinta,
Ya bude mota ,ya tattaro ta ya sakata ciki sannan shima ya shiga a fusace ya ja motar ya fice daga asibitin,a gogon dake motar ya kalla karfe daya saura na dare,kai tsaye ,babu inda yayiwa tsinke ,sai muwala hotel yayi parking din motarshi gurin haske tarwai kamar rana shagallalun sai rayuwa sukeyi babu abinda ya damesu ,wasu Na shaye-shaye wasu na tsotsa tsotsensu har da masuyin sex a gurin gaba daya ma
Marym ta gigice ganin irin abinda yake furuwa a gurin sabida tana kallon komai ta cikin glass din motar
Nasir ya fito ya zagayo gefanta ya bude motar yana kokarin jawota tana turjewa sai kuka takeyi tace"uncle kaji tsoran Allah mai yasa zaka kawo ni nan da mutumci na"
Tsinka mata mari yayi yace" waye Mara mutumci anan,duk sun fiki kima da mutumci a gurina "yar iska ,ni zakiyiwa rashin kunya"
Maryam ta riqe murfin mota taki fitowa ,sai kuka takeyi tana bashi hakuri,
Nasir yayi mata fizga guda sai gata a kasa a gurin ta zube ,ya mayar da motar ya rufe ,ya zagaya ya shiga mazaunin dravar ya kunna motar yayi tafiyarshi ya barta a gurin tana kuka ,tana ganinshi ya tsaya bakin get yana magana da sucurty din da suke tsaron gurin ta kwaso a guje amma kafin ta karasa ya fice daga gurin,tana kokarin fita ,suka mayar da kofar suka rufe ruf batare da sunce mata komai ba,sai ta zube a gurin tana ihu!!
[06/06, 01:44] +234 808 996 5176: [23/05/2019 3:40 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*85*
Wani haddadan gaye ne zaune can gefe bakin wani katon swimin yana zukar sigari yaga lokacin da Nasir ya shigo cikin hotel din idanunshi a kan motarshi har sanda yayi parking ya fito,cikin zuciyarsa yana mamaki ,yau Nasir ya shigo rabon da ya ganshi a hotal din nan tun bayan rasuwar mahaifinshi to kafin ya gama tunin ne kawai yaga yana jawo Maryam tana turjewa taqi fitowa,abin sai ya bashi mamaki ,yau Nasir ne ya kawo mace amma tana bashi wahala,
Abinda yakara daure masa kai yadda yaga ya fito da Maryam ya jefar a gurin ya shige cikin motarsa ya barta a gurin.
Chapter 34 · 0% Book details